Chapter 32
Chapter 32
wuce gida rai 6ace duk rai a dagule, dabarar ta ta kare kuma a akan Ja'afar, duk hanyar da zai zuciya ya daina kulata tabi ba nasara,tamkar ma zigi take mishi. "Mtsww... Taja t'saki,Tabbas so so ne,amma na Ja'afar son kai ne,dan shi yaja komai.. "Ke kuma ke da wa kike t'saki haka?.. Ba tare da ta dago ba tace "Ja'afar man.. Ya hanani sakat a unguwar n... Da sauri ta datse harshenta dan jin Mama fa ke tambaya, "Au har yau yana nan yana bibiyar taki koh?... Kai ta girgiza da sauri, zarar bunu.. "A'a, ni nasan hanyar maganinshi,ki ban nan da gobe. Da sauri tace "A'a Mama ba komai bane fa,kiyi hakuri zai daina... Shiru tai ganin harar da take aiko mata. Tun daga ranar Mama ta zama y'ar rakiyar Salma hanya,sai ta tabbatar ta hau abin hawa zuwa makaranta zata juyo tana aika mishi harara,da tai na sati sai ya bar tare hanya kuma ya dawo waya. Ana haka shima admission nashi ya fito shima,tuni ya shiga kunci,dan yasan ya kusa yin nisa da Salma,hakan yana nufin komai zai iya faruwa. Ranar da yamma ana washegarin zai tafi yazo mata sallama duk da sunyi fad'a. Taimakonshi daya Mama bata nan ranar ma,dan yana ga ita kad'ai zata iya tsaida shi a yima Salma kashedi. Shigarshi zauren kenan sukai kicibis zata fito,harara ya sakar mata kan yaja ya t'saya. Fita take shirin yi ya ruko gyalenta da sauri har yana zamewa,don haka a fusace ta juyo da niyar balbaleshi ya marairaice mata fuska. "Saken g'yale toh.. Murmushi yake yaki saka, ''ka saken gyale koh na fuce... Da sauri ya cika yana tare kofar fitar. "Maganar fahimta nake so muyi dake,dan Allah ki t'saya.. Hannu ta hard'e a kirji ta k'alleshi,itama zata so su fahimci juna. "Ina wuni toh,tunda har gaisuwa kin soke dani. Da kalar tausayi ya kara yana sukui da kai har taso yin dariya kamin ta gaishe shi. "Ina Miemie?. "Da Mama suka fita,kayi kai maganarka kan su dawo fa. Tsayuwa ya gyara tukun ya kira sunanta, rai sake ta amsa,fatan ta yasa zancen azziki zai mata ba wai shirme ba. "Salma".. A karo na biyu ya kara kiranta, bai jira amsarta ba ya cigaba, "Gobe zanje Zaria kan batun makaranta da zan fara, kima Allah Salma ki yi kamar ina nan dan Allah,banda kula tsagerun samarin nan wanda har yau basu mallaki hankalin kansu ba dan Allah. "In ma aure naso kiyi ina ga ni ya dace na baki mijin aura,bare a agendar mu bamuyi haka dake ba... T'sam tai tana kallonshi da halamun ya zare tana murmushi, amma zata bishi a haka a wanye lafiya. "Toh naji,zan kuma kiyaye,happy?.. Kai ya kad'a da murmushi, "yauwa koh ke fa,dan Allah Salma ki riken alkawari nan.. Kai ta kad'a tana taji ai.. Da haka suka rabu ya bata kayan zakin Miemie, murna fal ranshi suka rabu ranar. K'warai ta samu sakewa sosai bayan tafiyar shi,tuni ta kara bud'e shafin zawarci sabo,duk da kasan ranta tausayinshi take ji sosai. A wata daya tai samari biyu irin son Mama, barin Alhaji Usman Dan chanji. Kud'i sosai yake kar mata kamar ba gobe, albarka kwa kullum samunta take gun Mama,yace shi ba yaro bane,dan haka yana so ai auren cikin k'ank'anin lokaci. Ya sanar mata yana da mata daya da yara biyu kachal,aurenshi uku,sun rabu da biyu sai Hajiya ta k'arfen. Tunda suka rabu tazo gida tana tuna abu uku, tabbas a yanzu bata da ra'ayin auren mey mata,dan taga aya akan Bintu. Sannan bata son mutum mai irin kud'in Alhaji Usman sam a rayuwarta. Gwara ma Kamal dan shi matashi ne kamar su Ja'afar, kuma yafi kwanta mata a rai,gashi da saukin hali da saukin kud'i. "Oh ni y'an nan,ashe arziki ke binki Salma a rayuwa?.. K'allon Maman take yadda take daga abubuwan da Alhaji ya bata,ita dey nata ido. "Bana jin koh lokacin y'an matancinku kun ta6a had'uwa da irin wannan, babbar harka ai tayi y'an nan... "Mama ni fa mutumin nan bai kwanta min ba sam Allah,gashi har ya fara maganar aure tun yanzu,ga yana da mata fa,ga ni sam irin kud'in nan baya... Baki sake Mama ke k'allonta,tuni ta tsayarta cikin fad'a. "Rufe baki ni sauraniyar y'an iya t'sari, ashe har yau kina nan da halin nan Salma? Arziki na binki kina zura da gudu?.. "Ina ruwanki da matarshi?.. Koh a kanta zaki zauna?.. Kai ta girgiza zatai magana ta dakatar ta. "Koh dai Salma hudubar yaron chan tai tasiri akanki?.. Kai ta kad'a, "Allah Mama ba haka bane,ni ina tsoron kishiya ne,kinaji fa wai aurenshi uku suna rabuwa sai ita ke zama... "Sai mey toh?.. Kar ki bada mata mana Salma?.. Baki sake take k'allon Maman,kamar ba ita ke fad'in ba mai zama da kishiya ba a yaranta tunda itama bata zauna ba,wace daga ce ba'aci ba lokacin auren Bintu da Ja'afar amma yanzu kud'i ya warware Mama?... Kat'seta tai, "Saboda haka komai yace ki ce toh, in ma ita ke fidda su toh ke zama daram,dan wannan ba gidan fita bane in an shiga... Hawaye ke zubar mata yayin da tazo k'wanciya tana tariyo zancen Mama, dole in dai tana son faranta mata wai ta ba wa Alhaji dama. Waya ta d'auka jin shigowar text message,tasan na Ja'afar ne. _"Salmatee,remember, a heart dat truly loves never loses hope..but always believes in d promise of love,no matter how long d time and how far d distance,at d right time,love will fine a way".._ ki rike alkawarin ki,love you.. *Ja'afar* Kukanta ne ya karu sosai bayan ta gama karantawa, tabbas in ta cigaba da sauraran kalaman Ja'afar zasu sa ta karaya har ya ci galaba akanta.. "Bani da kamar ka har kullum Ya Ja'afar, sonka gareni ba mai misaltuwa bane,amma kai kaja mana koma meye... Fuska ta goge sakamakon jin tahowar Mama da Miemie na kuka. Washegari kanta t'saye ta bawa Alhaji damar ya turo magabatanshi kawai koh ta huta da dawainiya da son Ja'afar. Sabon sim ta siya tasa a sabon wayar Alhaji da ya bata,a haka suka raka wata kusan biyu, duk da tai kewar text da kiran Ja'afar din. Shikam yana chan hankali tashe na rashin samun wayar Salma, ga Abba ya sanarshi kar ya sake ya dawo sai an nemeshi a makaranta, Duk da an sanarshi ana kawo Miemie gidansu ta yini. A jikinshi yaji abu na faruwa,duk sai yaji bai da nut'suwa sai ya je gida dan tabbatar da zarginshi. *** Tunda daga d'anno kanshi layin su Salman ya ja ya t'saya. T'saye take da dan murmushi a fuskarta, sanye cikin favorite dinshi riga da skirt na atamfa purple, tai kyau matuka gyalen nan a kafada,daga inda yake zai iya gano bakin gashinta a tufke ta chan kasan dankwalinta, tasha ado tamkar zata party. Wani abu ne yazo dai dai makogwaronshi ya tsaya,kishi... Bai san ya isa gun ba sai da yaji ana "lafiya?.. Kallo shi yayi, duk sai yaji yau baida ma k'warin g'wiwar fad'a,Salman ya kalla,da sauri ta kawar da fuskarta gefe ta had'e rai. Sai ya dawo kan Alhajin,tsaf sai ya haifi Salma,sai t'sabar kud'i da jindadi da suka 6oye shekarunshi. Kallonshi yake tun daga sama har zuwa kafa, so yake ya gano ta inda ya fishi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41