Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

A Bakin Aurenki Book 1 Complete Hausa Novel – Salma’s Painful Return 1,264 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dawo,da harara ta bisu har sukai waje. "Jishi kamar wani dan daudu rike da jakar mata. K'wafa tai tana tashi t'saye, "Ba dai kin fara fita ba?.. K'wanan nan zaki yabawa Aya zakinta wallahi. ** K'wana biyu yau tayi tana fita yawan arba'in, yau ne na uku,yau kuma aka tafka t'siya da maigidan,dan fur yace ba inda zata je. "Bazaki k'waso ma yarinya rana ba fa,kiyi hakuri kawai. Iya wuya Salma ta kawo dan takaici, tayi magiyar yaki kuma,kawai sai ta raya mata tunda dama taki bari ta koma hagu. "Amma gaskiya baka min daidai ba Abban Miemie in har ka hanani fita yau. "A ka'ida sati ake fita yawan arba'in fa,amma ni na yarda zanyi ukun shine har na gama shiri amma kace bazani ba... Gaskiya da sake. Gefe tai da kai tana kunkuni,tuni ta kular dashi shi zuciya kusa. "Toh ban hanaki ba kije d'in, amma ki ajiye min y'ata ki tafi ke kad'ai. Baki sake take k'allonshi,ganin yadda ya fidda waya yasha kunu ya barta. A zuciyarta tace "Eh lalle,da gani abin Ya Ja'afar yazo da wulakanci... "Kasan dai ba yadda za ai na tafi na bar Miemie a gida,dan Allah in wasa ka ke ka bari,dan kam nasa rai da fita yau.. A tunzure ya mike da niyar magana cikin masifa,sai yai shiru yana k'allonta. "Kiyi toh gaban kanki kawai.. Sai yai waje da zummar barin gidan ma dan haushi. Sai dai mey?.. T'saye yayi yana binta da k'allo galala, ganin yadda ta fara kame-kame dan ya kamata tana musu la6e ta window. "Ke kuma lafiya kike abu kamar marar gaskiya?.. Dakewa tayi tai ganin kamar bai ramfota ba. "Dama zuwa nayi ina son na leka nan na dawo ne... "Ba mai fita yau acikin gidan nan in dai ni ne mijin, wacce ban isa ba ta fita nagani.. A fusace ya fice yabar gidan,duk sai ta Salma tafi zafi. Ita kam Bintu dariya tasa harda shewa, "Yau karya ta kare,sai a za6a zaman gidan miji koh fita yawan gantali gard'i... Tana jiyota tai banza da ita tana hawayen bakin ciki. Waya ta d'auka ta kira Aunty A'i kan abinda Ya Ja'afar ya mata. "Salma kiyi biyayyar aurenki, dan Allah kiyi hakuri da fitar kawai. "K'wana biyu ai yayi ma,tunda kin zaga ko'ina ai har gidan su... "Aunty A'i ban fa wuni a gida ba kullum a ziyara muke wuni. "Ai duk fita kina zuwa,dan Allah kar ki dawo muku da hannun k'yauta baya man,kuna cikin zamanku abin sha'awa. Baki tai ta bata sai da ta tabbatar mata da ta hakura kamin sukai sallama. Haka tanaji tana gani ta hakura da fitar tai zamanta a d'aki. Koh abincin rana kin zuwa yai yaci a gidan sai gidan Garba yaje. Kawai zuciya ke raya mishi Salma ta fita,bazai so yaje gida yaga tabbas ta fitan ba,kawai sai yai zamanshi har yamma tukun ya koma gida. Dakin Bintu ya nufa har yanzu baida walwala sai ya tabbatar da Salma bata fita ba,yasan Bintu kat ce,bata t'sallaka doka akan fita,in yace A'a, toh ta hakura. Sannu da zuwa tai mishi tana fara'a, a ranshi yana aiyana da Salma ce yasan sai ta cika tai fa kan ta mishi sannu da zuwa duk akan ya hanata unguwa,amma kullum y'ar uwarta ko ajikinta. "Yau bayan fita ta Salma ta fita?.. Kai zata girgiza, sai tai saurin kwa6ar kanta, dole yadda tasa taga bakin ciki har yau itama ta gani. "Eh,bata jima da dawo wa ba ai,baka sani bane?.. Hannu ya daga mata,cike da jin haushi yace "ya isa ni,tambaya na miki kawai. Waje yayi tana binshi da g'walo, yana yin nisa ta tuntsire da dariyar mugunta. Kamin cikin sand'a tai waje jin ya zata kaya. Ba koh sallama ya shiga parlourn, ganan takalmin a gefen kofa wanda ta fitar zata sa dazu. Tana zaune tana _feeding_ din Miemie ya shigo yana binta da kallo,da fara'arta tai mishi sannu da zuwa. Kekam yayi yana k'allonta ba koh kiftawa, tabbas Salma ta fita,dan mud'in bata fita ba bazata tare shi da wannan fara'ar ba haka,yasan kayarshi. "Wato kin fita hankalinki ya kwanta koh?.. Ban isa ba ashe har yau halinki yana nan baki sauya ba koh Salma?.. Baki sake take K'allonshi da tsananin mamaki,sai d'aure ta yake da jijiyoyinta. Cikin nut'suwa tace "Ni fa ba inda naje tun fitar ka,dan Allah ka d'aina tun.. Malama ki amshi laifi kawai,kinsan nafi t'sanar musu sama da komai, koh kina nufin Bintu karya zata miki?. K'allon mamaki take mishi,a hankali ta maimaita "Bintu".. Yaki ma bari tai mishi bayani sai zazzaga mata yake kan bata maidashi abakin komai ba. Kawai sai ta sau mishi kuka,tama rasa abin fad'i,wai Bintu ce ta fad'a mishi,wato ita ba abin yarda bace sai kishiyarta indai kan fita ne. "Haka ki ke ai,da kukan rashin gaskiya Salma..sam bana son ki dawo mana da hannun agogo baya,ina ta murna komai ya wuce ashe albarkar ciki ne yasa ki zaman dole. Ganin kukanta na karuwa yasa ya fice ya koma d'akin Bintu. Har da bawa kura ajiyar nama,wai duk randa Salma ta fita dan Allah karta 6oye mishi. Tun daga ranar ya sauya mata,sam in ya shigo sai dai ya d'au ya'rshi ya fice,itama daga gaisuwa shikenan ta gama,dan a ganinta wulakanci ne wannan babba. Ga wani fi'ilin mutunci da Bintu ta koya da kissa,kullum faram faram take mata,harda gaisuwa in antashi. Ta d'au Miemie ta goya a bayanta in Baban ya d'akko ta. Ba karamin dad'i kwa Ja'afar din yake ji ba,dan yana karrama mai son Miemien shi,ita kam Salma nata ido,sai ta dukufa gun kai kukanta ga Allah. Dan tabbas tasan tai saken da har mijinta yai mata mummunan tambari. Bintu kuwa kullum rokon ta Allah duk wani sharrin da take nemanta dashi Allah ya mayar mata kanta. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [8/2, 2:29 AM] Feenat Ja'afar: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 30_Sai ya huce kamar sati ana mutunci da ta tambayi fita unguwa zai kicin-kicin,yace tai son ranta,haka zata hakura tanaji tana gani,in ya dawo kuma tasha fad'an da batasan laifi ba. Kawai Allah ya d'aura mata wani irin hakuri,daga Ja'afar din har Bintun ido tasa musu kawai. A haka har Miemie tai wata hudu Salma na zaman hakuri, musamman ga saurin fushin Ja'afar gareta,ga tai alkawarin daina kai kara gun kowa sai gurin Allah. Ana haka Maman Abba ta haihu. Ganin yau y'an mutuncin na kanshi yana zaune ya shagala da yiwa Miemie wasa tana wage mishi baki tana dariya. Da fara'arta ta zauna kusa dasu tana k'allonsu. "Abban Miemie... K'allota yayi tare fad'in yana jinta,cigaba yayi da wasan su. "Inda hali dan Allah zani barkar Maman Abba yau kwananta hud'u da haihu banje ba. Kai ya kad'a, "wace Maman Abba?.. Da zumudin zai batta ta sanarshi makociyarta ta unguwar su ta da. Abinda yake ya t'sagaita yana k'allonta ba koh kiftawa. Tuni ya zata an rufe babin y'an tsohowar unguwar su a gidan,ashe har yanzu tana makale dasu. Bazai manta dasu ba,dan sune ummul aba'isin wargaza gidanshi. Kai ya girgiza mata, "Kiyi hakuri ba halin zuwa.. Baki ta sake tana K'allonshi, a gaskiya bazata zuba ido tai ta zaman gida na y'anci ba,da takura gaskiya. Amma sai ta bishi da lallami. "Dan

Table of Contents

Chapters

41 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});