Chapter 28
Chapter 28
kanshi da kanshi. Jiki ba kwari ya tada machine yai gida. Dole ya tit'siye Bintu ta sanarshi gaskiya. Bata d'aki,ga nan wayarshi da ya manta da tata akan gado halamar tana sana'ar tata ta charting. A garin ya d'auki tashi ya danno screen na Bintun, haske ya baiyana halamar tana ma kan charting din tai wani waje. Kwanciya yayi da bayanshi jiki duk a sanyaye,bazai iya bawa wannan ranar suna ba. Ido ya kura ma wayar Bintun kirar _Techno_, zai so yau yaga mey ke debe hankalin ta zuwa Facebook. *Bintu U*. _"ke an saki shegiyar fa,ki tayani murna zan sakata in wataya_.. *Shining star*: _"Kai matar nan baki da dama,a bani satar amsa dan yanzu na dawo makarantarki_.. Da azama ya mike zaune dan ganin charting din. *Binta U* _"Hhhhh,tuggu dai kamar kullum nayi,sai dai na yau mai zafi ne,dan jiya an bani sa'a har gida, take ina fad'in ta fita ya d'anna mata saki,baiwar Allah harda dan guntun wa'azin ta ta min hhhhh_.. *Shining star* _"ina ma zan iya irin wannan sharrin naki dana huta, sai dai tawa tasan takan duniya,ina mata take dawo min da abu na_.. *BINTU U* _"ba gari daya muke ba,da wallahi taci karya,ni zan baki maganin y'ar banza_... "Ya Allah... Kai shafo cikin ranar jiki hawaye na zuba, da sauri ya d'anna _previous chat_ Sai gata kamar an jehota da buta a hannu tana zare idano na munafukai. Sam bataji koh dirin machine dinshi ba,sai arbawa tai da takalmanshi. Da d'ukkan hannu biyu ya dafe kanshi yana hawaye,mey zai ma Bintu ya huce da bala'in da ta jawo mishi?.. A hankali kalaman Salma ya dawo mishi, _"Allah ya biyaki da dai-dai abinda ki kamin Bintu..Ki sani,sharri kare ne,ko yayi nisa zai dawo gun maishi_... Gashi tun kan a kwana ya dawo ma Bintu bata shirya ba... "Ka dawo..yaushe ka shigo..ban banji shigowar ka ba.. Da in'ina take maganar, ganin yadda hawaye ke diga a kafafunshi ga kuma wayarta a hannunshi tasan yau karya ta kare. Ido ya goge kamin cikin nut'suwa ya ajiye wayar kan gado ya k'allota. "Tabbas kinyi nasarar rabani da d'ukkan farin cikina Bintu.. Kinyi nasara,tanan kam nasan kin ma Salma fincinkau,dan ita bata sharri.. "Na baki d'ukkan wata amana,ki mayarni shashasha.. Ki nunan yau abinda Salma take gudu a kishiya,"makirci".. "Amma ki sani,wallahi!,wallahi!!.wallahi!!! Uku,yadda kikai sanadin 6allewar aurenmu da Salma kinyi naki. "Kamin nan zaki ji jiki kamar yadda ki ka sa taji t'sawan zaman ku.. Kan tai kwakwaran mot'si ya hard'o ta, ta ko'ina mari yake bata iya karfinshi tana ihun jama'a su ceceta.. Sai da tabbatar ya taga wuta dan mari kamin yana haki ya nuno ta. "Kije kema,na yanke igiyar aurena dake kanki har guda uku... "Tun kan ki kwana maganar Salma ta kar6u gun Allah... Ihu ta saka tana bashi hakuri kan ta daina, "dan Allah karka sake ni... Hanyar waje yayi yana sa waya a aljihunshi. "Ki tabbatar baki kara awa d'aya cikin gidana ba,dan saki uku na furta. Waje yayi ya ja ya t'saya a zaure,tamkar wani yaro ya rushe da kuka mai tsanin ciwo.. Yayi kuskuren da dak'yar ya g'yara shi cikin rayuwarshi.. Yayi kuskuren da ya bari Salma tai mishi nisa... Yayi kuskuren kin kar6ar shiryiwar Salman sa.. Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwa. "Allah ya isa t'sakani na dake Bintu... Ubangiji yai ma Salma sakayya akanki daga yau har ranar sakamako... Allah ya isar mata cikin sauri.. Ganin hakan ba mafita bace gareshi yasa ya d'akko waya hannu na ka'rkarwa zai nemo Garba yaga kiran Aunty A'i na dazu. Garban ya kira,dole ayi wacce za ai,Aurenshi da Salma mutuwa ce kadai zata raba. Da Allah ya had'ashi cikin muryar kuka kan yazo gidanshi yanzun nan.. "Isha'i ake kira fa Ja'afar.. "Dan Allah kazo,in bakazo ba komai zai iya faruwa... Ba'a fi minti goma ba yazo,fatattakar arziki yai ma Bintu ta bar gidan ya rufe ya fad'a mota. Da t'sananin mamaki yake k'allon abokin nashi, a iya abotarsu bai ta6a ganin koh da hawaye na Ja'afar ba bare kukanshi mai sauti irin haka. Dan Ja'afar namijin duniya ne,Jarumi, kuma jajirtacce, yasan komai ya sashi kuka ayau ba karami bane. "Gidan Aisha zaka kai ni yayar Salma.. Baki sake yake k'allonshi, "Yayar Salma kuma?.. Ido jajir ya kalloshi ba halamar wasa,dole ya tada mota suka d'au hanya. Waya yai mata kan ta fito yana kofar gida. "Malam mijina ya fita..kai hakuri.. Kit ta kashe wayarta,yau Aunty A'i ta d'au zafi ya sani,tabbas kuma Salma na gidan.. Murfin motar ya bud'e a fusace ya fice Garba na kira.. Kofar a bud'e take,kawai ya tura ya shiga, nufinshi a d'aureshi bayan yaga Salman. "Salma!,, Salma!!.. A tunzure Aunty A'i ta fito a parlourn dan tsayarahi shiga mata parlour. Yadda taganshi bata isa hana shi ba ganin Salman, dan g'wiwa biyu ya zube gabanta tamkar yaga Salman. Hanya ta bashi ba musu,da zafin nama ya mike ya shiga parlourn, bata zata ba taga mutum a kanta,da sauri ta zabura ta mike tana kwad'a kiran Aunty A'i da sauri. Bata nufa ba taga mutum zube a gabanta kanshi a kasa. Ido ta rint'se tare da kawar da kanta,koh kadan bata son kara ganin Ja'afar a rayuwarta Abadan. Juyo wa tai da niyar surfa mishi ruwan bala'in da ba shiri zai bar gidan,sai dai mey? Da t'sananin mamaki take kallonshi tana k'allon Aunty A'i. Hawaye ke malala a idonshi kamar wanda ya rasa jin dad'in rayuwarshi,abin g'wanin ban tausayi. Ja'afar?.. Kuka ma?, a namey toh?. "Salma gani gabanki, a matsayin wanda ya tafka miki laifi cikin rashin sani,da kuma sharrin Bintu..Salma kiyi hakuri,wallahi _am really really sorry.. Kar ki barni dan Allah.. Zan tagaiyyara Salma.. Zan zauce.. sharrin Bintu ne,kuma itama ta amshi hukunci,dan na saketa kamar yadda ta jawo mana, _please_ Salma _forgive me_... Wallahi _I can't live without you anymore_,ki tausaya ma mijinki uban yaranki... Baya taja da sauri ganin yana kara kusantota. Da sauri Aunty A'i tai waje jin kuka zai kubce mata.. Dole haka zata kasance dasu Salma,ranar rabuwa, rabuwar da ba a da tabbacin za'a dawo ta.. Tabbas tausaya wa rayuwar su,dan a irin soyayyar nan ita ce ake kira *Mutu ka raba*.. Gashi yanzu K'ADDARA ta raba masoyan biyu. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 32_Kuka take yanayi iya karfinsu, tabbas K'ADDARA ta rigayi fata, duk kuma yadda ka t'sara rayuwarka sai ka ga ba haka ya tafi ba,tabbas ta Allah itace daidai. Baya tai ta zube kan kujera da6ar.. Duk sunyi kuskure, kowa na da laifi,meyasa ma tace ya saketa?.. Mey yasa?.. Le6e ta cije tana mai sa d'ukkan hannunta biyu zuwa fuskarta, kuka kam yau har sunji ba dad'i. A hankali ta dago tana K'allonshi ido yai luhu- luhu,duk ya marairaice mata hawaye na zuba, tafi tausayin kanta sama dashi, Kokarin magana take su Aunty A'i sukai sallama ita da maigidan da taima waya. Fuska Ja'afar yai saurin gogewa ganin yadda Abban Aslam ya sau baki yana kallonsu,bai tunanin abin ya kai haka ba, kuka a gaban mace da zubewa g'wiwa biyu?.. Lalle yasan abin babba ne. "Innalillahi Wa'ina Ilaihirraji'un... Itace kalmar shima da ya fad'i bayan yaji mai ke faruwa.. "Dole aje gida kowa ya samu labari,dan wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41