Chapter 18
Chapter 18
zama dole. By Feenat Ja'afar. Juma'@ Mubarak. 9/29/16, 9:07 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24-Kai ya kada tare da mikewa, "kiyi hakuri Salma.. A baya na baki d'ukkan wata dama taki kinyi watsi da ita.. K'arfi da yaji so ki ke ki mayarni wani iri,dame zanji Salma?.. Na fita waje na samo 6acin rai,sannan na shigo gida nan ma wani 6acin ran ne,maimakon a lallashe ni..A'a ni kullum ni nake lallashi. "Kiyi hakuri,Allah ya baki lafiya.. Garba ya k'allo yai mishi halamar su tafi. A hankali ta mike tana jin wata irin hajijiya na debarta. "Nasan ni na ja ma kaina komai Ya Jaafar... Ja yai ya t'saya, jin taci gaba yasa ya juyo. "Tabbas na chanchanci d'ukkan wani hukunci da zaka min in dai zaka yafe min.. Kasa tai da kai,tai matukar zama abin tausayi a gunshi,sai dai kawai ya kasa gane nadamar Salma a yau,dan ta saba, ga kafa sai ka'rkarwa take. "Amma dan Allah wa zaka aura?.. Ba dai Bintu ba?. A yadda ta t'sareshi da ido yasa ya kasa magana,sai ya kalli Garba,kafad'arshi ya daga mishi halamar ba ruwan shi. Sai da ta maimaita kan ya daga mata kai. Murmushi tai da yafi kuka ciwo,a hankali take neman juyawa wani kanta ya sara gami da ganin duhu. "Kar ki min fassara Salma,ba abinda ya had'ani da Bin... Luu ta fara halamun zata fad'i, cikin zafin nama yai taku daya ya taro ta. Gaba d'aya jikinta ya saki,ga wani irin zafi kamar garwashi. "Salma.. Jijjiga ta ya fara,da sauri Aunty A'i ta shigo,sai ga Mama na fad'in ta taimaka su sa Salman a Napep gashi ta nemo.. "Mey zan gani haka... Da sauri suka juya ganin Mama da tai turus ganin yadda ya mammakale Salman,ita k'wa k'allonshi kawai take hawaye nabin gefen idonta. Garba ke mishi da hannu kan ya saki Salman amma kamar yana zigashi,sai kara naneta yake. Gaida Maman sukai da girmamawa tai banza dasu. Sababi Mama zata fara Aunty A'i ta jata sukai waje. Garba ne ya tsayarshi ganin yana neman cicci6ar Salman. "Kasan dai yanzu ba a mat'sayin matarka Salma take ba,kar ka nemo mana magana dan Allah.. Harara ya sakar mishi,kan cikin fusata yace "na mayarta toh.. Koh da magana? Kai ya k'ada mishi, kan ya bud'e mishi labule, "Dan Allah kaimu asibiti... "Auntyn mu.. Aunty A'i ya k'wada ma kira, da sauri suka fito ita da Mama dake huci. "Asibiti zamu kaita, dan Allah Mama ki yi hakuri na kaita.. Harara ta sakar musu kamin tabi bayansu ta sallami mai Napep sai asibiti. Murna ta koma ciki,da d'ukkan hannu biyu mama ta dafe kai,jin rahoton likita kan tabbatar da cikin Salma,dan haushi ba tasan tai waje ba. Shikenan an 6ata mata shiri, ciki?.. Kai amma an sha da ita, sam ta zata fad'in A'in ne dan a bar Salma. "Mama kiyi hakuri zata samu lafiya,bari naje na siyo allurori mu dawo. Kala bata ce musu ba, asalima ji tai kamar ta rufeshi da duka koh ta huce. A gun Garba ya k'ar6i kud'i,basu juma da tafiya ba sai ga Ummi da Aunty A'i sun zo,tuni k'wa ta ware tana surfawa Ja'afar Ummi na tayata. Kai Aunty A'i ta k'ada, fatan ta a kullum Allah ya ganar dasu Mama alkairin Ja'afar, alkairin da batajin koh su wanda suka auri masu halin suna musu. "Mama Salma fa matar Ja'afar ce har yanzun,don musulunci ya mallaka mishi,matukar batai idda ba,bare da kunne na naji yace ya mayarta wallahi, dan Allah Mama ki sassauta, in har da mey lefi aciki toh fa Salma ce.. "Ke dama ina kika ga kishin kai?.. Ai guntunki ta tsotsa, shi yasa sam kusan halin ku daya... Aure kuwa in dai ni nai nakudar Salma toh ya kare ya gama.. Ba ruwana da wani ya mayarta,sakaryan yaro kawai,sam bai da zuciya wallahi. Ummi ce ta amshe tana k'wafa. "Ai wallahi dad'i yake ji dan yaga Abba na jibgarta,dama garin d'ukan yaja ya rasa cikin ai da shi ya jiyo... "Ummi mey yasa ke sam baki da mutunci ne?.. Baki Ummin ta turo, "Ja'afar fa ba sa'anki bane,in bazaki g'yara ba toh kar ki 6ata... Salma ita ta chanchanci komai ba Ja'afar ba,gashi taja yace aure zai kara... A zabure Mama ta jiyo, "Aure?.. Shine ki ke kuma fad'a min ya mayarta?.. Kai ta k'ada, "eh lalle Ja'afar, toh k'wa zama da kishiya ba dai y'ata ba, karan nan zamu banje da Malam wallahi akan maganar komen nan,sam naki jinin yaron nan wallahi.. "Ni kam Mama bana ganin aibun Ja'a.. "Kimin shiru,kar ki gani din,amma aure angama. ****************************** Yau k'wananta biyu aka sallame ta,fur Mama taki bawa Ja'afar fuska,daga ina wuni lafiya shikenan. Su Abban su Ja'afar harda y'an cikin gida sunzo sun jajanta abinda ya faru. Kowa ya bawa bangarenshi rashin gaskiya, take Baba yace ya mayarta. Kai duk'e yace ai tun ranar chan ya mayarta,nan ya ja mishi kunne kan sarar ki fita A BAKIN AURENKI. A gaban su Abba ya kara tasa zancen zai kara aure,cikin fusata Abbanshi yace "Ba mun gama maganar nan da kai tun jiya?.. Wane aure kuma bayan wannan da aka mayar? Kai yai kasa dashi yai shiru, murmushi Abban su Salma yayi,kamin yace "Kamin dai dai Ja'afar, fatana Allah yasa auren shi zai zaunar da Salma a dakinta ta rungumi ibada. Ja in ja sukai tai t'sakanin Abban Salma da Abban Ja'afar, dak'yar Abban Ja'afar ya yardewa Ja'afar kara aure. Ana watse wa koh gama jan mota basuyi ba Mama ta fara sababi,ita a fafur ba inda Salma zata,bata zauna da kishiya ba,saboda haka ba mai zama da ita a yaranta. Itade Salma bata um bata um- um,sai hawaye kadai ke zuba,ita kad'ai tasan ya zuciyarta take hautsina mata,ta faru ta kare,tunda har manya sun amshi magana. "Ja'afar? kishiya? Kuma da Bintu kawarta?.. Tab da matsala. By Feenat Ja'afar 9/29/16, 9:10 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 24_Daaga sosai akai da Mama akan komawar Salma,sai da Abba ya bud'e mata uwata sosai kamin harda Yayanshi ta saki aka ta koma din. Ita kanta Salman yanzu ba kaunar komawar take ba sai ta mot'so mata ga laulayi. Ga Ja'afar tunda ya ji batun ciki ya kasa sukuni,kullum yana zaryar dubiya da leda. Shi dai bai mat'sa da sai ta dawo ba lokacin, dan g'yaran gida sosai yake wanda Ummanshi ta bashi ya zauna aciki. Har gida yau Abba yaje gun Abban sun kan lalle yau Jafar yazo ya dau Salma. Da dare k'wa ta koma dakinta. G'yaran nan gidan ya t'saya chak,sakamakon aikinshi da aka mayarshi aka bashi albashin da ya wuce shi,bai da mat'salar kud'i yanzu,auren shi kawai yasa a gaba. "Ina k'wana.. Cikin sanyin murya ta gaida shi kai duk'e, kai ya daga kamin yace "ya jiki?.. Shiru tai ba amsa. "Ki tashi ki zauna man.. Kai ta dago ta k'alleshi kamin ta kada mishi, "A'a magana nake son muyi da kai. Zama ya g'yara yana sauraranta. "Mey yasa ka ke son auren Bintu?.. Da ido ta kafeshi tana jiran amsa. Murmushi yai kan yai baya kad'an harda d'aura kafa daya kan daya. "Saboda tana so na ne Salma.. Kai ta kada, ''kaima kana sonta?.. A bazata tambayar tazo mishi,ga takafeshi da ido
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41