Chapter 15
Chapter 15
iya haihuwa... Shiru tai ganin yadda Ummin ta 6ata rai. "Mey akai kuma ki ke wani 6ata rai ina magana?.. Baki ta ta6e,kan ta ja k'wanon namanta ta fara ci. A y'atsine tace "ya bazan bata rai ba?... Saboda t'sabar wulakanci tun jiya na haihu amma sai yau zaki wani zo kina nad'e taburmar kunya?... K'allonta take ba kiftawa, sam Ummi batta kunya.. Sai dai kawai ta basar. "Dadina dake Ummi baki bada uziri a koman ki.. Yanzu ina laifin kin haihu da magariba nazo da sassafen nan?... Baki ta ta6e kan ta had'iye naman bakinta. "Ki ce kinbi order mijinki dai Malama, amma bare nawa ne suka zo tun a jiyan?.. Karara tsoron mutumin yaci k'arfin ki k'wana biyu na fuskanta... Shiru tai dan bakin ciki, ba abinda ta t'sana irin a dinga cewa tana tsoron Ja'afar...K'wafa tai cikin ranta. Zuwan Aunty A'i ne yasa aka dawo mutunci kuma. Kullum tana gidan Ummi,duk dan gudun magana. Yau kam Ja'afar yace ta hakura gobe tunda aiki jibi kuma suna,yau masu g'yaran gida zasu zo. Ba tace toh ba,haka bata ce a'a ba. Sai dai duk ta sauya,tunaninta muddin yau take zuwa gidan Ummi,toh ba makawa sai sunce chaketa,hakan ya tabbata kenan ita mai tsoron Ja'afar ce. Tabbas lokaci yayi da zata nuna musu bata tsoron Ja'afar. Hakan yasa da k'warin g'wiwarta ta tashi ta bishi d'akin waje. Shiri yake yana son fita wajen ciciku cikun neman takaddun shi da ya kone. Yanayin da ya ganta ta dan kama kai yasan yau abin ya mot'so. Kawai sai ya kau da kai. Zama tai gefen gado tana k'allon shi ta gefe, "Haba Ya Ja'afar dan Allah... Yau daya kar kamin haka dan Allah, ka barni naje tunda an g'yara kitchen ga kuma d'aki muna dashi a waje bayan suna suyi aikin.... Ido kawai ya zuba mata,sai da ta kai Aya tukun yai magana. "Ke mey yau din zata miki in baki fita ba?.. Kullum fa tun haihuwar nan kina fita Salma,dan yau kad'ai nace ki hakura sai gobe shine ba zaki iya ba Salma? Fuska ta y'atsine, kan tace ita dai kawai ya barta ta fita toh. K'allonta yake,abu yai sauki yanzu tana son dawo da hali? "Son ranki za'a bi yanzu koh nawa Salma?... A gida na ban isa nace ga abinda za ai ba sai ace a'a?.. Meye haka kike son kawo wa kuma da ya wuce?.... Hawaye ta fara mishi,tabbas yau in bata fita ba,toh gobe fa sai dai ta toshe kunne. Haushi tai bala'in bashi,akan wannan shine harda kuka?.. Sam bai son abin da ya wuce a dawo dashi. Nan ta zaune mishi tana mishi kukan gardamar sai ya batta. Haka yanaji yana gani sai shi ya sauke ya barta yace ta shirya su je. Da murnarta ta shirya suka fita ya sauke ta. Sai dai shi sam baida walwala. Haka tai ta fita har ran suyar nama,washegari ma wai zata wanke gida,anan suka hau suka fad'o.. Ya ja ta ja,harda fad'in dama ance tsoronshi take ji. Ya rant'se da in har ta fita,toh zai maimaita mata abin ranar,wato ta fita a bakin aurenta. Tuni ta nut'su ta dawo hankalin ta. Tuni ya kashe bakin t'sanya,har ya fice ya barta tana kuka,harda dariyar mugunta... Ya k'wa gano lago ai. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Jul 29 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 21_Ranar ta fita a Napep ta layin su Ja'afar taga wani kamar shi tare da wata, har zasu wuce ta gane Bintu ce,da sauri tace mai Napep ya t'saya. Sam a yadda suke ba kace ba masoya bane,dan sai wani sunne kai take kasa halamar kunya. Tuni zuciyarta ta hau tafasa,ba shiri tai wajen gadan-gadan,dai dai suyi sallama harda dago mishi hannu. Kan ta karasa har ya juyo itama ta tafi... Ganin yanayinta shima ya dan tsorata,amma sai ya maze. "A'a, har kin fito?.. Harara ta sakar mishi kan ta k'allo Bintun da har tai mata nisa. "Ban sani ba... Ashe dama zance ka fito shine kace na hau adaidata koh?.. Kuma da Bintu?.. Har kana wani yage mata baki... Hannu ya kai kan bakinshi halamar tai shiru yana duba layin, "Haba Salma,a titi fa muke,kiyi hakuri ba abinda ki ke zata bane ba... Harara ta kara sakar mishi,kan ta farga har ido ya ciko da hawaye. Tabbas yau ya tabo jaraba... Dan sarai yasan Bintu kam sonshi take,kuma Salma ta sani. Akan kishiya k'wa, yasan sai Salma taki ci taki sha. Tuni ya hau lallami harda rantse rantse kamin ta yarda bayan anje gida. Wataran yakan yi tunanin koh Salma na da Aljanu,in ta tashi sauya hali tafard daya ne,sai dai in ya bud'e mata wuta su shirya. ~~~~~~~~~~ "Shiru ake jinki makociya,koh dan ziyarar yamman nan an daina zuwar mana sai jefi-jefi, koh mutumin har yau yana nan da kullen?... Baki ta dan ta6e,kan ta bawa maman Ummi amsa. "Ai sai abinda yai gaba, yanzu tunda akai abinnan na farko abu kadan sai ya kafan sharad'i kan in na t'sallaka a bakin aurena, ina gudun rabuwar mu,yanzu ma minti goma ya ban na dawo. Baki Maman Ummin ta ta6e, "lalle kina da aiki in dai mazan nan ne, saf zasu mayarka marar y'anci in bakai ma tufkar hanci ba,harda lokaci? Tab aiki.. Ga gobe sunan _nurse_ din layin chan (Maman Nuwaira),ke koh barka baki je ba, ke kinsan za'a watsa karya kiyi kok'ari ya barki muje. Kai ta k'ada, "Ai dole,dan wallahi baza ai bani ba,ko bai bari ba naje koh minti ashirin ne a wat'sa warishan nan dani. Hannu Maman Ummi ta bata suka tafa harda shewar su,ana haka Ummi tai sallama,kan tunda ta shiga Jafar yace tana nan ta fito,wai sai had'a rai yake,shi yasa ta bar mishi gidan, nan ta daura kan na Maman Ummi, Zuwa chan Maman ummin tace "Kiyi kok'ari hudu ki biyo min zuwa 5 dawo. Da wannan suka baje har ta wuce ka'idar Ja'afar. *Washegari*. "Wai dan Allah Salma na tambaye ki zaki ban amsa? Y'atsine fuska tai kan tace "ina ji.. "Shin dad'i ki ke ji in kin t'saya muna musayarya magana dake?.. "Mey yasa in na ce ki bar abu sai dai nai son ranki,amma ni ban isa ba? "Ita maijegon ta ta6a tako kafarta cikin gidan nan da sunan tazo gunki?.. Ki ban amsa? Baki ta saka,kan tace "oho,kana nufin gyaiyar sod'i zani kenan?.. Tunda ga areni muje biki koh?.. Kai ya kada, "Ke ki ka kira kanki haka,ba Ja'afar ba,abu daya na sani,ko na fita ba jimawa zanyi ba, saboda in ma kin fita,toh kisan inda dare ya miki... "Mey ka ke nufi? Kana nufin yau ma zaka ce a bakin auren nawa Ja'afar?.. Da sauri ya kada kai, "K'warai,tunda abinki naga na yanzu har so yake yafi na da, in har kam kin fitan,toh kisani,kin fita *A BAKIN AURENKI*... Sai ki zabi wanda ya fi miki, aure? Koh gidan suna?... Kofar ya bugo mata yai waje tare da barinta baki sake. "Eh lalle yau zan nuna ma tabbas ba tsoron ka nake ba Ja'afar... Wannan kurin bakin wallahi bazai hanani fita sunan ba,daga yau kalmar nan ta *A BAKIN AURENKI* tabar bakinka. Daki tai tana balbalin masifa ita kadai kamar yana k'allonta. Kaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41