Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,263 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gun Mama,dan har gida tace ai mishi t'sakani da Salma,sai dai yazo za'a bashi Miemie in dan ita ne. Sosai yaji haushi,yasan aikin Salma ne..shi yasa ya d'auke mata wuta,sai dai ya tura k'annenshi su dakko mishi Mimi Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Aug 4 Feenat Ja'afar Novel's Su Salma an samu gurbi a school of hygiene,da shawarar baba ta cike ba Polly ba. Ranar da ta fara fita da personal zata kai takaddun ta. Ba yadda zaka ga Salma ka gane itace da lokacin tana budurwa, yanzu Salma ta daban ce,ta gaban goshin Mama, dan ta dage dole sai tayi kara'i da zawarci. Kwanar su Ja'afar ta shawo,tasan yanzu haka yana makaranta dan sha d'aya na safe. Sosai tai k'yau cikin doguwar riga ruwan kwai mai duwatsu,da g'yale karami ta nad'a fari,ta ritaya jaka karama mai (chain),ba wata k'walliya tayi ba ta azo aga,dan wannan ma Mama na t'saye tayi ta,ta kuma rantse ita da hijabi sai a sallah. Zai wuya kace ta ta6a aure har da rabon Miemie, dan yanzu ne take shekarunta na (22) a duniya. Kanta kasa take tafiyarta cikin nut'suwa, sai dai ji take duk ta tsargu,tamkar Ja'afar na kofar gida yana kallonta. Dak'yar ta kai kanta bakin kwalta tana sauke numfashi, ashe feeling take... "Kin k'yauta Salma kenan?... A razane ta juyo jin mai maganar.. Rai had'e yake kallonta tamkar bai ta6a dariya ba. Duk da ta tsorata da ganin yanayin da yake amma ta cije itama ta ci kunu. "Da nai mey fa? Rai 6ace yace "Ina Miemie?.. Kai ta k'autar gefe,kan tace "Gida".. A fad'a fad'a yace "Wato bakiji abinda nace ba koh?.. Kalli shigar ki,kamar wacce zata party,sam baza mu shirya dake ba in.. "Tafiya ne?.. Wani mai keke napep ya tambaya, kallo irin na baka isa ba tamai, kamin tace ma mey keken "Eh tafiya ne. Tana kokarin shiga tace "ba ruwanka da shiga ta,cos I know what i'm doing.. And ni ba y'arka bace, na fad'a ma ka rabu dani. Sam taki k'allon fuskarshi bare ta sare gun taka mishi burki. Baki sake yake binta da k'allo har mai napep yaja kamin ya samu k'warin ya tanka. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/7, 11:03 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 34_Jingina tai a jikin Napep din tana sauke ajiyar zuciya. "Kai hakuri Ya Ja'afar, ya zama dole na koya ma nisa dani,kai hakuri,ina sonka wallahi.. "Hajiya magana ne?.. Kai ta dago jin mai Napep na tambaya, ashe maganarta ta fito fili. Ta gama komai Monday zata fara zuwa,kwarai taso ta yaye Miemie sai dai ba hali,dole tabi yadda uban y'ar ya t'sara. Shikam Ja'afar tun daga wannan ranar kullum zata makaranta sai yai mata maganar wani abu,koh yace k'walliya tayi yawa, koh yace uniform ya d'ame ta. Wani sa'in har ta wuce tana dariyar zariya irin ta Ja'afar, tabbas gani take ya zare. Shima kamar yadda Abba yace haka dole ya fara _processing_ dan tafiya masters a B.U.K,sai dai fur Abba yace garin zai bari,a Zaria zai yi,kar ya damu an ma kusa shirya masa komai ba koh kwandalar sa. Tamkar ya aza hannu aka ya kwala ihu yake ji ranar,yana nan ma ya ya k'are da Salma bare ya mata nisa?.. Tafe suke ita da wata y'ar makarantar su da tazo zata rakata bakin kwalta, ta gama shirinta kenan zata gidan Aunty A'i sai fasawa tayi. Tai kyau,fatar sai shining take taji mai da sabulun Mama. "Allah ba wanda zai ce kin haifi Miemie sis Salma,kin ganki kuwa?.. Murmushi tai ma kawar tata lokacin da take t'sayar mata da Napep. "Haka dai kuke cewa kullum.. Murmushi tai mata sukai sallama. Tana kula da wani mai mota yana ta kallonta ya t'saya siyan Apple. Kokarin tsallakawa yake ganin zata wuce da sauri,kai ta kada dan sarai tasan yau ma za'a tafka dirama irinta ranar chan da Ja'afar, dan tana kallon yadda yake maka mata harara a kofar gidan su suna zaune shi da Garba da wani,tasan darajar kawarta taci da yanzu ya taso bambami dan tasa g'yale a kafad'a, kai ta girgiza dan yanzu abin dariya yake bata ma... "Assalam Alaikum.. Waiga wa tayi jin an mata sallama. Da dan sakin fuska ta amsa tana mai cigaba da tafiya a nut'se. "Gunki nazo fa y'an mata dan Allah. Kai ta daga aikwa idon Ja'afar kyar kanta. Da murmushi ta juya badan taso ba sai dan yakice dan gudanta, duk da tasan baza a wanye lafiya ba. Tuni dad'i ya kama saurayin dan da har ya fara d'ari-d'arin mata magana,sai ya ga kamar matar manya ce. "In bazaki damu ba dan Allah ki ban numbern ki,wannan ne gani na biyu da na miki a layin nan yanzu ina sauri zan kira ki... Ta gefen ido ta sato k'allon Ja'afar ai kwa a suk'wane yake zuwa gun nasu. Da sauri ta karbi wayar mutumin da zummar sa mishi ya iso. Su dai su Garba ido ne nasu,dan abin Ja'afar ya daina bashi dariya yanzu tsoro yake bashi. "Bashi wayarshi ya kauce tun kan na dagargazata a gun nan.. Banza tai dashi tana cigaba da latsa wayar karya,bata aune ba taji ya warce da karfi. "Karbi wayarka ka bar layin nan Malam, koh kaga tayi sa'ar tsayuwar ka?.. Baki sake saurayi yake kallonshi,shi a tunanin shi koh yayanta ne ma,dan shima haka yake ma samarin k'annenshi baraza,dan haka bakin shi alaikum ya kar6a yana kallon Salman. Cike da tsiwa ta kallo Ja'afar din, "Malam wai ina ruwanka da samari na ne eyeee?.. "Kimin shiru tukunna, kema zan dawo kanki ne ai. Da hannu ya nuna ma saurayin hanya halamar ya ware,ba daban yaga Ja'afar din ba na wasa bane ba da ba yadda za ai ya bar wannan sankaceciyar budurwar. Da sauri ganin zai tafi tace "Malam ina zaka ne?.. Kai ya kad'a mata yana murmushi kan ya kara gaba. A fusace ta nuno shi da hannunta "Wallahi Ya Ja'afar na gaji da wannan abin fa,dan wallahi na kusa kai karar ka gun Abba ya mana t'sakani,mey ruwanka dani wai?... Shiru tai tare da matsawa da sauri ganin ya mika hannu bayan gyalen ta. "Wai kai lafiya ka ke?.. Harara ya sau mata kan yace "Tun muna sheda juna ki daina sarar nan ta sauke g'yale a kafad'a Allah... "Bazan daina ba din, na fad'a ma bani ba kai, tunda kai har yanzu bakasan Annabi ya faku ba... Shiru tai ganin Garba. "Haba Salma,haba,a titi fa ku ke?.. Tunda kinsan halin kayanki sai ki gaba ki barshi ya karata, dan Allah ki daina biye mishi. Harara ya sakar ma Garban, "ina ruwan ka toh kai ma,kowa dai yasan da matata nake t'saye ba kowa ba.. "Mtsww... T'saki taja rai 6ace, duk suka kallota.. "Wallahi you are sick.. "Ni matarka ce, amma fa a da, kai istigfari ma tun wuri,dan wallahi za kayi sa6o... "Kimin shiru fa Malama..dan kwanciyar hankalinki wallahi kibi abinda na ce kiyi,period.. Shiru tai tana kallonshi,karfin hali sai gun Jafar,tabbas sai tayi da gasken gaske,dan abinshi gaba yske,shima Garban k'allonshin yake,abu dai kamar wasa yake gani yanzu zai zama babba. By Feenat Ja'afar. [8/7, 11:07 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 35_Drama sosai sukai kan ta

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});