Chapter 22
Chapter 22
kamar yadda na fi ƙaunar kallon horror film. ★A can ɓangaren Uncle Salem kuwa Nafisa na fita da gudu yayi saurin tattare littafansa kafin ya gyara zaman hiramin kansa ya fito.Direct ƙofar da za ta sada ka da babban falon ya nufa bakinsa ɗauke da sallama,tsit duk falon ya ɗauka kafin duk su yi ƙasa da idanunsu saboda yadda yake da matuƙar muhimmancin da kuma girma a idonsu.Cike da girmamawa suka soma gaishe shi “ Barka da fitowa Daddy ƙarami“ domin haka suke kiransa in ka fidda Nafisa da take ce masa Uncle ita ma ɗin shine da kansa ya koyar mata da hakan. “Fatan dai ba ƙara ta ba aka kai wurinka,a toh don na san ba kasafai za a gan ka a nan ba” cewar Daddy yana ɗan murmushi yana kallon babban abokinsa,amininsa kuma ɗan uwansa.Uncle Salem ya ce “tun da ma ka sani ai shi kenan sai a fara shirya mata abubuwan da za ta buƙata in ta je can” Daddy ya ɗan nisa yana kallon yaran wurin duk sai suka tashi suka kama gabansu,sai a lokacin kuma Uncle Salem ya zauna suna fuskantar juna. Duk shuru suka yi na wani ɗan lokaci kafin Daddy ya ce “ ba wai yadda kake tunani ba ne aboki,ina da dalili na daban da yasa ban so Nafisa ta yi nisa da gida” Uncle Salem ya murmusa ya ce “tun muna makaranta ake faɗar wannan kalmar akan kana da dalilin ƙin yin wani abu amma har yanzu ba ka taɓa faɗa min mene ne dalilin ba.Abdul Hameed ka sani cewa su yara da kake gani sun fi son bin zaɓinsu kan na iyayensu,kuma kai ma in ba ka manta ba...” sai kuma yayi shuru. Yanayin fuskar Daddy ta ɗan sauya kafin ya ce “babu damuwa zan bari ta je ɗin, Allah ya bada sa'a ya kuma tsare ta akan abin da nake tsoron faruwar” da “amen“ kawai Uncle Salem ya amsa kafin ya miƙe tsammm ya nufi ɗakin Nafisa,ya tura ƙofa tare da yin sallama sai kuma yayi tsaye cak yana buɗe ƙofofin hancinsa saboda kalar wani ƙamshi da ya dake shi da bai taɓa jin irinsa a wannan duniyar ba.... [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 02 Tsaye yayi yana kallon yadda take bacci tana wani taɓe baki kamar mai kuka yayin da goshinta ke fitar da gumi.Ya furzar da wani huci kafin ya ƙarasa ya zauna bakin bed ɗin,a hankali ya cire mata hijabin nata wanda ya ɗan jiƙe saboda zufa.Sumar kanta wacce take baƙar ƙirin ya soma shafawa yana tofe ta da addu'a,a hankali ta soma sauke ajiyar zuciya tana wani motsa idonta kamar mai son buɗe su. Kamar wanda ke wasa da maciji haka ya soma shafa farar fatar fuskarta wacce ta yi ɗan ja saboda kukan da ta yi.Wata irin azababiyar ƙaunarta ce yake jin tana bijiro masa,ji yake tamkar ya ɗauke ta ya haɗiye tsabar so. Sam bai san abokin nasa ya shigo ba don ya lula sosai a duniyar tunanin muradun ruhinsa,sai jin saukar muryarsa yayi “ sai yaushe ne za ka sanar da ita ɓoyayyen sirrin da ka binne abinka?” Uncle Salem yayi saurin ɗagowa ya dubi Daddy ya saki ɗan murmushin da ya zame masa jiki kafin ya ce “ har yanzu Naf yarinya ce aboki,zan ƙara mata lokaci ” sai kuma ya mayar da duban nasa ga fuskarta a iya kallon da yake jifar ta da shi ya isa ya fallasa ma sirrin da ƙunshe a zuciyarsa. “ Shekarunta ashirin har da biyu fa,lokaci na ƙurewa girma na sake zuwar ma amma har yanzu ba ka ajiye iyali ba aboki” Daddy ya faɗa cikin rashin jin daɗi. “ Shi aure ai ba sauri yake so ba,a'a fahimtar juna aboki.Ka yi tunanin yadda Naf za ta ɗauki lamarin ne in ta ji cewa ni mijinta ne alhalin a uba ta ɗauke ni?” Daddy yayi murmushi kafin ya ce “ to ai kun fi kusa,ban iya na sani” Uncle Salem na shirin yin magana aka shigo haɗi da sallama,Ammy ce hannunta riƙe da kofin ruwa.A mutumce ta gaishe da Uncle Salem wanda a girme ya girme mata sannan ta dubi mijinta hasken idaniyarta ta ce “ ga maganinta yau ba ta sha ba sam” ya karɓa ita kuma sai ta fita. Kan dakalin gado Daddy ya ajiye maganin yana mai kallon Nafisar wacce har zuwa yanzu take baccinta yayin da kuma hannun Uncle ɗinta ke kan sumarta. “ Aboki me kake ɓoye min dangane da Naf?” yayi tambayar cike da kulawa. A ɗan rikice Daddy ya ce “ no babu komai zan je na duba wasu takardu in ta tashi ka bata maganin” yana gama faɗa ya fice,shi kuwa Uncle Salem kai ya girgiza tun suna yara suke tare amma har izuwa yanzu bai san dalilin da yasa abokin nasa ke ɓoye masa wani babban sirri da ke ɗawainiya da rayuwarsa.Tun da Nafisa ta soma tasowa yake lura da yadda hankalinsa kocokwam ke kanta hatta makaranta in ta je ya dinga kiran waya kenan yana tambayar labarinta,yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuma ya basa aurenta tun ba ta san kanta ba amma har yau ya ƙi sanar da shi mene ne sirrin. Ganin kamar baccin nata irin wancan ne da ta saba yi ,sai Uncle Salem ya ɗauki kofin maganin ya cika bakinsa da shi kafin ya taɓe bakinta yana ɗura mata shi kamar yadda tantabaru ke ciyar da junansu,a hankali kuma take haɗiye ruwan maganin da shi ne ya haɗa mata shi a haka har ta shanye shi tasss.Da ya kai ƙarshe sai da ya ɗan lashe mata lips kafin ya miƙe ya fita,sashensa ya nufa ya rage kayan jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa turare kawai sai ya ɗauki system ɗinsa ya soma aiki yana duba saƙonnin sojawan da shine ya tura su mission a daji.Reppot ne iri-iri wasu na murna wasu na jimame,tuni kansa ya soma yin hayaƙi yana jin cewa da buƙatar ya je can ɗin da bada wata sabuwar atisaye. ★ NAFISA Ban san iya lokacin da na ɗauka ina bacci ba,ko da na tashi da ƙamshin turaren Uncle Salem na soma cin karo wanda ya game ko ina na ɗakin.Na turo baki gaba kafin na dubi hijabina wanda na san da shi ne ya cire min shi ko shakka babu.Wanka na shiga,bayan na fito na yi sallar azahar don sallah na ɗaya daga cikin abin da na fi so a kaf cikin abubuwan ibada ita da azumi wannan kuma horarwa Uncle Salem ce tun ina ƴar shekara sha uku yake saka ni yin azumin Litinin da Alhamis,tun ina kukan yunwa har na kai na saba. Ina zaune kan dadduma Ammy ta shigo,“yawwa kin sha maganin ashe ” shi ne abin da ta fara cewa. Shiru na yi ina tunanin yaushe na sha magani amma ban tuna ba,amma tabbas da na tashi na ji bakina na zaƙin zuma.Na sake turo baki don kuwa tuni kwanyata ta hasaso min ina baccin ya bani magani. “ Ammy ni yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,“ Sai ki je ki ci mana,ki taso ki kaiwa Daddy ƙarami
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38