Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya shiga sawun gaba bayan yayi nafiloli sai ya zauna har lokacin sallar yayi .Tuni kuma masallacin ya cika aka tayar bayan an gama ne Uncle Salem ya juyo yana kallon headmaster wanda ya zauna kafaɗa da kafaɗa da shi.Ya saki wani murmushi kafin ya ci gaba da yin Azkhar ɗinsa,har sai da ya gama kafin ya basa hannu ya ce “ Assalamu alaikum ” Headmaster cikin mazgewa ya miƙawa Uncle hannu suka yi musabaha wacce yayi da na sanin yin ta,don kuwa akwai kumfan magani a hannunsa na karye sihiri. “Wa'aleykum Salam ! Fatan an sauka lafiya?” ya amsa tare da saurin janye hannunsa. Uncle Salem ya ce “ lafiya lau alhamdullah ! Na zo duba wurin da matata ne za ta yi aiki ita da Kakarta sai kuma na ga wuri yayi kyau” Cike da takaici headmaster ke kallon Uncle ,don kuwa tun zuwansa jiya akan idonsa na ɓoye ya sauka.Sannan sarai ya san da shi ne ya warware zare da abawar da ya ƙullawa Inna A'i,amma saboda ya iya munafurci shine zai ce masa wuri yayi kyau. Cike da iya tako shi ma headmaster ya ce “ ai kuwa dai school Ƙwargwam na kula da malamanta har ma da ɗalibai” Uncle wani murmushin ya sake yi kafin ya ce “ ni ne shaida,amma me yasa kuka bata ɗaki mai lamba uku bayan ita sabuwar zuwa ce?” “ Ɗakin nada matsala ne?” “A'a kawai na tambaya ne” “In ba ta sonsa ai sai a canza mata” “ A'a na faɗa ma wuri ne mai kyau,kuma lamba ukun ai ita ce daidai da ita surukar Inna Delu guda” Uncle ya faɗi haka ne ya na saka idonsa cikin na headmaster don yi masa gargaɗi kan cewa kar ya sake cutar masa mata in kuma ya ƙara yin kuskuren haka shi da shi shege ka fasa.Da sauri kuma ya miƙe ya barsa nan. ★ Bayan na gama sallah haka na tsure Inna A'i da tambayoyi sai ta faɗa min inda ta je amma sai kwana-kwana take yi min daga ƙarshe ma ta shige kitchen tana cewa “bari na haɗa mana breakfast ” Na ce “ yau fa Litinin ko kin manta azumi muke ni da Uncle ” “ A'a yau ba za ki yi ba,ki bari har Alhamis ” Uncle ya faɗa wanda ke shigowa.Na dube shi da mamaki jin yau shine ke cewa na ajiye azumi,“ Uncle ina yi fa” na faɗa kamar zan yi kuka ina kallonsa.Ya ɗauke kafin ya ce “a'a akwai maganin da za ki sha yanzu kafin ki ci komai” sai yayi gaba ya ƙarasa gaban jakarsa ya fiddo wata kwalbar zuma. Ido tab hawaye nake dubansa,ya ɗago ya kalle ni kafin ya ce “za ki zo ki sha ko sai na zo nan na ɗauko ki na matse miki baki tare da ɗura miki shi?” Jin ya fito a Uncle Salem ɗinsa mai tsanani yasa na ƙarasa gabansa na yi zaune tare da tanƙwashe ƙafafuna.Da wata ƴar ƙaramar cokali ya soma bani zumar har sai da na sha bakwai da ita kafin kuma ya soma bani wasu sauran maganin,ɗaya kuma ya ce “ wannan kuma sai in kin ci abinci za ki sha” sai ya miƙo min na karɓa ina gunguni. Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ Naf sai yaushe za ki girma?” Kamar suɓutar baki na ce “ ranar da ka yi min aure” Shuru yayi bai ce komai ba,ni ma sai na rashin kunyata.Na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa sai na ga ashe ni ɗin ce yayi ƙuri kamar mai kallon tv.Zan yi ƙasa da kai yayi saurin tallabo haɓata ya ce “ da gaske kin shirya zaman auren?” Na lumshe ido ina dariya,ya ce “ faɗa min na ji saboda in na koma gida na yi wa Daddynki magana a soma shirin biki” Na ɗan cinno baki gaba na ce “ni da ko saurayi banda” kamar daga sama na ji bakinsa kan laɓana, wannan karon dai kam cikin hankalina nake.Cike da razani na buɗe ido kafin da sauri na tashi daga gabansa jikina na ɗan yin rawa,duk da ba yau ne ya saba yi min kiss ba amma a goshi ne ko a kumatu ya saba min sannan an ɗauki lokaci mai tsayi rabon da yayi. “Nafisa?” na ji muryar Inna A'i,da sauri na nufi kitchen ɗin ina jin daɗin kiran nawa da ta yi.Ina shiga ta yi min wani kallo sai na ji na tsargu na yi tunanin ma ta gani ,a ɗan daburce na ce “ ni ma ban san me yasa Uncle yayi haka ba,shi ba giya yake sha ba ballantana na ce bai cikin hayyacinsa ” “Ungo ni ki je ki sha ya fi wannan surutun da kike yi min marar kan gado,duk duniyar nan akwai mai sonki sama da shi Salem ɗin da har za ki yi tunanin zai yi abin da zai cutar da ke” Inna A'i ta faɗa . Na karɓi kofin kunun tare da komawa can gefe na soma sha sam na ƙi yarda na koma can,ita ma ba ta matsa min amma ina shanyewa sai na fito don tuni gari yayi haske sannan lokacin da za mu je bakin aji ƙarfe bakwai ne. Ina fitowa na gansa a zaune ido rufe yana wani jan numfashi tare da ɗan game fuska haɗi da yamutsa ta.Toilet na shiga na yi wanka,da na fito sai na tarar ba ya nan.A gaggauce na shirya tsaf,na zuba takardun da zan yi amfani da su da abin rubutu. Inna A'i ta fito tana min wani kallo kafin ta ɗauke kai,“ki je yana mota yana jiranki ku yi sallama” Jiki a sanyaye na fita ganin irin yadda ita Innarmu ta canza min fuska wacce nake ɗauka uwa ta biyu.Hijabi na saka kafin na fita,gidan gaba na buɗe na zaune na sunne kai tare da yin shuru ina wasa da zoben hannuna.Kujerar da nake zaune a kai ya ɗan buɗe ta ja baya,da sauri na kalle shi yadda na ga idonsa sun kaɗa sun yi ja yayi bala'in bani tsoro.Murya na ɗan rawa don duk a tunanina kuka ne yayi,na ce “Uncl...” sauran maganar ce ta maƙale jin bakinsa kan nawa abin ma bai tsaya nan ba ya soma shafar hijabina ta sama .Hawaye ne suka soma zubo min ,ba yau ne farkon jin cewa uba yayi mu'amala da ƴarsa ba na sha jin ire-iren labarun nan a kafar BBC amma ban taɓa tunanin akwai ranar da abin zai zo kaina ba don ban taɓa banbance Daddy da Uncle ba.Duk abin da yake yi ko motsi ban yi ba da yatsana ballantana na yi yunƙurin hana shi ,hawaye kawai nake yi don babu bakin kuka saboda Uncle ya mayar da shi sweet ɗinsa.Sama da minti goma kafin ya janye daga gare ni amma ina jin hucin saukar numfashinsa kusan fuskata da na rumtse idona.Shashekar kukansa da na ji ta yi kuma bala'in tayar min da hankali fiye da abin da ya gama yi min,na buɗe idona ina kallonsa shi ma hawayen yake fitarwa kafin ya kama hannuna dukkan biyun ya ce “ don me Naf? Me yasa kike horar da ni da yawa? Me yasa ba ki ganin zazzafar ƙaunar da nake yi miki? I love

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});