Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 4

Chapter 4

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,240 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

taɓa jin haushinsa sosai kamar irin na yau ba,kamar wasu kurame haka muka ci gaba da tafiya har muka isa gidansu Lubna. A tsakar gida muka tarar da Ummah tana gyara wake,bayan mun gaishe ta sai muka shiga daga ciki.Kan katifar da ke shimfiɗe na yi wa kaina masauki na kwanta tare da yin lamo,maganganu Lubna ta kai wa junansu karo a cikin kwanyata. “Bari na yi wanka,kin ga kunun tsamiya nan ki zuba ki sha” ta faɗa kafin ta fice,sai dai a yadda ta bar ni haka ta same ni.Cike da mamaki take cewa “wai ba ki sha kunun ba?” Na ɗan yamutsa fuska na ce “ban ra'ayi ne” Ta taɓe baki kafin ta ce “ke ma ai jujun ce kamar Maheer ba a gane kanki wani sa'in ni dai ci gaba da bani labarin naki ” Na ja ajiyar zuciya kafin na ce “zan baki har mu koma can gidan Hajiya ” “Ni dai ki fara bani yanzu” Na ce “a daren ranar muka faki idon Goggo Lami muka je ni da Hassana muka binciko kayan Husseina waɗanda suke ajiye ko tsinke ba a taɓa ba.Kayan da ta mutu da su wata doguwar rigar atamfa ce,tana mugun sonta wanda kusan tana yawan saka su wannan yasa har zuwa lokacin ba mu manta ta ba.A nan cikin ɗakinsu Hassana na saka rigar sannan na hauda tawa a sama,sai na mayar da hijabina.Waje muka fita kamar babu komai muka zauna cikin ƴan uwanmu muka ci abinci kafin duk a watse saboda yau babu wata hira mai daɗi da za mu yi in banda ta jajen mutuwar Haidar . Ko da na je ɗakinmu sam ban cire hijabi ba da shi na kwanta,babu jimawa kuwa bacci ya ɗauke ni.A cikin baccin na ji ana buga ƙofa tare da kiran sunana,na buɗe ido sai na yi tozali da Husseina sanye cikin kayan matattu wato likafani.Idonta na zubar da hawayen jini take kallona,kafin ta ɓace ba tare da ta ce min komai ba...” Lubna ta yi saurin katse ni “wai a zahiri kika gan ta?” Na ɗan harare ta na ce “ke fa ba ki iya cin ƙwan makauniya ba,ki bari na baki labarin mana” “To na bari” ta faɗa tana gyara zama. Ni kuma na ci gaba da cewa “daidai nan na farka daga bacci sai na fahimci mafarkinta ne na yi,wanda kuma hakan ba ta taɓa faruwa da ni ba in ba yau da na saka kayanta ba.A lokacin wani irin tsoro ne ya kama ni sai na kasa yin bacci,don da zarar na rufe ido Husseina nake gani tsaye kusan ƙafafuna da fararen kayanta .Ƙwan lantarki na kunna saboda tsoro,ɗakin ya kawo haske sai na ga Innarmu zaune a tsakiyar gado ta yi tagumi da dukkan hannuwanta yayin da kuma hawaye ke yi mata shatata kamar an kunna pampo.Na matsa kusa da ita na ce “Innarmu kuka kike? Ki yi haƙuri don Allah ki bar kuka in kina yi hankalina tashi yake” ban san me ya ja ra'ayin Innarmu a wannan lokacin kawai dai na ji ta jawo ni tare da rungume ni tana mai cewa “Haule ina son nesanta ki daga gidan nan amma banda ƙarfi ko izzar yin haka,na sani ke ce ta gaba” “Ta gaba kamar yaya? Innarmu wai mene ne kike son faɗa min?” na tambaye ta duk da a lokacin ba zan wuce shekara goma sha biyu ba amma na fahimci kamar da akwai wani sirri da Innarmu ke ɓoye min” ina kawowa nan sai na yi shuru ina goge ƙwallar da ke yi min zuba saboda wata irin kewar mahaifiyata da ta tsirga min,na miƙe na ce “zan tafi sai kin iso” “Jira na saka kaya mu koma tare” ta faɗa ita ma duk idonta sun yi ja,bayan ta kimtsa muka yi wa Ummah sallama muka dawo gidan Hajiya sai kuma muka tarar da wani sabon tashin hankali Maheer ne a kwance duk ya sandare kamar gawa ga kuma likita biyu kai gare shi.Ni da Lubna muka kalli juna don kuwa tuni muka san mene ne matsalar,da kuma maganin da zai warkar da shi..... [07/03 17:32] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 03 Daga inda nake tsaye muke ƴar kallon-kallon ni da Maheer,kallo ne yake yi min wanda ke nuni da cewa eh ya san komai a kaina.A yadda yake juya idonsa tuni na fahimci abin da ke zuciyarsa,magana yake yi min ta ido wacce kuma sarai nake jin abin da yake cewa tamkar da bakinsa ne yake magana. “Ki zo ki cire min ƙwayar kambun maitarki da kika jefa min ,in kuma mutuwata ce farin cikinki shi kenan sai ki ci gaba da riƙon inuwata da kika damƙe” Ido na lumshe bayan na gama sauraran abin da ke fito wa daga idonsa,maimakon na basa amsa ko yi masa zancen abin da ya shafi maganin cutarsa sai tambaya da na jefo masa ni ma ta ido kamar yadda yayi min ,“wane ne kai ? ” ƙin bani amsa yayi sai ya juyar da kansa gefe. “Kar dai ki ce min zargina gaskiya ne ke ce kika jefa shi cikin wannan halin?” Lubna ta tambaye ni tana mai matso bakinta kusan kunnena.“Ki ɗauko kofin ruwa ki same ni a ɗaki” shi ne abin da na ce mata kafin na yi gaba abina,babu jimawa kuwa ta shigo kofin hannunta na karɓa na yi ta kallon ruwan na ƴan sakanni kafin na tofa yawuna a ciki suka fara tafasa suna canza kala a sannu-sannu,sai kuma na ƙara tofa wasu sannan na miƙa mata kofin ta fita. Na ja wata ajiyar zuciya ina jin duk babu daɗi yadda ya wahala domin ni,duk da cewa ni kaina ban son hakan nake yi ba na cutar da mutanen da suka ɓata min rai. Na saki ɗan murmushi a fili na ce “ko wane ne shi? Ta ya aka yi yake magana da ido?” ban kai ga samo amsa ba Lubna ta shigo tana yi min wani kallo kafin ta ce “sai ki je suna son yin magana da ke” Na ce “su wa?” “Likitocin da suka kasa yi masa magani mana,a gabansu na basa ruwan ya sha ya kuma tashi daram ya zauna kan ƙafafunsa shine suke son sanin sunan itaciyar maganin da kika yi amfani da ita” Banda kallonta babu abin da nake yi,kafin ma na ce wani abu Hajiya ta shigo ɗakin tana washe baki tare da kamo hannuna ta ce “zo mu je yarinya kin zama cele ai ,manyan likitoci sun kasa maganin cutar Maheer amma maganinki na gargajiya ya warkar da shi garas.Kar ki so ki ga yadda na fita a guje neman taxi ni na manta ma da akwai mota a gidan,ina dawowa kuma aka ce ke ce kika basa maganin” tana maganar ne tana jan hannuna har muka iso falon. Wani irin faɗuwa gabana yake yi,ga manyan likitocin da duniya ta san da su don har a tv ana nuno su.Duk sun gyara zama suna jiran amsa daga gare ni,shi kuma gogan ya wani haɗe rai kamar ba shi ne

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});