Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,245 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tare da haɗe rai ta ce “ki tashi mu je Malama oga na jiranmu” Cike da masifa na ce mata “babu inda zan je! Gidanmu zan tafi” Nan ta yi wata dariya kafin ta ce “au haba? Kenan? To wuce ai ga ƙofa nan sai ki tafi” Sam ban damu da gyatsen da ta yi min ba sai na fita daga ɗakin na fito harabar gidan,babu kowa a bakin get sai na je na buɗe ƙofa da zumar fita nan na yi arba da wata lukutar masifa don kuwa ruwa ne maƙil a wurin tamkar za su taɓo sararin samaniya,babu shiri na koma can cikin falon sai na tarar da ita tana shan ayaba cike da shaƙiyanci ta ce “har an dawo daga gidan ko kuwa an fasa zuwa?” Idona ne suka kawo ruwa shaaa,ina kallon Zulaihat wacce da dukkan alamu babu ɗigon imani a ƙirjinta.Miƙewa ta yi tare da ɗaukar key ɗin mota ta ce “mu je” dole dangi na ƙi yasa na take mata baya muka shiga motar .Mai gadi ya buɗe mata gate yana wani murmushin da ya tabbatar min bakinsu ɗaya shi da Zuly duk munafukai ne,gudu sosai ta yi har muka isa gidan Ogan.Muna shiga ana kiran sallar magrib,a zaune muka tarar da shi kan kujeru na alfarma ya saka ɗan madaidaicin table a gaba mai ɗauke da cake wanda aka yi wa kwalliya kamar ba ci za a yi ba. Tsoron Ogan ne ya ƙara ratsa ni,amma duk da haka ita ɗaya kawai ta gaishe shi.Ya amsa yana kallona kafin ya fara jawabinsa “Luby na san zuwa yanzu kin fara gane aikinki, sannan kin san cikin me kika shiga,da kuma su wa kike tare da su.Sai dai ki sani a tafiyarmu ba gudu ba ja da baya,kamar yadda kika saka hannu a yarjejeniyar tsarin aikinmu za ki yi komai da family suka buƙata wato ƙungiya,to ya zama dole ki yi shi.Sam family ba mu da matsala,ba kamar sauran ƙungiyoyin da kika sani ba ne,mu sam ba mu da buƙatar jini sai in dai mutum ne ya kawo taurin kai muke ɗaukar mataki mai tsauri a kansa.Abin da muke so ba komai ne ba sai abin da bai da amfani wurin al'umma,kamar dai abin da kika gabatar a yau wato kashi/bahaya sai kuma sperm ko yawu ko kuma audugar mata da suka riga suka yi amfani da ita shi kenan fa.Mene ne matsala a nan?” ya ƙarashe tambayar yana mai kafe ni da idonsa masu mugun dafi. Wasu sabbin hawaye suka zubo min kafin na zube a gabansa na ce “don Allah ka yi haƙuri ka goge sunana daga ciki, wallahi na yi ma alƙawari babu wanda zan faɗa wa wannan labarin ko da kuwa iyayena ne” Yayi wani murmushi ya ce “tuni ai iyayenki sun san da aikinki,don yanzu haka mahaifinki na asibiti an yi masa gyaran ƙafa sannan mun aika saƙon cewa yau ke ce za ki yi gadi a babbar pharmacie ɗinmu ta saida magunguna.Ko ba ki yarda ba?” yayi tambayar yana mai jawo wayarsa ya kunna min video duk abin da ya faru tun daga lokacin da aka ɗauko Abbana har izuwa lokacin da suke asibiti an yi masa aiki ga Ummah nan zaune kusa da shi fuskarta cike da farin ciki. Wani irin tausayin kanmu ne ya kama ni,tabbas sun yi min dabaibayin da ban isa na warware ta sauƙi ba. “In kuma kika ce za ki bijire minti biyu yayi yawa zan aika mahaifinki barzahu” oga ya faɗa . Cikin razani na dube shi,sai ya gaskata maganar ta hanyar cewa “ƙwaran gaske ,kamar yadda kai ki ƙasar Turai bai yi min wahala ba haka zan katse igiyar numfashin mahaifinki don haka kar ki kawo min wasa ki zo ki yanka cake ɗin nan kafin ya sha iska” Yana gama faɗar haka sai Zuly ta miƙa min wuƙa,ba don na so ba na yanka cake ɗin wanda yayi daidai da jin wani mashi ya caki zuciyata tamkar ma zuciyar tawa ce na yanka. Mu uku muka cinye cake ɗin duka,kafin Zuly ta ja ni mu koma can gidanta..... Ga masu son fara yin payment 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [02/04 11:51] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 06 Da muka isa gidanta dakyar na samu na yi sallar isha'i,ita kuwa magrib kamar yadda lokacinta ya wuce to haka ta wuce ni don ba zan ranka ta ba. Gida nake son tafiya,amma da dukkan alamu ba zan samu wannan alfarmar ba.Haka na yi shuru cikin ɗaki ina tunani iri-iri da kuma mamakin yadda Zulaihat ta koma muguwar sheɗaniyar marar imani.Na goge hawaye masu ɗumi da suka zubo min lokacin da tunanin yadda na ga iyayena suna farin ciki ya faɗo a kwanyata. “Luby sai fa in kin so ne za ki damu,kamar yadda oga ya faɗa miki mu family sam ba mu da wata matsala.Kin ga fa babu wani abu da za a nema wurinki in kika cire lokacinki,ni ban ga abin damuwa ba a aikin da babu kashe mutane ciki sannan ko jinin ɗan tsako ba mu buƙata” A lokacin da ta yi min wannan magana sai kuma na ga fa kusan tana da gaskiya,duk da cewa su ɗin matsafa ne amma dai fa ba su kashe mutane.Amma abin da ya fi bani mamaki bai fi ta yadda suke son abubuwan shirme ba,cikin son sanin dalilin haka na jefo mata tambayar “Amma Zulaihat me za ku yi da kashin mutane?” “Don Allah ki bar ce min Zulaihat ɗin nan,ki kira ni da Zuly sannan maganar me za mu yi da kashin mutane ke ce a ba ki san amfaninsa ba shi yasa amma da shine ai ake yin takin zamani ana kaiwa gona don yin noma” Na ja ajiyar zuciya da yake ni sokuwa ce sai na yarda da maganarta,kuma in faɗa muku gaskiya sosai kalamanta suka yi tasiri a raina don sai na ji na kuma yarda zan yi aiki da su.Ban taɓa sanin illa ne ba sai da na haɗu da ke Haule na ga irin abubuwan da kike yi na ban mamaki. Jin na samu ƴar nutsuwar ruhi sai na je na yi wanka da ruwa masu ɗumi,da na fito na sha salade na fruit sai kuma a lokacin ne Zuly ta bani wayata wacce take sabuwa dal.Wani irin daɗi na ji ganin ta canza min waya amma layina ne a ciki,ta yi wani murmushi tare da zama kusa da ni ta ce “kwaɗayin na gan ki cikin daula yasa na kawo ki cikin family,dubi yadda jikinki yayi kyau cikin ƙanƙanen lokaci ” Na ɗan yi murmushin farin ciki kafin na ce “ni dai ki koya min yadda ake aiki da ita” ta yi ƴar dariya kafin ta soma nuna min,muna yi muna taɓa hirar makaranta da kuma ƙawayenmu wanda muka yi aji guda.Duk wani wanda nake da labarinsa sai na faɗawa Zuly aikin da ya samu ko kuma halin da yake ciki.Ban taɓa tunanin cewa rahoto ne take haɗawa ba don farmakarsu sai a ranar da ni ma tawa

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});