Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 41

Chapter 41

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 543 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bata shiga ba ga y'an uwanta suna ciki? Kai a kasa tace "Abba ban tambayi nan ba ne,dan jiya munzo yini. Murmushi yayi na jin dad'i, "hakane kinyi tunani mai kyau,Allah ya miki albarka. Kai ta kara kasa kamin ta amsa. Kud'i ya ciro daga aljihu ya kirga dubu ya bata,dan sosai Salma tana wa mutane bazata,yana matukar son mutum mai gyara kuranshi. "Sannu da jira uwar y'an ka'ida... Juyawa tayi daga kallon wani a mota sun tsaya da Kawunsu da ya wuce yanzu,sai dai kan ta tantance su Ummi sun fito. Murmushi ta mata tare da basar da zancen suna tafiya. "Wannan ai wahala ce,ace duk inda zan shiga sai miji ya ban izinin shiga?.. Kai ta girgiza, "gaskiya da sake.. Hararar da Aunty A'i ta mata ne yasa tai shiru. Kallo Ummin tayi da murmushi, a irin hudubar nan a baya suka dilmiyarta,ita kwa yanzu a shirye take da yima Ja'afar biyayya matukar bazata sa6a Allah ba. Har akaje gida nan ma Ummin ta hau zaiyyanawa Mama halin da Salma ta tsiro, tuni Mama tai mata kacha-kacha,Ummi harda kukan takaici ranar. Da dare yazo ya dauke su,sai taga a motar Garba da kamar ta ganshi dazun. Taga anje gida yana kokarin rufe mota da abin rufa sai ta kasa d'aurewa ta tambayi nan zata kwana? Murmushi ya mata tare da bud'e gida. Sai da akazo kwanciya yake sanarta ai shine albishir din dazun da yace sai sun zo gida. "Ya sai sabuwa ne,sai mukai cinikin wannan dashi tawan, munyi abin hawa. Murna tai ba kadan ba tana k'allon mukullin motar. Ido ya zuba mata yana kallo ba koh kiftawa. Baki ta kai kan idon tare da hurewa. "Salma.. Hankalinta ta bashi tana murza yatsunshi cikin nata. "Daga yau na yard'e miki koh ba idona ki taka ko'ina u r free... "Dazun naga komai Salma,ina horn bakiji bane,kin sani farin ciki dazun kinsa naji ni din na isa gun matata.. Duk inda ta tambaya nan zata jefa kafarta. "Sai ganan kuma kawu shima ya labarta min yadda kuka yi sai murnar wai kin san ya kamata yake.. "Nagode sosai,yau har kawu yasan ni mai fad'a aji ne a gidanshi.. Murmushi tayi tana kara ruk'unk'umo shi. Ta gode Allah da yasa ta gyara dabi'ar ta maras kyau ta maye mai kyau. Fatanta duk wata mace mai irin halinta ta daina,dan ita taga misali akanta. Dan a yanzu rayuwarta ta fi mata dad'i da kwanciyar hankali, ta gane yanzu kulle ma wasu matan ke ja ma kansu, tana fatan kowacce mace ta guji fita a bisa sharad'in *A BAKIN AURENKI* da suke yi,dan gudun haifar da saki irin nata mai gabadaya. Alhamdulillah.. Nan na kawo karshen littafin A BAKIN AURENKI.. Ina rokon Allah kuskuren da nayi ya gafarta min. Da fatan darasin ciki ya isar masu halin Salma za kuma su gyara,Allahu ya datarmu aikin kwarai a gidajenmu. Gareku dubin masoyan Feenat Novel's, na gode kwarai da kaunar ku gareni,Feenat na son duk mai sonta, dama wanda bai yinta.. Luv you all. Sai kun sake jina a sabon littafi mai sunan... *RABO IN YA RAT'SE*... Nafisa Bashir Tanko, (Feenat Ja'afar) ke muku fatan saduwa da alkairi.

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});