Chapter 10
Chapter 10
Tabbas shawarar nan tayi ta makamin rike miji, ta hakan kam ba yadda Ja'afar zaiyi ya raina ta... Toh amma Ja'afar yana sonta,batajin zai mata dabi'a irinta mazajen sauran Matan da ke fad'i. Nan ta jefar da dayawa a hudubar da taji a makota tai kitchen dan k'unna ritio. Sai d'ai Washegari ma da yamma Salma ta sake tambayar shiga makota. Karan nan kam kir ya fito yace mata a'a, da ido kawai take binshi, "Ya Ja'afar yafi zaman kad'aici ne,ba jimawa zanyi ba ka ji... Ta langwa6e kai. Ba dan yaso ba ya k'ada mata kai. Minti biyar bata kara ba tai makota,gidan chapter. Yau kam a sa'a taje,dan suna a kan firar rashin fitar matar gidan,sai bata dabaru suke akan yadda zatai mijn ya rika barinta fita. "Kar ki fara tambayar unguwa kina fara'a, sosai zaki dake mishi,mud'in yaga 6acin rai toh jiki na bari zai barki. Ni da farko haka Salisu ya t'siro min da k'ulle,tun farko nai ma tufkar hanci,da yace A'a yana fita zan arce, gashi yanzu har ya saduda yana barina duk inda na tambaya. T'sam Salma tai,tana tariyo maganar Ummi da Mama ta ranar,ga nan ta makotanta. Daga ganinsu sun san takan duniya. Tabbas ta yarda itace tun yana d'anye ake tank'wara shi. Tun yanzu ya dace ta takawa Ja'afar birki koh dan ta t'sira daga zargin wai tana tsoron shi. *Wasa farin Girki.* Daga ranar Salma ta tsiri dan hali,fita makota,tambayar fita gida,ga wani t'sarewa da take in tana tambayar. Kamar kullum tazo rakiya taja ta t'saya a gefe, "Ya Ja'afar... Jiyo wa yai shima rai ba dad'i,tare da zuba mata ido,yasan abu daya zata tambaya. "Zan leka gidan Maman Ummi gobe suna za ai k'ulli... K'allonta kawai yake, yadda tasha mur tamkar wanda take bashi umarni. "Anya Salma wani abu bai shiga kanta ba kuwa?.. Gaba daya ta sauya mishi hali k'wana biyu in dai akan fita ne.. G'wara tun wuri ya taka mata burki dan yaki jinin yawan fita sam shi. "Kiyi hakuri Salma,ki bari ki leka goben tunda suna ne... Tuni ta k'ank'ance ido, "gaskiya kar ka maidani saniyar ware a unguwa ya Ja'afar, yau k'ulli kowa ya je sai ni ce bazani ba?.. Ai sai a chake ni gobe dama suna fad'in ni dad'i miji... "Kuma ma ba wannan ba,nima sai ina zuwa za'a zo min in nawa yazo ai.... Shiru tai ganin yadda ya zuba mata ido yana kallo, chan ya nisa "amma Salma kin fuskanci kin fara sauya hali kuwa?... Kin koyi ja dani,kin koyi gantali k'arfi da yaji.. K'alloshi tai a wani iri, "au gantali ma nake Ya Ja'afar?.. Fisabilillahi wace fita ce nake yi ba dalili? A satin nan sau biyu koh uku ne fa na fita kuma dubiyar Ummi ne ba wani waje ba, koh shi ka ke nufi da gantalin? Kai ya k'ada,"kar mu rika ja in ja dake Salma,kiyi hakuri kawai gobe ki je... Juyawa yai ganin tana neman wata maganar yai waje, baki ta ta6e,kan tai cikin d'aki. Tana jin tashin machine d'inshi ta zaro hijabi ta k'ulle gida tai cikin gidan k'ulli. "Ai na zata bazaki zo ba,da har zanyi aike naga machine din maigidan. Hijab ta cire ta jawo jarka, "bari ke dai Maman Ummi,dak'yar na fito fa.. Murmushi tai kan ta d'akko wani abu a bakar leda,"yanzu saratu ta fita an kawo sabbin kaya dakakku wallahi,tai ta jira baki zo ba zata tafi na dau miki wannan... K'ar6a tai tana dubenshi kan ta kunce ledar,roba ce karama da wani abu mai d'anko. "Takalmin Kaza ake fad'a miki,nasan yafi haka,kawai ta mana sauki ne.. Amma abin ba magana,sai an g'wada akan san na k'warai... Dariya suka sa aka tafa harda shewa. "Wannan ne kawai makamin wulakancin D'a namiji,tunda kuka d'aurani kan _network_ nake son raina Allah. "Dari biyu ai ma yai araha... Bari yazo dari biyar zan tat'sa, dan asusu nake kan zuwa watan haihuwar Ummi na tara da yawa... Sai da aka gama k'ulli ana firar duniya,a debo gulma har aka gama,ana kiran magriba ta tuna Ja'afar, da sauri-sauri tai gida dan yau abinci ta zarce tayi. Kamar kullum ya dawo bayan magriba ana kiran isha'i, sai dai sam ranshi ba dad'i,nan tasha jinin jikinta,koh ya dawo bata gida ne? Har yaje masallaci akai isha'i bai dawo ba har ta gaji da jiranshi ta k'unna inji. Sai chan kusan tara ya shigo,har yanzu jiya iyau,sam kuma sai taji ba dad'i, tun kan ya fad'i lefin da tayi,amma de sai ta dake. Komai yayi,dan har abinci ya ci,sai dai fur yaki sakar mata. "Wai Ya Ja'afar mey nai ne ka ke ta shan kanshi?.. K'allonta yake da mamakin anya Salman shi ce wannan?.. Bai da amsa,sai a gunta kawai,saboda haka ya tashi yai hanyar d'aki. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:03 AM - Queen Safiyyert馃憫: *A BAKIN AURANKI* *漏 Feenat Ja'afar*. 16-Ya fito a band'aki ya ganta zaune a gad'o,kai ya dauke yana goge jiki da _towel_,d'uk sai jikinta yai sanyi,tabbas tasan Ja'afar kila zuciya yayi,har ya gama shirin bacci uffan bai ce mata ba,tuni ta fara kuluwa ganin ya ja filo bai bi takanta ba. "Wai mey in ma ina ta maka magana tun dazun?.. Kai ya dago ya k'alleta da tuhuma, "mey kika ce ban amsa miki ba?... Baki ta turo gaba kad'an, kai ya kada,tukun yace "Salma!... Salma!!.. Dagowa tai ta bashi hankalinta dan jin kiran da yawa. "Na'am.. Ido ya tsura mata,sai tai gefe da nata. "Ina kika fita dazu har magriba?.. Jin tambayar tai ta bazata,hakan yasa ta kasa K'allonshi, sai da ya maimaita tukun ta amsa a hankali da "gidan k'ulli... "Gidan k'ulli?.. Mey mukai dake toh kan na fita?... Duk t'siya ta ki jinin kuma taga ran Ja'afar ya 6aci, sai dai an rinjayi zuciyarta. "Kai hakuri... Itace Kalmar da ta fad'i. Tashi yai ya jingina da pillow,kan cikin nut'suwa ya fara mata magana. "Ba wannan ne ba karon farko da ki ke fita ba'a son raina ba Salma,nasha aiko yaro da sako yace gida a k'ulle yake,amma nai ta daga miki kafa. Duk gantalin da take bada yardar shi ba sai da ya sanarta,ga t'sinuwar mala'iku dake binta har ta dawo... "Sam wannan ba Salman da nasani a wata 5 d'in baya ba... Wannan cikin wata d'aya ta sauya,bata jin magana ta,duk abinda tasa kanta take ganin shine d'ai dai shi take... Sosai ya kasheta da kalamai,har ta fara hawayen wai bata jin magana. Murmushi yai kawai,kan ya dan taso ya janyo ta ya hau kuma lallashi,da alkawarin bazata kara ba,sosai ya ji dad'i,dan yana son mutum mai gane kuskure in ya yi. Washegari _week end_suna ma haka tai shiru,sai dai kasan ranta ji take kamar tai filfilwa taje gidan. Tasan iyanzu an kusa sauke abinci ana ta cin chapter ba ita. Sai dai tai ko'k'arin ganin bata tambaya ba. Shi kuma ganin haka yasa yaji dad'i,fatanshi yasa Salma ta g'yara ne. Ce mata yai yana zuwa,yana fita ta kasa zaune ta kasa t'saye. Anya bazata leka ba kan ya dawo?.. Dan tasan yanzu ana chan an kafa da ita uwar son miji. Sau biyu tana k'wata fita tana dawo wa,a na ukun taji dirin machine d'in Ja'afar ta koma. Sai gashi da leda baka a hannu. Sannu da zuwa ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41