Chapter 24
Chapter 24
balbalin bala'i sai dai ni na bar mata. "Yanzu da banzo ba Allah kad'ai yasan mey zatai ma y'ar mutane,k'alli a halin da take fa,amma Salma taki k'wantar da hankalinta ai zaman lafiya.. "Ni fa kar ma ka zata kishi nake da kai koh kuma waccan amaryar taka,sam ba haka bane,ni mud'in za'a tada min hankali toh lalle na kowa zai tashi... _period_. Aunty A'i ya k'allo halamar tasa baki. Tambayarta take mey ya had'a su?.. Amma fur taki magana a gaban shi,har aka gama sulhu yace ta taso su koma tace sai dare. Da kai Aunty A'in tai mishi kawai kan ya k'yaleta. Ba musu ya tashi kan sai ya zo,yana fita ta mike tai kitchen. Tana cin abinci Aunty A'i na mata fad'a, kan ta d'aina fada Ja'afar na fada,dan ta fuskanci Bintu ta iya bariki. Nan ta fad'a mata ainashin abinda ya faru,harda irin habaici da sharrin da Bintun ke mata kullum. Baki ta ta6e. "Ni fa Aunty A'i Bintu bata gabana, abu daya na sani na tsani a gabana yana biye mata tana mishi abinda taga dama.. Yana konan rai ne,shi yasa yake rasa kaina. Murmushi tai mata, "Lalle Salma kina so Bintu ta kai ki ta baro, kin kuma yi saken da kika bari kishiya har ta gano lagon ki,dole yai ta ganin bakin ki ke kadai,dan ke kadai ki ke iya daga jijiyoyin wuya agabanshi akanta,in sharri ma ta miki ki barta da Allah kawai,shi zai isar miki,kar ki manta igiya daya tai saura a t'sakanin ku da Ja'afar, kuma kince ta sani,toh wallahi ki sani ingiza mai kantu ruwa kawai zata miki,so take tai ta tunzuro ki har ki tafka kuskuren da za ai mai dika, kinga taci galaba kenan. "Gaba koh abinsu suke kina d'auke kanki a kansu, sannan abu in kinga zai ja ki fad'i wata magana musamman kan Ja'afar kiyi shiru kar ki tanka dan Allah Salma. "Ja'afar na sonki,kiyi amfani da hakan sai ki ci galaba kan Bintu.. Har ta gama mata fada tana ta nazarin abin,toh Allah yasa ta iya k'auda kan. Ita kwa Bintu murna fal rai,dan tana lekensu ta k'auran zauren, fatan ta Allah yasa yadda ya figi machine din nan in yaje kawai ya dankara mata saki. Shi yasa tun kan ya dawo taje ta t'sant'sar wanka ta hau kananan kaya, duk da ba ita ke dashi ba. Ita a ganinta an sau Salma an gama,.. K'warai ta gode da shawarar su Aunty Ladi ta waya da ta yau,tabbas da BARIKI kadai zata mallaki Ja'afar ba boka ba Malam. Sai dai har dare ba Ja'afar ba dalilin sa,kawai sai ta zata bai gama hucewa bane,tasan mutumin ak'wai saurin zuciya. Dirin machine dinshi taji,da sauri ta kara fesa turare ta haska touch light tai zauren da zummar taro shi yasha Bariki. Turus taja ta t'saya gabanta na fad'uwa, ganin ya mike yana fad'in ma Salma "Dafani man toh,ban san ki fad'i ne garin sauka. Da kamar kar ta kulashi,amma ganin hasken fitilar Bintu yasa ta hau shagwaba. "Toh ni kam tsoron sauka fa nake tunda cikin nan yai girma,in zaka iya ka sauke ni toh... Ta karasa da kalar tausayi. "Toh toh,amma ki kokarta,ki rikeni gam, koh ki bari na fara sauka... Kofar Bintu ta saka da sauri ta koma ciki dan bakin ciki. Tana jiyo su a t'sakar gida Salman na fad'in "Wash.. Allah Ya Ja'afar kafata rikewa take fa.. Tuni gogan ya hau rikicewa abinda aka jima ba'a mishi ba yau yake gani,bar zuciya da abinda take so. "T'saya na d'auke ki toh ai kina ma kok'ari.. Tana jiyo Salman na fad'in "kai Ya Ja'afar, anya zaka iya kuwa?.. Nayi nauyi fa yanzu. A zabure ta mike ta tana lekensu ta window ta cika tai ham. Dariya suke k'yak'yatawa kan yace"bari ki ga,nawa ki ke.. Da sauri ta sau labulen ganin ya k'wa daga Salman ya dauke kamar y'ar tsana suna dariya. Har d'aki ya dire ta suna nishad'i kamar ba su bane dazu an bar Bintu da kukan d'aki. Sai yanzu ya tuna ai koh sallama basuyi ba suka shigo. Murmushi tai mishi lokacin da yace bari yaje ya dawo. K'wafa tai tana kada kai, "kowa ya iya BARIKIN ai,in na baje tawa sai kin ji jiki Bintu. Yau da sauri-sauri yai ma Bintun sallama yana ta zumudin sun dinke da ta k'arfen. Kuka wiwi tai tayi bayan fitarshi. A gaban mudubi ya tarar ta tana g'yara gashi,kowa farin ciki fal ranshi,ta baya ya sakalo cikin yana shafawa harda sakar ajiyar zuciya. Murmushi tai mishi,tare da shafo siririn sajen shi ta bayan, sai ya k'wanto da kanshi wuyanta suna ma juna murmushi ta jikin mudubin. Yaushe rabon su kasance haka shi da Salman sa?.. Ga y'ar shagwa6ar nan yau yana shanta,duk sai ta mantarshi komai. A hankali ya rad'a mata a kunne "I love you... Murmushi tai kan ta juyo tana lumlumshe ido jin dad'in kalmar, lafewa tai jikinshi tana fad'in ''Me too.. Sosai yasha mamakin Salman shi yau,komai yi mishi take cikin kauna da kulawa, kamar farkon aurensu kamin komai ya wargaje. Hakan yasa washegari kowa fuskar nan kamar gonar audiga dan fara'a, amma banda Bintu Lol. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 28_Tun daga ranar aka dinke da Salma da Ja'afar d'inta, sam ta d'aina sanya da abinta, shima abin nema ya samu,wai ! Matar falke ta haifi jaki. Kan kace k'wabo,tuni tsohuwar soyayya ta dawo d'anya,sai ya zama kamar kamar yanzu ma tafi yawa. A cikin wata guda duk sun sauya,takanas zaice su fito aje siyayyar kayan baby,fur Bintu take kin zuwa,sai suyi tafiyarsu a kafa suna tadin su,sai jiran EDD. Kwana biyu Bintu an tsiri zaman d'aki,sai ta kule ka rasa abinda take aciki ita daya. Ranar tana bacci da safe wajen k'arfe goma taji kwkwazon maigidan yana tayi ba kakkautawa. Tashi tai ta fito parlour. "Na fita ban karya ba,yanzu ma na dawo ashe baki tashi ba, bayan tun asubar fari kika fara wannan charting din danaki jini a rayuwa,na hana kin ki hanuwa,toh ina gaf da fasa wayarnan a gidan nan Allah. Baki ta ta6e tare da tashi a hankali tayi d'aki dan fita wanka. Tana kallo ta fito wai yai hakuri ta daura mishi indomie,koh ta kanta bai bi ba yai waje yana huci. Kamar jira take,da dan gudunta ta koma d'aki ta dane Facebook cikin group din su na KI G'YARA DA KANKI. Kusan duk anyi katari masu kishiya sun da yawa, nan zatai ta samun shawarwari mey kyau da marar k'yau,dak'yar ta tashi ta d'aura jalof ta koma. "Wato sai yanzu nake hangen maganar ka abokina, dan yanzu abinda Bintu take har yafi mai na gantali ciwo,in ta hau wannan Facebook din nata,sam bata ji bata gani,abinci a kone, in ma ta samu d'aurawa kenan,sallah a kure,bacci sai biyun dare,da asuba ta d'aura a inda ta tsaya,ga in ka shigo kaji tana dariya ita kad'ai, Allah zaka zata Bintu sabon kamu ce... Dariya ya fara mishi harda k'yak'yatawa,har ya fara k'uluwa,yasan haka zata biyo baya, amma shi yanzu shawara yake nema ya zai da sabon halin Bintu?. "In ka gama kai magana sai ka bani shawarar abin da zanyi. Dak'yar Garba ya takaita dariyar ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41