Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,240 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya gama shan yawuna ba yanzu. “Ga ta nan ita ce mai maganin” Hajiya ta faɗa tana wani murmushi kafin ta ɗan bangaje ni ta ce “ki gaishe su” A ɗan rikice na ce “ina wuninku?” kusan duk a tare suka amsa kafin ɗayan ya ce “hajiya dama wannan ce ai kamar na sha ganinta restaurant ” yayi furucin yana wani sanyayyen murmushi yana ɗan ƙare min kallo. “Eh ita ce, tana ɗaya daga cikin masu kula da restaurant ɗin ai” Hajiya ta faɗa . “To likitar gargajiya muna son ganin maganin naki ” ya ƙara faɗa wannan karon cikin raha. Da sauri na kalli Hajiya kafin kuma na maida dubana ga Maheer wanda nake jin idonsa a kaina tun ɗazu. “Eh muna son gani Please ” shi ma ɗayan likitan ya faɗa. Hannuna na ji yana jimƙewa da kansa,yayin da kuma nake jin muryar Maheer tana furta wasu harufa cikin Yaren da ba na Hausa ba,haka ma turanci.Kallonsa na tsaya yi yadda sam bai nuna alamar yana yin wani abu ba,amma tabbas amon muryarsa na fita wanda ina da tabbacin iya ni ɗaya ce kawai nake jinta. Ba a ɗauki lokaci ba na ji wani abu jimƙe cikin tafin hannuna,sai na ɗago hannun tare da buɗe shi nan idona yayi tozali da wata koriyar flowers mai masifar haske. “Waooo! ” likitan ya faɗa yana mai zuwa ya ɗauke flowers ɗin daga tafin hannuna kafin ya ce “wannan ai furen floris,Dr Muhamud ka tuna Dr Maheer ya taɓa nuna mana ita?” “Eh sosai ya ce tana maganin komai amma a lokacin ba mu yarda ba,amma Umar ba ka ganin kamar abin nan camfi ne?” “Ya isa haka don Allah,ku bata furenta ta tafi kun tsaya surutu sai ka ce yau ne kuka fara ganin abin almara” Maheer ya faɗa cikin ɗaga murya,duk suka tuntsire da dariya kafin su fara tsokanarsa can kuma shi Dr Muhamud ɗin ya zo ya miƙo min furen,sai da na saci kallon Maheer kafin na karɓa.Har tuntuɓe nake wurin barin falon,ina shiga ɗaki na ja wata doguwar ajiyar zuciya ban taɓa jin tsoron Maheer ba sai yanzu har wani ƙwarjini na ga ya ƙara min. Ban tarar da Lubna ba, kitchen na wuce don na fi zaton tana can amma kafin nan sai da na ɓoye furen floris ɗin cikin kayana.Ai kuwa can na same ta tana ta aikin tuwon gobe,wuƙa na ɗauka na soma yanka mata albasa ba tare da na ce komai ba.Ita ma sai ta ƙi tanka ni sai ma waƙe-waƙe da ta tsira wanda kusan duk na habaici ne. Na yi ɗan murmushi na ce “ko ki tambaye ni yadda muka yi” Ba tare da ta dube ni ba ta ce “ai na san ba za ki kasa nemowa kanki mafita ba tun da kamar aljana haka kike ” “A'a aljanar ce ba kama ba” na faɗa ina dariya . Ta ce “to ƙila ɗin ma haka ne tun da babu wanda ya san abin da ke cikin duhu” “Amma kin san da cewa na tsorata sosai?” na tambaye ta ina mai tsayawa da yankar albasar. Ta ce “na san dai ba na Maheer ba sai dai ko abokansa” “Wai ke duk komai kin sani game da shi? Ya aka yi kika san abokansa ne?” ba ta kai ga bani amsa ba Hajiya ta shigo kitchen ɗin,wata ƴar matashiyar budurwa na take mata baya. “Lubna ga sabuwar ƙanwa na samo miki,za ta dinga taya ki aiki ki dinga nuna mata komai yadda ake yinsa,don ina sa ran ƙara sunayen jerin wasu sabbin abinci” Cike da ladabi ta gaishe mu duk da dai ko na girme mata ba irin can ba,Lubna ta ce “me sunanki?” “Aliya” ta bata amsa sai muka ɗan kalli juna,Hajiya ta ce “mene ne kuma?” “Babu komai” muka amsa mata. Har ta kai bakin ƙofar fita ta ce “Haule ki haɗa wa Alhaji tea ki kai masa ɗakinsa ki saka citta dayawa da lemun tsami” “Wane alhajin ?” na tambaya da sauri har ina sakin wuƙar hannuna ban shirya ba,Hajiya ta juyo fuskar nan kicin-cikin kafin ta ce “alhaji nawa ke da kwai gidan nan?” Sai da na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ɗaya” sai kuma ta juya ta yi tafiyarta.Jikina na ɗan ɓari na ɗora tukunya kan gas na soma haɗa masa tea ɗin wanda dama can ni nake yi amma ban taɓa kai masa shi ɗakinsa ba ina dai jera su kan dianing. Tsit kitchen ɗin ta yi sai Lubna da ke magana jefi-jefi tana kwatanta ma Aliya yadda ayyukan ke tafiya.Ni kuma ina gama dafuwar tea ɗin na juye shi cikin flask na ɗora kan tray da kuma kofukansa,sai da na dubi Lubna kafin na fita na yi tunanin za ta cece ni ta ce na kawo ta kai. Tun da na fara taka step ɗin da za ta kai ni ɗakinsa jikina ya soma rawa,hakan ya bai wa kofukan yin ƙara suna fitar da wani sauti. Bakin ƙofar na ja na tsaya,na fi minti biyu kafin na danna ƙarar rawar neman izinin shiga.Ƙofar ce ta buɗe da kanta,wani sanyi ya ratsa ni haɗi da wani dadaɗan ƙamshi.Murya can ƙasan maƙoshi na yi sallama,ba tare da kuma na ɗago kaina ba. “In kika zuba min ruwan zafi mugun duka zan yi miki fiye da wanda aka baki labari” na tsinkayo muryarsa.Da sauri na ɗaga kai sai na ga ashe ina kusa da shi,hannuna na rawa na ajiye trayn kan table ɗin madubi da ke tsakiyar lafiyayyun kujerun ɗakin.Ina juyawa ƙofar ta rufe kanta,na juyo da sauri ina kallonsa murya na ɗan rawa na ce “hajiya ta ce na kawo ma tea ga shi nan,ni zan tafi” Wani miskilin murmushi na ga yayi kafin ya ɗauki kofi ɗaya ya soma haɗa tea,bayan ya gama ya ƙara ɗaukar wani kofin shi ma ya zuba a ciki duk ina tsaye ina kallonsa. Ya ɗauki kofin ya soma kurɓa kafin ya ɗago ya dube ni ya ce “ki ɗauka ki sha” ko motsawa ban yi ba,sai da ya ƙara cewa “in ba ki sha shayin nan to a nan za ki kwana” ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɗauki kofin na soma sha da sauri duk da kuwa yana da zafi.Ina gama shanye wa kuwa na ji ƙofar ta buɗe da kanta,da wani irin sauri na juya har da ɗan guduna don gani nake in na tsaya wasa ƙofar za ta sake rufewa. Da na fito ji na yi tamkar na baro wuta ne na shigo aljanna, kitchen na koma na taya su aikin sai da aka kira sallah na fita. Ko da na gama sallar ma ban koma ba,ɗaki na yi zamana don gobe ni ma a tsaye zan wuni aikin kai wa mutane abinci.Har sai da aka yi sallar isha'i sannan na fita zuwa ɗayar kitchen wacce ita kuma iya girkin gida kawai ake yi a cikinsa.Kuloilin da ta zuba abinci na soma ɗauka ina kai wa can kan table ɗin cin abinci,bayan na gama sai na ɗauki kwanon abincinmu wanda aka sauya mai girma ƙila saboda zuwan Aliya ne.Ko da na koma ɗaki sai na tarar da su duk sun shigo,Lubna ta fara shiga wanka sannan ita ma ta yi daga nan sai na

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});