Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,253 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zo min? Har nayi fushi ai.. Baki sake Salma take k'allonsu,tana k'allon suna nuno kofar dakin da baki suna ma Bintun kuskus tai baya da sauri. Ido ta rint'se tare da cije le6e,lalle mutum mugun ice ne,yanzu ta gane inda Bintu ta samo duk wasu _information_ na zaman aure nata ba agun Ja'afar ba,ido ta bud'e, ta d'au alhakin Ja'afar, har rantsuwa yai mata amma taki yadda. Karshe har raba shimfida tai dashi akan maganar har sai da ya gamo ta da Aunty A'i aka shirya. Zama tai tana jiyo shewarsu a dakin Bintun. Har kullum bazata daina nadama akan taraiyarta dasu Maman Ummi ba,tasan duk fushin Ja'afar ne da t'sinuwar mala'iku ke bibbiyarta. Har hawayen bakin ciki tayi yau,tai kuma alkawarin daina sa6awa mijinta ko da taji haushin shi. T'sakar gida ta fito bayan ta g'yara fuskarta, tai sa'a kuwa sun fito zasu tafi suna ta dariya. Ganinta a t'sakar gidan yai bala'in saita nutsuwar su,a t'saye take k'yam tamkar wata soja ta had'e rai tam,ido cikin ido take k'allonsu,tuni suka hau inda-inda, "dama kina ciki?.. Sannun ku da gida.. Harara ta sakar musu,ba shiri sukai hanyar waje,Bintu ce ta t'sayar su, "bari na raka ku hanya Aunty,ina zuwa na kira mai gida izinin fita. Duk tana k'allonsu,har tai ma Ja'afar waya wai za tai rakiya waje ya bata izinin fita. Bokiti ta zaburo da sauri tai hanyar fita,da sauri sukai waje sun zata kansu zata iyo,kawai sai ta ja t'saki ta shige band'aki. "A toh na zata koh rafka mana zatayi ai,g'wara muyi ta kai ta kai,dan wannan da gani zatai kishin hauka... Dariya suka sa tana jiyo su ta band'aki daga zauren sunki tafiya. Ruwanta na cika da ta tara ta bud'e band'akin a hankali tai zaure, basu nufa ba sai jin saukar ruwa sukai akansu har Bintun. Bokitin ta d'auka tai kansu dashi a sukwane, da ture ture suka fita waje da gudu. Tana haki ta leko kofar gidan ''Ashe karyar munafurci kuke, da ku t'saya na g'wada muku aikin mahaukaciya, shegu gadon na aiya,a haka zaki kare Maman Ummi wallahi, InshaAllah kema dubinki ta kusa cika. "Ke kuma yau mai rabani dake a gidan nan wallahi sai Allah, yau zaki ga karyar iskanci. Gida ta koma tana hakin daga ruwa bucket guda da tsohon ciki. A t'sakar gidan ta zauna tana maida numfashi a hankali, ta jima da zama kamin taji tafiyar Bintu cikin sand'a, kofar ta zubawa ido tana harara, kai ta leko dashi dan ganin koh Salman bata nan sai suka had'a ido. "Wallahi baki isa ki ce zaki hanani shiga ba, in gaske ne ki bari na shigo na shirya in fad'an ki ke nema dani ba hauka ba. Murmushi tai daga inda take, "Lalle kinyi kuskure in kina zatan zan iya had'a jiki da karya irin Bintu,haukar nake son sauke miki aka yau ai, gaba kin d'aina irin kuskuren nan ina zuba miki ido kawai,yau dole na fidda ki cikin gona ta. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's "Karya ki ke wallahi ki iya koyan hankali Salma,ai fad'a da makami tsoro ne,ki ajiye bokitin mu gabza da hannu in kin is... "Meye hakan ke kuma Bintu?.. Juyawa tai da sauri,tana ganin Ja'afar ta sau kukan munafurci harda kank'ame shi,wai Salma tace in ta shigo sai ta kashe ta da duka da bokiti bayan ta jika su ita da bakin da zata raka... Ciki yai gadan-gadan gun Salman,tana ganinshi ta mike t'saye rike da bokiti,bai watawataba kawai yai kanta da niyar mari tai baya. Kunci ta rike har tana halamar yin baya zata fad'i, "Kin haukace ne Salma ko mey?.. Gidan ki ne da har zaki kafa dokar wa zai shiga ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace "eh wallahi, da da halin duka ma sai na miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada, kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi, "Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira.. Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara.. Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Jul 31 Feenat Ja'afar Novel's *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 27_Tun kan Napep ta t'saya ta mika mishi kud'in, da sauri ta shige gidan Aunty A'i fuska duk hawaye. "Toh kiyi min bayani man ba kuka ba Malama,mey aka mi... Wayan Aunty A'in ne ya hau ruri Aslam ya miko mata. A takaice ta k'alli Salman sai tai waje dan amsar wayar. Tana ji tana waya da Abban Aslam kan zata shigo da Ja'afar. "Dan Allah karki shigo dashi,wallahi ban san ganinshi,gwara in na huce da kaina zan koma. Baki sake take k'allonta hijab a hannu, "Ok,kina nufin yaji kika yi kenan?.. Shiru tai mata tana ci gaba da goge hawayenta. Bata kara bi ta kanta ba tai waje. Ba'a jima suka shigo tare,kai ta kautar gefe, tana jan hanci,ido yayi luhu-luhu dan kuka. Abinda ya faru ya t'sarawa Aunty A'in, tuni ganin duk ita ya d'aurawa lefi yasa ta hau musu bori ba shiri. Ido kawai Aunty A'i ta sa mata. "Auntyn mu kin gani koh? A gabanki ma kenan,wallahi na rasa rikicin Salma sam yanzu,abu kadan yanzu zata hau

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});