Chapter 9
Chapter 9
ƙwan lantarki,na lumshe ido tare kuma da buɗe su. “Ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai saura ”shine abin da ta ce min. Da mamakin jin wai har dare yayi gari ya waye na ce “kina nufin yanzu safiya ce?” wani irin kallo ta yi min kafin kuma ta fita,na sauke ajiyar zuciya na tashi na shiga toilet sai a lokacin kuma na lura da an canza min kayan jikina zuwa na bacci. Cikin bahon wankan na shige,ina tunanin kaina a can ƙasan zuciyata sai dai fa na kasa tuna wace ce ni daga ina nake abu guda kawai ke cikin ƙwaƙwalwata shi ne aikina da kuma Zuly sai oganmu wanda nake jin mugun tsoronsa ya samu wuri a zuciyata ya zauna daram. Bayan na gama wankan sai na fito,da taimakon wasu turawan masu aikinta na kimtsa cikin wasu arnan kaya riga da wando waɗanda suka ɗame ni sosai suka fitar da shap ɗina.Tamkar wata ƴar tsanar roba haka na koma na yi kyau sosai,gashin kaina kuwa an dunƙule min shi tsakiya sai aka ƙara min da ribbob na gashin doki ta yadda ya sauka har gadon bayana. Zuly ta shigo ita ma cikin shiga mai kyau sai dai na fi ta haɗuwa kasancewar na fita kyawun fuska da na jiki.Jaka ta miƙa min da sabuwar waya irin ƙatuwar nan wacce ake aikin ofis,kafin ta ce “mu je” ta kamo hannuna,dakyar nake tafiya saboda yadda ban saba hawan takalmi masu tsini ba. Da muka fito harabar gidan nan na ga ikon Allah don kuwa ba gidan da muka zo ba ne ni da Zuly,wannan tamkar aljannar duniya haka yake.Hatta motocin da ke wurin sun sha banban da waɗancan,cike da girmamawa aka buɗe mana gidan baya muka shiga abun mamaki har da masu take mana baya.Sai da muka hau babban titi ne sannan na gane nan ɗin fa Turai ce ba Afirka ba,wani kamfani ne muka je tun a bakin ƙofa Zuly ta tsaya kafin ta ce “ki nutsu ki aiwatar da aikinki kar ki wani damu jin cewa ke ce baƙar fata a cikinsu” kai na jinjina mata kafin Bodyguard biyu su take min baya har zuwa ɗakin da za a yi meeting ɗin. Direct kujerar da ke ɗauke da sunana na je na zauna,suna ne wanda ba wanda uba mahaifina ya saka min ba a'a Oga ne ya canza min shi ba tare da na san ta ya aka yi kuma na gane nawa ne ba.Leena shine sunan da ke jikin ɗan ƙaramin allon gabana,sai da na yi gyaran murya sannan na danna wayar hannuna wacce ke ɗauke da dukkan bayanan da za mu tattauna a kai. “Sunana Leena daga ƙasar Kamaru,wakiliyar kamfanin El Mansoor a yau mun kawo muku wata babbar haja wacce muke fatan za ku ji daɗinta sosai fiye da sauran business namu na baya” ina kawowa nan sai na yi shuru ina yi musu murmushi su kuma duk fuskokinsu sun nuna zaƙuwar jin abin da zan ce ɗin. Na ci gaba da cewa “a ƙididdiga ta malamanmu na spirituality sun gano cewa dayawan mutane a yayin yin bahaya mutum na zubar da kaso hamsin cikin na abin da ya shafi taurarinsa marar kyawu,yayin da kuma zubar da yawu a lokacin da mutum ke tsugunne kan salanga yake ɗauke ɗigo biyu na sinadarin tauraronsa mai haske.In muka haɗa hamsin da biyu sun tashi ɗari cicif.Na san dayawanku za su tambaya ta ya aka yi aka samu ɗari? To amsar mai sauƙi ce duk tauraro mai haske ɗaya yana daidai da kaso hamsin na baƙin tauraro,da za a saka su a injin markaɗe a garwaya su to tasirin farin tauraro ne zai ƙwace kaso mafi rinjaye.Kun ga shi kenan mun samu tauro ɗari kenan” duk shiru suka yi suna nazari amma babu wanda ya iya cankar ainahin gamsashiyar amsar kawai sai suka fara yi min tambayoyin yadda za su yi su zuba hannun jarin wanda dama ni shi nake jira.Sai na soma yi musu bayani dalla-dalla “iya adadin kuɗin da mutum ya zuba iya adadin taurarin da zai samu,kenan kowa sai ya aiko min da saƙon abin da ya yanke ta adreshing email namu” Ina kawowa nan sai Zuly ta shigo ita da wasu masu aiki su biyu suna ɗauke da tray,amma ita Zulyn ce ta ajiyewa kowa kofin shayi a gabansa tana ajiye min na ɗauka na soma kurɓa ina kallon yadda suke shawara a tsakaninsu. Ba a kuma ɗauki lokaci ba kowa ya soma faɗin abin da zai zuba na hannun jari,bayan nan duk sai aka watse aka bar ni daga ni sai Zuly wacce ta danna wa oga video call tana murmushi tare da yi masa congratulations akan aikin da na yi nasara ba tare ni na san muhimmancin meeting ɗin ba ko kuma ina jawaban da na kawo suka dosa ba. Yadda suke murna yasa ni ma na ji sanyi a raina,ina jin oga na cewa “ku tawo gida mu yi shagalin murnar a nan” Yanayin fuskar Zuly ya ɗan canza ina ganin lokacin da ta saci kallona ta wutsiyar ido kafin ta ce “oga kana ganin lokaci yayi da Luby za ta ga zahiriya da idonta?” “Eh mana! Ai ba zama za mu yi muna kashe kuɗi wurin controling memorynta ba kawai ku dawo yanzu,sai ku same ni a can filin hutawana ” Da ƴar damuwa a fuskarta ta ce “oga ko dai ka tarbe mu a can ɗin,don ina gudun Luby ta yi min tirjiya ko borin hauka” “Ki yi yadda na ce” yana gama faɗa ya kashe,sai a lokacin ne ni kuma na jefo mata tambayar da ta ɗaure min kai “Zuly wace ƙasa ce nan? Ta ya aka yi muka zo nan?” “Ki taso mu je,yanzu kin samu amsar tambayarki in mun koma Kamaru” ta faɗa tare da nufar ƙofa,sai na take mata baya ina mai ci gaba da yi mata wata tambayar “amma ina ne nan?” ba ta bani amsa ba har muka shiga mota muka isa gida. Da umarninta kuma na bi bayanta zuwa wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa sai wani madubi da aka rufe da jan ƙyalle.A gabana ta buɗe shi tare da ɗaukar wuƙa ta tsaga yatsanta jini ya soma ɗiga sai ta shafi madubin nan take yayi ƙara ƙiiiii tare da buɗewa ya fitar da hoton ƙofa amma fa ba ƙofar ba ce don ba ka ganin komai sai wani farin abu kamar gajimare. Jikina ya ɗauki rawa na ce “ina ne nan kuma Zulaihat?” na yi tambayar ne jin tamkar tunanina ya dawo normal,iya ni ɗaya kawai ke sarrafa shi. “Ba mu da saurin lokaci Lubna ki zo mu tafi” ta faɗa tana kamo hannuna da niyyar shigar da mu cikin madubin,a tsorace na ce “mu je ina? Wai cikin madubin? Zulaihat wannan ai tsafi ne.Ina kika kawo ni? ” ba ta bani amsa ba ta wani fizgo ni muka ratsa mirror ɗin sai gamu muna yawo cikin wani iska kafin kuma ƙyaftawar ido na gan ni a cikin ɗakin Zulaihat a cikin falo.Tuni zaren carbin tunanina ya tsinke,dukkan jikina rawa yake yi min ina son yi mata tambayoyi amma ina tsoron jin amsoshinsu don ban so a ce abin da nake zargi gaskiya ne. Ita kuwa Zulaihat sai ta yi fuska
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38