Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,242 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kwanta gefena bayan kuma Innarmu ta ce ta kashe ƙwan lantarki.Duhu na game ɗakin na buɗe idona,tunanin na shiga yi iri-iri yadda ake yawan yin mutuwa gidanmu kusan kuma duk date iri ɗaya ne.Na jima sosai cikin wannan tunanin,don gari yayi tsit kafin kuma na soma jin motsi a can babban falon ahali.Kamar munafuka haka na miƙe na fita,amma ban fita zuwa ƙaramin falo sai na laɓe,iyayenmu maza na gani kaf illahirinsu suna magana akan zancen da ban san ina ya dosa ba. “Ibrahim yanzu ta ɓangarenka ya kamata mu fitar da alƙawari” Kawu Hamza ya faɗa wanda shi ne babba kaf cikinsu. Kawu Laminu ya karɓe da cewa “hakan shi ne daidai,kuma dai kyautar namiji don ni ai mace na bayar wancan lokacin ” wato mahaifin Hassana . Ibrahim wanda ya kasance mahaifina yanayin fuskarsa ce ta ɗan canza kafin ya ce “zan yi shawara” sai kuma suka miƙe suka shiga wani ɗaki ƙwaya ɗaya tal wanda tun da na yi wayo ban taɓa ganin an buɗe shi ba sai yanzu. Ba tare da na san mene ne meeting ɗin nasu ya ƙumsa ba sai na koma kan shimfiɗata na kwanta.Ina shirin rufe ido haske ya game ɗakin nan muka haɗa ido da Innarmu,“daga ina kike?” ta jefo min tambayar da kafin na bata amsa Haidar ya fashe da wani masifafen kuka wanda yasa Innarmu nufarsa da sauri. Haidar ƙaramin yaro ne duka ba a yi wata biyu da yaye shi ba,ruwa Innarmu ta basa amma yadda take ɗura masa su to kamar haka ya maido su ta baki da hanci kafin kuma daga ƙarshe jini ya zubo masa ta hanci shi kenan bai ƙara motsi ba” ina kawowa nan na miƙe na bar Lubna zaune sake da baki da hanci. “Haule ina kuma za ki je?” ta tambaye ni,ba tare da na juyo ba na ce “zan wanke kwanuka kafin Hajiya ta dawo”. Wurin da aka tanada don yin wanke-wanke na nufa na soma wanke plate ɗin da customa suka ci abinci.Ina tsaka da yi Lubna ta zo tana yi min ɗauraya,mun yi kamar minti biyar muna aikin kafin ta ce “fatan dai ba mutuwa Haidar ɗin yayi ba?” Na san halin Lubna da mugun son jin labari,in ba ta gamsu ba to ƙila har gida tana iya bina don ta ji ƙarashe hakan yasa na ɗora daga inda na tsaya. “Ina tsaye a gaban idona Innarmu ta soma yin hawaye tare da furici guda “don me sai Haidar?” wannan kalmar ta daɗe tana yi min yawo cikin kwanya don nemo ma'anarta amma tsawon lokaci ban samu ba.Na durƙushe kan gwiwaina tare da tambayarta “Innarmu me ya samu Haidar ɗin?” “Ya mutu Haule! Haidar ya mutu!” ta bani amsa tana ƙanƙame gawar Haidar,ban san lokacin da na yi kururuwa ba wacce kusan ita ta tashi kowa na gidan ciki kuwa har da anty Aliya. Kan ki ce wani abu ɗakinmu ya cika da mutane,ana ta kuka goggo Lami ce ta je ta rungume Innarmu tana bata haƙuri.Yayin da Hassana ta yi tsaye kusa da ni ta ce “duba ki ga irin yadda Husseina ta yi ne yayin mutuwarta” cak hawayen da suke yi min zuba suka ɗauke,yayin da idona ya soma tariyo min gawar Husseina wacce har bayan an yi mata wanka jinin da ya fita ta hancinta yana nan bai goge na sai ma ƙari da aka samu wanda kafin safe har da idonta suke shatatar da kukan jini.Ban iya cewa Hassana komai ba a wannan lokacin sai dai mun ci gaba da kukan mutuwar Haidar,wanda har asubah babu uba namiji ko ɗaya da ya leƙo ɗakinmu sai da gari yayi haske shi ma ɗin karɓar gawar suka zo. Bayan an yi wa Haidar wanka aka bai wa Innarmu damar yi masa ganin ƙarshe,haka don ƙwaƙuwa na mara mata baya har sai da ta buɗe likafanin nan na yi arba da idonsa su ma suna shatatar da jini.Kuka ne ya kubcewa Innarmu,kawai aka rufe gawar tare da fita shi nan gidan namu ya ƙara kancamewa da koke-koke ganin an fita da shi. Ana cikin zaman makoki ne Hassana ta zo ta ja ni gefe,na ce “ke lafiya?” Sai da ta waiwaiga sannan ta ce “jiya bayan mun kwanta na yi mafarkin Husseina ta ce na baki kayanta waɗannan wanda ta mutu da su ki saka a jikinki” “Saboda me?” na tambaye ta ,ta ce “ke dai don Allah ki saka” nan na yi da ita zan saka ɗin kamar yadda ta buƙata” sai kuma na sake yin shuru na kalli Lubna wacce ta tsaya cak da yin aikin,na sakar mata murmushi na ce “ya dai kin tsorata ne? Ai ba ki ji komai ba nan duk shimfiɗa ce ke dai ki yi haƙuri da sannu duk za ki ji dukkan labarina” Lubna ta ce “ai duk jikina yayi sanyi duk da dai ni ma da nawa labarin mai matuƙar firgici ” Masifar Hajiya ce ta katse hirar tamu,da sauri na fita ina bata haƙuri ita kuwa kamar ƙara zuga ta nake sai ƙaimi take ƙarawa wurin faɗan. “In ba ku canza ba wallahi sai duk na kore ku na kawo sabbin ma'aikata,dubi yadda har yanzu ba ku goge table ba”. “Yi haƙuri Hajiya amma don Allah kar ki kore ni ba ni da kowa” na faɗa murya na ɗan rawa ,amma da yake Hajiya ƙarshe ce wurin rashin mutumci sai ta tsiro da wani zancen “yau ba za ki ci abincina ba sai da ki saya da kuɗinki,saboda kin ga ina tausayinki ne kike yi min iya shege” tana gama faɗar haka ta yi ƙuuu ta fice,ni kuma na yi baya na zauna kan kujera saboda kaina da ke mugun sara min..... [07/03 15:42] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 02 In akwai abin da ya fi ɗaga min hankali shine zancen kora ta da Hajiya ta ce tana iya yi,wanda kuma ya ɓata min rai shi ne yadda a kullum take wulaƙanta ni kawai don ina ƙarƙashinta. Lubna ta fito wacce ita tun tuni ta gama aikinta,dama ita iya girki ne take yi.Ni kuma tarben baƙi da kawo musu abin da suka buƙata,sai kuma wanke kwanuka da share restaurant ɗin. “Ki je ki yi wanke-wanken ni sai na goge wurin” ta faɗa cikin sanyin murya,ban ce mata komai ba na miƙe dakyar na je na ida aikin nawa.Sannan na dawo nan muka ƙarasa gugar,bayan mun gama na rufe ko ina kafin mu kama hanyar gidan Hajiya .Da ɗan nisa wannan yasa sai da muka yi sauri kafin mu isa,a falo muka tarar da ita ta ƙure ƙarshen ac amma duk da haka sai gumi take fitarwa. Kallo ɗaya na yi mata na ɗauke kai,saɓanin Lubna da ta je tana cewa “hajiya ko jikin ne ya motsa?” Cikin murya wacce kana ji ka san babu lafiya ta ce “olser ce ta yi min wuf sai ɗan kanoma,ki bani maganin nan na sha wanda kike bani” Lubna ta ɗan dube ni kafin ta ce “ai Haule ce ke da shi dama ba ni ba”

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});