Chapter 11
Chapter 11
mission ɗin ta zo,zan faɗa muku yadda komai ya wakana sannu-sannu. A daren nan sosai muka jima muna hira kafin duk mu kwanta, washegari Zuly ce ta tashe ni sai kuma ta hana ni na yi wanka sallah kawai na yi na saka kayana waɗanda na fito da su daga gida sai jakata. Fita muka yi muka shiga mota ta kai ni asibiti da tambaya muka samu ɗakin da su Ummah suke. Ina ganinta na je na rungume ta ina tambayar jikin Abba wanda ke bacci. “Da sauƙi sosai yanzu likita ya shigo ya duba shi tare da yi masa allura,ya aikin Lubna? wannan fa?” Ummah ta faɗa tana nuna min Zuly . “Ah na manta ban gabatar miki da ita ba,Zulahait abokiyar aikina ce” na bata amsa. Umma ta ɗan yi murmushi kafin ta ce “ma sha Allah! Allah ya taimaka ya baku sa'a ya kuma baku cimma nasarar aikinku,ki ƙara yi wa oganku godiya don Allah Lubna .Mutum mai kirki jiya bai bar wurin nan ba har sai da ya ga an shiga an kuma fito da Abbanki” Wani irin sanyi ya ratsa ni jin wani abin farin ciki,na so in zauna da iyayena amma Zuly ta ƙi bani damar yin haka ta hanyar cewa “ki dai tashi mu je gida ki yi wanka ki canza kaya sai ki dawo ko?” Da wannan tasa ta ci galaba kaina muka fito,“Zuly mene ne haka? Na ga kamar ba ki son na zauna tare da iyayena” na faɗa ina kafe ta da ido. Ta ce “ke ba fa komai ne ba,ina so dai ki yi wanka ki canza kaya ko kin ji sanyi” “Amma daga nan fa?” “Za mu wuce kamfani” ta bani amsa.Kafin mu shiga mota mu koma can gidanta,da isarmu kuwa wankan na shiga bayan na fito na shirya cikin ɗaya daga cikin abayar da muka siyo jiya.Ina tsaka da fesa turare ta shigo sanye cikin kayan atamfa har da luluɓa uban mayafi kamar ta ƙwarai,ina shirin yi mata tambayar ya na ga ta yi shiga ta kamala daga can falo na ji muryar wani gardi yana kiran sunanta cikin tsawa “Zulaihat?” murya na rawa ta amsa kafin ta kama hannuna ta ce “in ya tambaye ki wace ce ke sai ki ce ƴar uwata ce ke kun zo nan ne domin jinyar mahaifinki” ba ta bani damar cewa komai ba kuma ta ja ni muka fita can falo. Yadda duk ta nutsu cike da tsoro yasa ni ma na kama kaina tare da gaishe shi cike da ladabi,dakyar ya amsa kafin ya ce “wace ce ke?” Sai da na saci kallon Zuly kafin na ce “ƴar uwarta ce,jiya muka zo nan garin domin jinyar mahaifina da ke asibiti” “Ita kuma ta ce min yau ne kika zo” “Eh nan gidan ba,amma ai tun jiya muka zo ni da iyayena suna can asibiti” “Wace asibiti?” “Private asibitin nan da ke kusa da babbar kasuwa” na basa amsa,bai ƙara cewa komai ba sai ya je ya zauna kan kujera yayin da ita kuma Zuly ta je jikinta na ɗan rawa ta fara zuba masa abinci tana gamawa ta zo ta kama hannuna tare da jana muka koma can ɗakina.Bayan ta rufe ƙofa sai ta ja ajiyar zuciya,ni kuma na ce “wane ne kuma wannan?” Cikin ƙasa da murya ta ce “mijina ne,ki bari daga baya zan yi miki bayani” tana gama faɗar haka sai ta fice ta bar ni sake da baki ina mamakin kenan Zuly tana da aure amma ta rasa wanda za ta aura sai babban mutum kuma irin mai zafin kai. Bakin bed na zauna ina tunanin ni ma ai lokaci yayi da zan bai wa maza dama ,saboda can baya gani nake in ba aiki na samu ba to fa ba zan taɓa kula namiji ba. Tsawon lokaci ina wasiƙar jaki kafin Zuly ta shigo ,“ taso mu ci abinci” ta faɗa .Tashin na yi na mara mata baya,ita ce ta zuba mana sai da muka fara ci sannan ta soma bani labarinta. “Lubna kamar yadda kika sani ba duk abin da mutum yake so yake samu ba,to ni ma hakan ce ta faru da ni.Bayan mun kammala karatu na fara neman aiki ,duk inda na je babu nasara sai na samowa kaina mafita wato ita ce ta auren miji mai kuɗi shine fa na auri Alhaji ” tana kawowa nan ta yi shuru ban matsa mata da sai ta ƙara cewa wani abu ba lura da yadda take bani labarin a takure.Bayan mun gama cin abinci daga nan kuma kamfani muka wuce,kafin nan bisa hanya sai da ta ƙara gutsura min labarin nata. “Akwai wani group mai suna sugar Daddy ,a can muka haɗu da Alhaji ta hanyar wata ƙawata na samun link ɗin.Tun da na tura hotona na gabatar da kaina ya biyo ni pc ya ce na yi masa ban kuma ja aji ba muka fara soyayya kar ki so ki ga yadda yake yi min batal ɗin kuɗi.Ba a ɗauki lokaci ba kuma ya zo gidanmu suka yi magana da iyayena waɗanda kafin auren sai da suka tambaye ni ai dai ina sonsa ko ? Na kuwa ce eh.Amma a zahiri ba haka abin yake ba,kawai saboda in samu gidan hutu ne yasa na amince da aurensa.Muna yin aure hannunsa ya koma na jariri hahaha! Ya bar bani kuɗi sai dai fa duk abin buƙata yana zuba min su a store kuma bai damu ba don na ɗiba na yi kyauta da su,ana haka sai na fara haɗuwa da manyan mata .In an je biki su yi ta liƙen kuɗi,wata don ta ɓarar da 200k ba wani abu ba ne ,to abin sai ya fara damuna har na soma tunanin ko rabuwa zan yi da Alhaji .Da na kai wa waccan ƙawata da ta bani link kokena sai ta haɗa ni da oga” tana kawo wa nan da labarin ta yi parking duk muka fito,duk da a lokacin na so jin yadda ta kaya amma na yi shiru muka shiga ciki. Cike da girmamawa aka dinga gaishe ta,direct kuma ofis ɗin oga muka wuce.Yana ganinmu yayi saurin tasowa ya shayar da ni giyar mamaki don kuwa rungume Zuly yayi ƙyam a ƙirjinsa tare da feso wasu kalamai waɗanda suka sa na zauna ban shirya ba. “Ya haka Baby? Na ji an ce mijinki yau yayi saukar asubah,shine ba ki faɗa min ba.Me ya kawo haka ko yayi miki wani abu ne?” Ita kuwa ƙoƙarin fizge wa take,tana satar kallona da sauri na kawar da kai. Ina jin lokacin da oga ke ci gaba da cewa “faɗa min kun yi wani abu da shi ne?” “A'a ! Please ka sake ni mana ” ta faɗa. “Luby ki ɗan fita ina son yin magana da Oga” ko kallonsu ban ƙara yi ba na fita,direct kuma ofis ɗinta na shiga wanda ke kusan na oga.Kaina na ji yana sara min a fili nake tambayar kaina “wai da aurenta take kula wani? Da aurenta take zina? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Ya Rabb ka tsare ni daga sharrin zina Allah kar ka jarabce ni da ita,kar ka kuma nuna min ranar da zan yi ta Ya Rabb kafin ranar nan ta zo Allah ka aiko tirela
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38