Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,254 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

murmushi tai dan tuna wa da kalar da Ja'afar yafi so kenan. Tunda ta zura kayan ta nad'a d'auri take bin kanta da k'allo a mudubi ta gefen Ummi. MashaAllah tai k'yau, gashin da ya fito ta kasa take turawa cikin dank'wali,ta kai dubenta ga Ummi wacce sai ko'k'arin fiddo nata take tabi dank'wali ta kansu. Murmushi kawai ta mata,tasan da tace ta mayar su ciki ma a iska. Sai dai tana d'akko turare ta hau feeeee ba ko kakkautawa. "Haba Ummi,turaren nan kinsan haramun ne sashi ki fita koh?.. Ga gashi kullum sai ance ki alkinta shi.. Allah kina *TABARRUJ* da yawa.... Galala take k'allonta, kan ta ja t'saki tai waje. Iya wuya Salma tazo, ta bala'in t'sanar t'saki. Ba'a jima ba Ja'afar yazo.. Tabarma yau ta d'aukar musu,shima yasha wankan farin kaya da farin takalmi _half cover_ sosai yai mata k'yau. Yadda yake fara'a da bin k'allonta tasan itama ta wanke shi. Suna t'saka da gaisawa cikin nishad'i yaro yazo,wai tazo a waje inji Ummi. Tuni ya sauya,dan yaga zuwan su Muzammil. "Minti biyu kawai.. Kai ya k'ada mata da dan yake. Tana fita suka ware gefe,tsakani da Allah ta fad'a mishi yai hakuri. Baki sake yake binta dashi har ta kule cikin gida. Amma Ja'afar ya bala'in k'wada shi da kasa,dan haushi koh isma'il bai jira ba yai gaba. Ita kam tana zuwa ta bashi amsa gamshasshiya, wanda tasa fara'ar Jafaririn ta dad'u ba shiri. Tad'i suke kamar ba gobe, mot'si kad'an yace "kinyi k'yau..... Itama cikin kunya tace yayi shima. *************** ************** "Naga sai zarmewa kike fa akan Ja'afar salma,sam kinfi k'arfin shi kima ji da wai,gaba ake son ci ba baya ba wallahi,d'uk da ban san wacce iriyar amsa kika bawa Muzammil ba... Da harara Salma ta bita, kan tai k'wafa, "ina ruwan ki da sha'anina? Ke har kin isa ki fad'a min wanda ya dace dani Ummi? Baki Ummin ta ta6e, "ke dai kika sani,dama ni meye nawa? Ni koh ana saurayi mey zanyi da Ja'afar mai shegen dacin ran t'siya... "Wai ku baku zama inuwa d'aya ne da juna Salma? Mey yasa baki iya daga ma Ummi K'afa sai kin tanka mata kullum kuna sa makota na jin ina daga murya.. Kasa Salma tai da kai kawai,tasan yanzu in mama taji ta kad'e.. Kamar k'wa wacce Ummi ta karanci zuciyarta ta amshe.. "Wai fa mama daga shawara ta tsaya min masifa,yau akan wannan dan gidan Malam Kabiru mai shago ta kori Muzammil,daga fad'a mata gaskiya ta hau ni da masifa.. Dan Mama daga ganin yadda Muzammil ya tafi rai 6ace nasan cewa tai bata son shi... "Eh bana son shi,koh ana son dole?.. Ja'afar d'in da kika rena ni shi ya min ki ji da wai.... "Kunga ku min a hankali,koh yanzun nan na sa6awa mutum... Shiru sukai,yayinda Salma taci ka tai dam. "Ke ummi wani dan wajen Malam Kabirun kike fad'a? Da harara Ummin ta k'allo Salma kan tai ma Mama bayani,"yanzu haka mama Malamin makaranta ne wallahi yana chan yana kokawa da alli.. Jim Maman tayi kamar mai tunani,chan ta nisa tace "Ikon Allah..anya yarinyar nan Salma ba'a min misanye dake ba a layin jarirai a haihuwa ba?... Mutum arziki na binshi yana ki?...Ina laifin yaran nan?har kasa suka gaida ni,ga mota ga boko..amma in banda abinki mey na sama yaci bare ya bawa na kasa? Da shagon uban zaku dogara koh da kud'in malami?..... Shiru Maman tayi ganin yadda Salman ke hawaye... "Au,au,Salma kuka? Daga fad'an gaskiyar? Kai ta k'ada ma Maman. "A ni tawa mai sauki ne Salma,ina d'ai hanga miki gaba ne kawai... Amma banga abin kuka.... "Wa ke kuka?... Assalamu Alaikum. Shiru sukai salman na goge ido,sai Mama da ta amsa mishi sallama. "Sannu da zuwa Abba. Kai ya daga musu kan ya amsa. D'uk suka tashi sim-sim sukai d'aki. Sai da Abban ya gama komai yasa Mama ta kira su. Kowa tai ladab kai kasa suna saurarar Abba. "Ni ke Ummi na ma kasa gane alkiblar da ki ka kama sam,kullum da wanda za'a ga yazo gunki,sai aukin shegen zance a titi ba wanda ya iya yazo ya samu iyayen ki.. "Ga nan yayarki yau d'in nan yaron nan na wajen Alhaji Kabiru yasa Baban shi yazo muka zanta kan yana son Salma da aure,kuma har sun sasanta da ita.. "Koh ba ai haka ba Salma?... Kai duk'e cike da kunya ta daga kai halamar anyi. "Haka shine musulunci, ta haka kuma ake gane da'ar yaron da zai auri y'arka... Shiru kake ji Ummi anyi lakwas. Nan ya kara ja ma Ummi k'unne kan tara samari da zancen waje,ya kuma ja mata k'unne kan ta fidda na aure koh ya fiddawa mutum. ***** *** Zancen aure dai ya kank'ama tsakanin Ya Ja'afar da Salma. Itama Ummi Isma'il yace da gaske yake.. Mat'sala d'aya tafi damun Salma,yadda komai Ja'afar ya bata na alheri a rene yake gun su Mama, barin Ummi. Dan ita fachaka isma'il yake mata kamar ba gobe. Tun abin bai damunta yau da gobe har ta fara ganin kamar Ja'afar mammako yake mata. Zuciya bata kashi. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 24 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 14_Anyi bikin su Garba. Ana haka saurayin Ummi ya d'allo mata wata sabuwar waya,ita kam tun wata Zain da ya bata,nan habaici ya karu gun Ummi. Biki ya kusa sukai shirin zuwa Borno dangin Abban su. Sunyi sallama da Ja'afar ta shigo gida rike da farar ambalan,d'uk suna zaune t'sakar gida har Aunty A'i da yaronta. Hannunta Ummi ta k'alla, kan cike da shakiyanci tace "ta Ja'afar mey aka samu ne haka har a farar takadda?.. Harara ta dan mata kan ta mikawa Mama. Kai Maman ta k'ada, kan tace "a rabani da kayan haushi,rike abinki kawai ki kirga... Dariya Ummi ta sa,wanda tuni ta kara kular da Salma. "Mama ba ma sai ta kirga ba,dan wallahi ba kaffara nasan kud'in nan bai fi dubu biyu ba... Kanta Salma ta yiwo a tunzure mama tai musu iyaka. "Meye na jin haushi?.. K'yautar tashi tana wuce nan ne?... Ba dai d'an d'an kasuwa zaki aura ba? K'wafa tai,kan tace "baki fara ganin komai ba ma Salma. Aunty A'i ce ta k'ar6a ta kirga,ai kam sabbin hamsin hamsin ne ta dubu biyu. Mama tace "Ahab,na sani ai. D'aki Salman tai tana hawaye,sam bata kaunar abinda ake ma Ja'afar,amma shima da laifin shi,dubu biyu ina zata kaita? ****************************** Biki kam yazo,gashi yau har anje jere, k'warai sunyi mamakin gidan Ja'afar da gina kuma da kanshi. D'uk da ba wani babba bane,dan koh t'sakar gidan karama ce,babban _parlour_ ne sai _bed room_ da band'aki aciki,ga _kitchen_ a ciki karami,sai d'aki d'aya daban a waje, d'ai d'ai zaman mutum d'aya de,rufin asiri dai ak'wai shi,Alli da shago sunyi rana. Sa6anin Ummi mai tafkeken gida da mai gate yasha alatu. Yanzu lefe ake wat'sa ido aga na Ja'afar, dan tuni na Ummi yazo san barka,sai zuzutawa ake. Salma in ta tuno gabanta har fad'uwa yake,fatan ta Ya Ja'afar ya fitar ta a magana. Dan tun a kud'in anko taga tasku,dan isma'il ankon k'yauta yai ma k'awayen Ummi da dubu ashirin nata na fitar biki. Shikam sai hakuri yake bata,kan shi bai

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});