Chapter 21
Chapter 21
zaki kafa dokar wa zai shiga ko ya fita?.. Cike da mamaki ke d'auke a fuskarta, ganin yadda ya rufe ido yake zazzaga mata bala'i harda yunkirin mari. "Ni zaka mara da akan waccan karyar Ya Ja'afar?.. A tuzare yace "eh wallahi, da da halin duka ma sai na miki,kuma daga yau kar in sake jin kin kamanta matata da sunan kare a gidan nan.. Kai ta k'ada, kan tai baya tana g'yara t'sayuwa tai d'aki. Code wear ta ciru, a masife ta fito tana mika mishi, "Amshi waya, yau in ka cika kaine Ja'afar ka dake a gidan nan sai nasan na ta6a maka y'ar g'wal dinka Ya Ja'afar, amma ni in naci sunan Salma,toh wallahi babu mai takani ya k'wana lafiya,zaman lafiyarta a gidan nan kawai ta fita harkata... "Bazata fita ba d'in, haba. Wannan wace irin masifa ce wai?.. Kullum ke kenan cikin dacin rai?.. Ba wanda yake t'sallake masifarki in ta motsa.. Haba Salma,yarinyar nan tun tana miki kawaici har sai kin kaita bango,koh tausayin yanayin da kike ciki ba k'ya yi?.. G'walo Bintun ta sakar mata tana a bayan Ja'afar. Kawai sai tai murmushi tai d'aki ta dakko hijabi da kud'i ta fito. Cikin sanyin murya tace "kamin izini zan fita Ya Ja'afar.. Harara ya sau mata!kan yace "Da in zaki fita ba kina gaban kanki ba?.. Wato ga shashasha yana magana dole ki fice,toh kije duk inda zaki ai kin saba... Dak'yar ta iya shanye kukan dake son subuce mata,ga Bintu sai dariya take mata a boye,da sauri ta zira hijab dinta tai waje. K'wafa yayi shima kamin yace Bintu ta shiga ciki yana zuwa. Waje yayi da sauri,har ta samu mai Napep ta shige tana hawaye, a tunzure yai gun mey Napep din, "Kar ka kuskura ka jata cikin Napep dinnan in kana son kekenka ya tsira.. Sauketa tun wuri.. A masife ta rufe ido tana mishi balbalin bala'i kan bazata sauka ba din. Shi dai mai Napep duk ya tsorata,jin ta dawo kanshi yasa ba shiri ya tada Napep,magana yake mata amma ina,da sauri ya juya shima yai gun nashi machine din yabi bayanta. "Hajiya wannan binmu yake a baya fa,wallahi kar ya tafkan asara.. Murya na rawa tace "Dan Allah ka kara gudu sabuwar gandu zaka kaini.. Kan ta karasa kukan har ya taho mata,kawai sai ta jingina kanta ta hau yi kamar ance mata Mama ta mutu. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 9:14 AM - Queen Safiyyert馃憫: *漏 Feenat Ja'afar*. 25_Yau amarya ta taro gidan Ja'afar,suna chan d'aki yan d'anna kirjin Salma. Tai kuka yau harta gode Allah,tukun daga baya taje ta d'au wanka. Tabbas ba'a iya dake wa kishi,koya sai ya tona ka,dak'yar ta samu ta saita kanta kamin y'an kawo amarya suzo kawo amana. Kowa ya wat'se, daga ita sai amarya, kowa tana dakinta. Karadin Garba ta kiyo a parlourn ta,tuni taji gabanta ya sara, tabbas tasan tare suke da ango. A hankali ta yaye labule tana k'allon su har suka shiga dakin amarya had'i da parlour mai k'allon nata. Zama tai ido tuni ya ciko da k'walla, sai tai ko'k'arin had'iye wa. Tana jin Garba yana bazai shiga ba yaje tai tanadin ta6aryar duka, tana suka sa dariya harda tafawa. Kwafa tayi,wato ga mahaukaciya sabon kamu. Tana jin rufe kofar gidan tai sauri ta k'wanta ta rufe ido. Da sallama ya shigo parlourn, ba kowa sai kamshin turaren uwar gida y'ar Borno jikar Shuwa. Ko'ina yaji sabon abu,kamar itace amaryar, labule da kujeru purple da baki, su Mama anga ba sarki sai Allah,kawai sai aka fito da tsohuwar ajiya,baba ya cika aka sai mata kayan parlour,ragowar nata na da suka siyar,gado k'wa tace bazata siyawa wani gardi ba,harda kukan Salma. Sai ma kuma gashi ashe yana da niya,gado barawan Italian da katifa yai mata a kud'in da Ummanshi ta turo mai daga Zaria. D'akin ya shiga,nan ma shiru ba amsa,tai rigingine kamar mai bacci. K'allonta ya t'saya yana yi kamin ya ajiye ledar hannunshi,sosai cikin ya kara fito mishi da k'yan Salma warai. Tai k'yau cikin attamfa ruwan purple da pink,tasha k'walliya sosai gun Ummi,idon nan yasha (mascara/eyeliner). Da komai Salman sa ta fi Bintu sau dubu agunshi,sai dai ta nuna mata hasken fata. Hannu ya kai kan cikin yana shafawa a hankali, tana jinshi yana yan surutanshi ma cikin. Ajiyar zuciya ta yi,sai ya k'allo ta,a tunaninshi baccinta ne yai nisa. A tashi yai yana k'allonta,kan a hankali ya duk'o tare da nufin kai bak'inshi nata,tana jin hucinshi sai ta juyar da kai da sauri. Murmushi yayi kamin ya shafo kanta da suka sha yiriyirin kitso. "Asbha ta ga Salma.. Ki yafeni kinji... Bargon kusa da kafarta yaja ya lilli6eta,kamin ya kashe wutar dakin yai waje. Ido ta bude tana nanata maganar shi a zuciyarta, mey yake nufi da ki yafeni?.. Saboda ya tafka miki t'siya mana.. Cewar wata zuciyar, le6e ta cije,yau gata a gidan Ya Ja'afar,akan gadon su,amma ba shi ciki,yau zasu fara raba matashin kafadar Ja'afar da wata chan.. Tana son Ja'afar, sai ma yanzu ta gano t'sant'sar son da take mishi,ji take kamar ta had'iyi zuciya ta mutu dan kishin mijinta, tuni tasau wani dan marayan kuka a hankali,kamar tace Ja'afar dawo. **** Ita k'wa amarya tuni ta mike ta fara zarya a d'aki, dan a idonta ya shiga bangaren Salma,tuni ta fara cika tana bat'sewa. Tana ko'k'arin fito wa a parlourn ya shigo,da sauri ta koma ciki har tana tuntu6e,duk ba tasan ya ganta ba. Ba laifi,tazo da tarikice dayawa,sam sai t'sarin na Salma yafi burgeshi,dan shi bai son tarkace a gida da sunan k'walliya,ga wani kala blue da pink na kayan labule da kujeru,sam bai mishi ba. "Ki fito da sallaya parlour.. Kawai sai yai waje dan yin alwala a band'aki. Assalatun farko ta farka,cike da mafarkin Ja'afar wai yana ta mata fara'a. Kasa tashi tai,tabbas da gaske yanzu tasan bakinshi kamar gonar audiga dan fara'a, tunda yai k'wanan d'akin amarya. Hakan ne yasa ko da gari ya waye taje kitchen ta d'aura abin kari,dan tun asuba taga text din Aunty A'i kan ta k'auda kishi tai musu kalacin da safe,dan Allah.. Wannan Kalmar ce tasa ta shiga dan dole. T'saye take tana juye abincin a flaks,ba abinda ta tsana irin hada kitchen da band'aki da kishiya,harar bangaren kayan jeren amarya tai tana gunguni ciki-ciki,bata nufa ba taji shafo wuyanta ta baya. A zabure ta juya dan ganin waye. Murmushi yake mata kanar dai a mafarkinta,da sauri ta d'auke kai daga K'allonshi zuwa gefe. "Kamshi duk ya karad'e gidan nan K'anwata.. Hannunta yake neman kamowa ta mat'sa tana "An tashi lafiya.. K'allonta yake daga sama har kasa,tana sanye da rigar banci _sky blue_ nai filawa purple, sai ta d'aura zani da dank'wali akai, tai mishi k'yau sosai,ga dan kurcicin cikin ya fito yai d'as. "Ya gajiyar jiya?.. Na shiga kinyi bacci ban son tashinki. Yawu ta had'iya tare da fad'in "ummm. Fur taki k'allon fuskarshi balle ta fassara mata bakin ciki. Dan da ganin yadda ya fara mata zagwadin nan ta faru ta kare. "Ga abincin ku,zan wuce.. Hannu yakai zai karbi natan tayi saurin janye wa ta wuce,kai ya k'ada bayan ya dawo daga k'allonta. Dakin amarya ya koma,tana kudindine cikin bargo, sai baccinta take narka abinta. Parlour ya dawo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41