Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,242 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bai da wata illa ya fi ki yi da wanda ba ki so” “Ba ki da hankali,sai na je na yi zina? Allah ya tsare ni” na faɗa tare da miƙewa,ina shirin fita wani abun al'ajabi kiran Dr David ya shigo wayata cak na tsaya kafin na juyo na ce “shi ne ke kirana ” sai ta saki murmushi ta ce “ki ɗauka mana” Kiran na ɗaga,bayan mun gaisa ya tambaye ni yana son mu yi magana amma don Allah ba ta waya ba mu haɗu ko da wani restaurant ne.A ranar nan rabon na rabu da alaƙaƙai ne yasa na yarda da gayyatar Dr David,wani abun mamaki kuma shine a restaurant ɗin Hajiya ne muka haɗu a nan ne na fara ganinki Haule haka kawai na ji kin yi min sai kuma na ga kina yawan kallona a duk lokacin da za ki kai abinci a wani teburin da aka buƙata.A tattare da ke na ga wasu abubuwan na daban sai dai ban san ya zan yi na yi miki magana ba,a nan ne kuma hankalina ya rabu biyu na yadda zan yi na samo sperm ɗin Dr David da kuma na mamakin yadda kike yin abu kamar siddabaru. Dakyar na iya tattaro jarumtar tunkarar Dr David kan cewa ina son sperme ɗinsa saboda an ce yana gyara fuska,bai wani musa min ba don dama ya kira ni izuwa nan ne don bani haƙuri da kuma neman alfarmar mu koma soyayya.Mun yi da shi zai kawo min sperm ɗin zuwa dare,da wannan muka rabu ya sauke ni gida.Duk yadda muka yi da shi na kwashe na shaidawa Zuly ta yi murna sosai har ta kasa ɓoye farin cikinta,sai kuma na yi mamakin haka amma na ɓoye shi har lokacin da Dr David ya zo ya kawo min abin da na buƙata cikin wata ƴar kwalba. Bayan na karɓa ya jefo min wata tambayar da ta hautsana hanjin cikina,“Lubna kin tabbata a fuskarki za ki shafa shi?” duk da a lokacin na firgita amma haka na mayar da abin tsokana na ce a'a cikin mahaifata zan ɗura shi don na samo baby mai kama da kai,nan yayi dariya muka taɓa ƴar hira kafin ya tafi. Yana gusawa motar Zuly ta parker na shiga muka lula can gidanta,cike da zumuɗi take cewa “meeting ɗinki na Japan an ɗaga shi,yau za mu je ɗakin sirrin Boss domin gabatar da sacrifice ɗinki na farko” sam ban fahimci abin da take cewa ba,sannan kuma ban tambaya ba. Yau ma ta cikin madubinta muka bi muka isa a ɗakin taron,abun mamaki kowa ya haɗu har da shi kansa Boss ɗin wanda idonsa ke jifana da kallon sha'awa.Ba a ɓata lokaci ba muka dugunzuma wani ɗaki mai shegen duhu ,babu abu mai haske ko ɗaya in kuka cire wani mirror . Cikin wata irin busashiyar murya Boss ya kira sunana,hakan yasa na ɗan matsa ba tare da na amsa ba.Hannu ya miƙo min,na san za ku ce ta yaya na ga haka duk da na ce akwai duhu a ɗakin.To abin shine da zarar mutum ya kai wani lavel yana samun wani ido a tsakiyar goshinsa mai gane masa komai da ido normal ba zai gani ba. Yana karɓar robar sperm ɗin ya buɗe ta,sannan ya dangwalo da yatsansa ya shiga yin rubutu a jikin madubin *BAƘIN RUHI* shi ne abin da ya rubuta nan take wata irin guguwa da iska mai ƙarfi suka cika ɗakin na yi tunanin duk za su yi murna sai dai fa akasin haka ne ya faru saboda kururuwa da suka soma,kafin ƙyaftawar ido wani jan maciji ya bayyana a mirror ɗin yana feshin wuta kafin kuma madubin ya tarwatse wanda turnuƙin fashewarsa ta haifar min da gushewar hankali ko da na farka a kwance na same ni kan shimfiɗa Ummah na yi min fifita.Ina ware idona sosai nan na yi arba da Alhaji wato Maheer,wani irin mugun kallo ne yake watso min yana hararena. Ummah ta ce “kin farka Lubna?” ban amsa ba sai dai na yunƙura zan tashi sai dai na kasa saboda yadda jikina ke yi min mugun ciwo. “Ki kwanta ki huta” cewar Ummah. Shi kuwa cike da mugunta ya ce “barta za ta iya tashi,ke miƙe ” Maganarsa tamkar umarni ne a gare ni,haka na ji ba zan iya yi masa muso ba na miƙe na tashi zaune duk da kuwa uwar azabar da nake ji.Wani magani ya fiddo cikin aljihu ya miƙo min,“komai za ki ci ki dinga zuba wannan a ciki,in kuma kika kuskure daidai ɗaya rana za ki koma hannun waɗanda kika fito” A lokacin da na ji Ummah na yi masa godiya sai na fahimci tuni ya shaida mata komai,ban yi mamakin yadda aka yi ya san komai ba don na fahimci yana da power.Sannan a cikin coma ɗin da na shiga haka aka yi min wahayin komai ta yadda aka yi ya tarwatsa komai,ashe lokacin da muke yin magana da Dr David Maheer ya shigo restaurant ɗin kuma ya ji abin da nake cewa.Sannan kuma abin da ba ki sani ba Haule sarai Maheer ya san cewa ke ma ba normal mutum ba ce,kamar yadda na dinga kallon abubuwan da kike na siddabaru to shi ma idonsa suna iya ganin duk abin da kike yi” Lubna na kawowa nan da dogon labarinta da take bamu ni da Aliya sai ta yi shiru,ni kuma numfashi na ja kafin na ce “amma ta ya aka yi ni ban san da cewa shi ma yana da power ba sai yau? ” “Saboda ƙarfinsa ya wuce yadda duk kike tunani,kin ga fa shi ne ya kuɓutar da ni daga komarsu tun lokacin ba su sake waiwayata ba.Haka ita ma Ummah ba ta yi sake kan kula da lamurrana ba kullum cikin yi min addu'o'i take,duk asubah in ta gama sallah kamar wata ƴar baby haka take dafa goshina tana yi min addu'o'i ” cewar Lubna. Na dubi Aliya wacce duk yanayinta ya canza kafin na ce “ya dai?” “Babu komai! Amma dai a yadda na fahimta ita ma Lubna ta shiga komar BAƘIN RUHI ne kamar yadda na saba ganin gawarwakin waɗanda suka mutu ta silarsa,su ma jini yana fita ta idonsu” Furucin Aliya ya tuno min da gawar Haidar,murya na ɗan rawa na ce “Lubna bayan an yi wa mahaifinki wanka shin jinin da ya fita ta idonsa ya wanku?” Ta ce “wallahi ban sani ba saboda lokacin ai na faɗa muku ban cikin hayyacina kuma ko da na farka tuni an kawar da shi” Na ce “da buƙatar mu samo amsa,babu kuma wanda zai bamu tabbacin haka sai Ummah.In dai hakan ta kasance to tabbas BAƘIN RUHI nada ƙarfi sosai ta yadda ya bazu a duniyar nan to amma wane ne shi?” na yi tambayar da ni da su babu wanda ya san amsarta..... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 🔞Don Allah masu zuwa suce min complet suke so ku yi haƙuri Ni ma banda shi,yanzu nake typing in kina so ki biya na saka ki group. [05/04 12:15] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});