Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,278 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Da sauri ta d'auke kai daga kanshi. Gaidasu tayi,budurwar na mata an dawo. Lafiya? A ciki ciki ta amsa,Garba yace "yaushe a gari? An gama lafiya _hope_? Da mamaki take k'allon shi,yanzu dama da wanda zai ce bai san y'an makaranta sun dawo ba? Kawai dai sai ta maze, "yau kusan satin mu da dawo wa. K'allo Ja'afar d'in Garba yayi,kan ya dawo da K'allonshi ga Salman. Ba wannan dawowar ba,yau k'wana uku da zuwan mu K'anwarki tace mana kinyi tafiya... Da sauri ta dago kai da mamaki,tana k'allo gun Ja'afar d'in ya d'auke kai. Garba yaci gaba, "zuwan mutumin kenan daga Zaria yace sai ya zo ya ganki ya miki murna,ashe ke har kin ma fice a garin. Batta bakin magana,dan bata san amsar basu ba,amma Ummi tana mata daya a rayuwa..wai tai tafiya? "Ga nan mutumin jiya har sururu yake yaganki da dare ina mishi t'siya, ashe ke ce. Kai ta daga,kan ta kara k'allon Ja'afar, d'anna wayarshi yake kamar bai wajen. Cikin wasa Garba yace "toh ni zan gabatar mata da ita ko mey da kai mikis?..kasan ba kunya zan ba ni. Murmushi budurwar tayi kai duk'e, dan sam bata ga fuska gun Salman ba. K'allon Ja'afar din take,yayin da yake k'allon Garba yai shiru. "Toh,mu bama sanya, sai ya juyo gun Salman, "Salma ga nan budurwa,kuma matar... Da sauri ta rint'se ido,kan ta karasa da "Ja'afar"... Na sani Malam Garba... D'uk ido suka zuba mata har Ja'afar baki sake,jin shirun yasa ta bud'e ido akansu,yadda suke k'allonta tasan tai su6ul da baka... Cije le6e tai,amma ta bada kanta wallahi.... Dariyar keta Garba yasa harda k'yak'yatawa, sai ta dago tana k'allonshi. Sai da yai mai isarshi kan ya k'allo Billy, "Haba,Yanzu na ji batu,ni fa naga kowa yana sassahan kamshi,ashe-ashe...uhm uhm _Jealousy_... "Toh wannan Matar Garba ce bata Ja'afar ba,sassauto madam. Wani irin sanyi taji ya ziyarci zuciyar ta,har batasan sanda murmushi ya su6uce mata ba. A kunya ce ta k'allo Billy,sai ta mat'sa kusan da ita kan tace "sannu da zuwa... Dariya suka sa mata banda Ja'afar da ya dan dara,idonshi kir a kanta,bazai iya fassara mey hakan yake nufi ba, shin Salma na son sa da kishin sa ne koh mey? Ita dey sai dan satar K'allonshi take,amma bazata iya fassara ina ya dosa ba. Mota su Billy sukai suka barsu,ga nan magriba ta gabato,gaidashi ta kara yi itama ciki ciki,t'sayuwa ya g'yara kan ya amsa,tare da mata murnar kammala karatu,shiru ba mai cewa uffan,kowa miskilin kanshi,kawai sai sukai sallama kan gobe zai zo. Tana shiga gida dan takaici kasa ma Ummi magana ta cikin fad'a."yanzu Ummi kina k'yauta min kenan a rayuwa? Mey Ya Ja'afar ya t'sare miki ne ki ka ki jinin shi? Rai ta had'e, kan tace "oho,kawai bai min bane... Ga nan sakon daga Muzammil,kinga in da ake harka ai... Kai ta k'ada dan takaici tai d'aki batabi koh ta kayan ba. Washegari dan kalata sai ga su sun dawo, ana la'asar, mama ta fita unguwa. Ado Ummi ta ciwo da tafi na jiya,sakare tai ganin Salma koh mot'sawa batai ba. "Koh ba zaki bane Salma? A tunzure tace "ba zani ba.. Baki Ummin ta ta6e,kan ta daga kafada, "mat'salar ki ce wannan kuma... Sai tai waje. Aiko yaro sau biyu ana yi daga waje daga Muzammil amma fur taki fita. A ka'ro na uku ne yaron suka shigo da Mama da ta dawo daga unguwa. Dole ta tashi badan rai naso ba,sai dan ganin Ummi ta shigo ta had'a ta da Mama kan taki zuwa gun Muzammil. Tana had'a rai ta fito,sai dai da mamakinta taga Ya Ja'afar t'saye yana aiken yaro kan tazo. Da sauri ta koma cikin zauren kan ya ganta. Jim tai kad'an bayan fitar yaron kan ta fito,kanta t'saye tai gun Ya Ja'afar, kan tace ya bata minti biyu dan Allah. Kai kawai ya k'ada mata,sai tai gun su Ummi,a mutunce suka gaisa,kan tace da Muzammil sakon shi sai gobe.. Bata jira amsa ba tai gaba. Shi kam Ja'afar k'allonta kawai yake,amma tuni har yazo wuya. Tabbas dole ya bayyanawa Salma yau ranshi ba sai an k'wana ba,dan wannan samarin tsaf sai su iya kasa shi yana k'allo. "Bissmillah, muje zaure... Bai yi musu ba yabi bayanta. Har ya dan saki fuska, dan sam ba kaunar zaman ta a layi yake ba. Bayan sun gaisa yake bata labarin abinda yasa bai je mata ba. "Kinsan Mamana tana a Zaria ne,sun rabu da Abba tun ina dan shekara biyar,hakan ya zamana Abba ya k'ar6e ni a dalilin tai aure,nakan kai mata ziyara haka,sannan dan ita na zabi zuwa Zaria karatu. A _time_ d'in da za ai _visiting_ aka aiko bata lafiya,chan naje har t'sawan wata uku. "Taji sauki sosai,har tana ta fad'an na koma bak'in aiki na,ana haka y'arta K'anwata ta dawo sun gama makaranta,hakan yasa na tuna da Salma.. Nan nai shiri na dawo,duk dan na ganki,sai aka samu akasi, Ummi tace kinyi tafiya... Shiru yai kai duk'e, itama tai tsam tana sauraren shi. "Salma"...kai ta dago ta dan k'alleshi, shima idonshi a kanta. "Yanzu kam lokaci yayi da zan sanar ki wani sirri,sai d'ai ina fatan wani bai rigani yad'awa ba... "Salma"... Cikin wata siga ya fad'i, kan yace "na jima ina dakon son ki azuciyata,tun ma kan Salman tasan itace... K'allonshi take baki sake,shikam ya zage sai tona sirrin ranshi yake a gare ta ido bud'e.. Dad'i, farin ciki har ya kasa misaltuwa a gun Salma,So d'aya ne, tasan Ya Ja'afar tai ma. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 8:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 13_Har yai shiru ita kam idonta na kanshi,kan dafa bisani tai kasa da kai cike da kunya,kawai shima sai ya zuba mata na mujiya yana murmushi. Magana suke jiyo wa kasa-kasa,duk sai suka zuba ma kofar ido. "Ba mutunci ace kowa yana wuce wa yana ganin ku a t'saye a titi, gaba na fad'a miki ki nemi koh zaure ne koh cikin gid... Shiru Abban yai dan ganin Ja'afar a zauren da Salma. D'ukawa ya danyi kan yai ma Abban sannu da zuwa. Cikin sakin fuska Abban ya amsa,Salma ma ta mai kai duk'e. Sim-sim Ummi tazo ta wuce,dan duk iskancin ta tana bala'in tsoron Abban su sosai. Yana shiga gida shima yai mata sallama da alkawarin gobe zai zo dan jin amsar shi. Da t'sananin farin ciki ta shiga yau, haka dashi ta tashi. Tun jiyan Ummi ke ci mata kunu, tasan kuma d'uk akan Muzammil ne,shi yasa koh bi takanta batai ba. Washegari tun kan Ummi ta shiga wankan yamman ta na kullum Salma ke gaban mudubi, sosai take k'yali, yau d'aya ta bata lokaci dan Ja'afar d'inta. Ummi da tun dazu ta fito tana jira ta ta6e baki, ''kiyi kare ni ki ban waje na zauna Malama... Juyo wa tai da tana yage mata baki, "dan Allah Ummi nayi k'yau?.. Bar zancen wasa. Baki ta ta6e kan ta juyar da kai gefe, "oho miki ni kar ki daman. Murmushi tai kan ta tashi ta bata gu. Bincike ta fara,a babu babu Mama kala 5-5 ta musu kayan _candy_ na ke ce sa'a, ciki masu ruwan _purple_ ne kusan duk. Cikin nishad'i ta ciro attamfa wata mai _purple_ da rat'sin _yellow_ riga da siket,

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});