Chapter 24
Chapter 24
mata don ko na ce zan faɗi abin da na gani a mafarki kamar abin tsayi sam bakina ba zai iya furtawa ba. Hawaye kawai nake yi,sai shi ma Daddy ya shigo yana tambayar lafiya.Kai kawai na girgiza masa ,ya zo ya kamo hannuna ya ce “ kina ji na Nafisa faɗa min mafarkin me kika yi?” da sauri na janye hannuna daga cikin nasa,na diro daga kan bed na nufi ƙofa. Sai kuma na yi tsaye ganin Uncle shi kuma zai shigowa gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala ce yayi. Haɓata ya tallabo ta yadda zai iya kallon fuskata da kyau ,tsakiyar idona ya dinga duba yana wani motsa baki kafin ya ce “kin kuwa yi Azkhar yau?” Idona na soma juyawa ina son kauce kallon nasa da ba ƙaramin takura min suke ba,sam babu daɗi ji nake kamar yana zuƙo raina ne. “ Kin yi Azkhar na ce?” ya sake tambayata. Kai na girgiza alamun a'a,don kuwa ban yi saboda tun asubah na samu saƙon cewa sunana ya fito a jerin waɗanda za su je bautar ƙasa wannan zumuɗin ya shagaltar da ni yin Azkhar kamar yadda na saba. Ya sake ni kafin ya ce “ biyo ni” sai ya juya,haka na take masa baya ina waiwayen su Daddy muka fita zuwa can sashensa da yake waje. Ɗakin Uncle Salem ciki biyu ne da falo,ɗakinsa guda na bacci guda kuma wanda yake zuba kayan maganin aljanu na ruƙiya.Direct ɗayan ɗakin muka shiga,kaina ne ya juya da na shaƙi warin magani iri-iri yayin da gefen cikina daidai inda aka soke ni ya soma motsi har sai da na danne wurin. “ Zauna a nan” Uncle ya nuna min wata doguwar kujera,babu muso sai na zauna ɗin.Wata kwalba ya ɗauko tare da zuwa kusa da ni ya zauna kafin ya buɗe ta,tun kafin ya ce min na sha na soma hawaye don ni kaɗai na san irin abin da nake ji a duk lokacin da ya bani ire-iren maganin nan. Bakina ya taɓe tare da ɗura min maganin,jikina ya ɗauki rawa kafin cikin fitar hayyaci na soma basa labarin mafarkin da na yi tiryen-tiryen.Kwantar da ni yayi yana mai jan doguwar rigar jikina sama,da sauri na rumtse ido lokacin da ya janye hannuna ya ɗora nasa a daidai wurin da ake ta yi min motsi. Teburin da ke ɗauke da tarkacen da shi kaɗai ya san na mene ne ya jawo,ina ji ina gani da raina Uncle Salem ya soma tsatsaga fatata da reza.Banda wani zaɓi banda hawaye don tuni maganin da ya bani ya kashe min dukkan jijiyoyin jiki sai kaina da ke faman juyi tamkar an jefa ƙwarya a ruwa. Wata kwalba ya ɗora daidai wurin ya soma tatsar jinina har ƙarar fitarsa kake ji,kamar minti biyu kafin ya cire kwalbar ya ajiye ta kan teburi.Wani magani ya shafa min a daidai ciwon mai bala'in zafi,har sai da raina ya kusa fita kafin da sauri ya cika bakinsa da wasu ruwa ya zo ya fara shayar da ni su.Duk ɗigo ɗaya na ruwan da zan sha to tamkar ana warware azabar da yake jikina ne , wannan yasa nake shan maganin cike da zalamar da ta haifar min da soma shan yawunsa da kuma laɓansa. Jikin Uncle Salem ne ya ɗauki wata irin rawa jin Naf ɗinsa na sumbatarsa kamar za ta cinye leɓensa,duk wani tsohon feeling nasa da yake faman yin ƙasa da shi a kowacce safiya ya soma taso masa.A daidai gaɓar da ya soma mayar mata da martani kuma tuni bacci ya ɗauke ta,idonsa na fitar da wasu irin hawayen jaraba ya soma sunsunar wuyanta yana jin tamkar ya mayar da ita cikakkiyar mace ko zai samu salamar ruhi. Dakyar ya rareashi kansa ya janye daga jikinta,daɓas ya zauna yana duban yadda take baccin wahala . Ƙonannen jinin mai tattare da guba yayi baƙi ƙirin a cikin kwalba,sai ya ɗauke shi ya je ya zubar toilet ya wanke kwalbar. Sai da ya je ya sake wata alwala sannan ya nufi masjid,a can ya samu Daddy bayan sun yi sallar sun fito ne Uncle Salem ya dubi abokin nasa ya ce “ Abdul Hameed ban san me yasa ka zaɓi ka ɓoye min rufaffen sirrin Nafisa ba,amma hakan bai da wani amfani don kusan na fahimci matsalar junun da ke jikinta ya samo asali ne daga can tushe ba wai gamo ta yi da su ba” Cak Daddy ya tsaya yana kallonsa, Uncle Salem ya jinjina masa kai ya ce “ tabbas ko yau sun ziyarce ta,saboda sakacin addu'ar da ba ta yi ba” Daddy ya ce “ mu je can gida zan yi ma bayani” haka suka wuce suka isa,a keɓaɓen falon Daddy duk suka zauna tare da yin shuru Uncle Salem ya matsu ya ji labarin yayin da shi kuma Daddy ya rasa ta ina zai soma.Can ya nisa tare da furzar da huci kafin ya ce “ to da farko dai kamar yadda na faɗa ma ni ɗana ga sarauniya Ayodele Ayush,kafin zuwan Musulunci a Victoria Falls suna bautar ababen bauta iri-iri ,yin tsafi kuma sai ya zama adon garin.Sai dai sannu a hankali duk komai ya canza saboda yadda mahaifina sarki Ameer ya taka muhimmiyar rawa ganin ya kawar da duk wani fasadi sai dai kash zuwana duniya kuma aka tsiro da wasu sabbin canfi wai alamomi sun nuna za a sake yin maimaici wato daga cikin tsatsona za a samu wacce za ta jagoranci mulkin ƙasar.Amma tabbas ni ba magajin sarki ba ne,sosai na ji tsoro da jin haka don tamkar karatu haka ake biya min maganar nan har na mallaki hankalin kaina” Uncle Salem yayi saurin katse shi da cewa “ haba aboki ta ya za ka yarda da wani canfi?” Daddy yayi murmushi wanda ya fi kuka ciwo kafin ya ce “ dole na yarda mana,duba da tun ina ɗan shekara ashirin a duniya na ajiye iyali saboda yadda kullum nake kasa bacci ina harin neman abokiyar rayuwa wacce zan jefar wa da ƙwan haihuwar shugabar gobe ko zan samu sukuni ” Uncle Salem ya ce “ kana nufin wai Naf?” Daddy ya jinjina kai ya ce “aboki tun lokacin da na yi aure zan ce ma wannan larurar da ka san ni da ita ta mugun feeling ta kau,shi ma tun a daren farkonmu.Sannan kana dai ganin yadda lamarin aurena ya kasance a sirrance sai daga baya iyayena suka sani,har bisa yanzu sarki fushi yake da ni saboda na ƙi yarda na zauna a can Victoria Falls ni kuma ina gujewa Nafisa ƙalubalen da za ta fuskanta ne in ta zama shugaba” “To amma mene yake baka tabbacin cewa hakan za ta kasance?” Uncle Salem ya tambaya . Daddy ya ce “ saboda kama take da wata goggon Mamana ita ce mace ta biyu da ta mulki Victoria,to yadda ka ga Nafisa ita ma haka take kai kace tsaga kara ne aka yi.Hakan kuma babbar matsala ce domin zai iya kasancewa ita ta dawo duniyar nan a gangar jikin Nafisa ” “ Wai ko sarauniya Deborat?” Uncle Salem ya tambaya,don kuwa ita ɗin ba ɓoyayya ba ce a duniyar nan duk kusan labarinta ya karaɗe ƙasashen duniya saboda shahararta wurin iya yin tsafi,sai dai ko kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38