Chapter 6
Chapter 6
juye abincin cikin babban faranti muka muka soma ci amma sai na lura Aliya babu abin da take sai satar kallona,tun ban damu ba har na tsargu na ce “Lubna ƙanwarki sai kallona take ki tambaye ta halan na yi mata kyau ne” Lubna ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “to ke kin ji Aliya wai kina kallonta” Maimakon ta kawar da dubanta a'a sai ma ta ƙara ƙure ni da ido kafin ta ce “na ga ba ta lafiya ne” Da mamaki na ce “wa ya faɗa miki banda lafiya?” Sai da ta saki wani murmushin kafin ta ce “ga gubar maciji nan tana yawo a jikinki” Kasa ci gaba na yi da cin abincin,ban ce komai ba sai Lubna ce ta yi magana “wace irin magana ce wannan? Ya za ki ce guba na yi mata yawo a jiki? Ke ta ya aka yi kika sani? Ke ki bar ma wannan maganar don in wani ya ji sai ya ce mayya ce ke,Ah to in ba maye ba wane ne zai iya ganin abin da ke cikin ɓargon jikin mutum” Lubna ta ƙarashe cikin faɗa yayin da ita kuma Aliya ta kai hannunta kan goshina ,nan take wani baƙin ruwa suka soma zubo min ta baki da hanci.Kamar zan mutuwa haka na ji yayin fitar abin,can kuma ta janye hannunta wanda yake ta kunno koren haske daga can tsakiya tamkar an kunna lantarki. Lubna ta zabura ta tashi tsaye tare yin baya tana “Ya Rasulullahi! Manzon Allah!” Ni kuwa ido na zuba wa Aliya ko kafin na ce wani abu an turo ƙofa,Maheer ne.Da sauri ta ɓoye hannunta mai hasken a bayanta,shi kuma ni ya kafe da ido kafin ya saki murmushi ya ce “kar ma ki ɓata lokacinki ko kin yi yunƙurin fitar da shi ba zai fito ba”maganar ido ce yayi min ya fice,sai kuma na fahimci cewa ba wai iya ni ɗaya ce wannan karon na ji shi ba har da Aliya wacce jikinta ya ɗauki kyarma tun lokacin da ta ga Maheer ɗin. “Wace ce ke?” na jefo mata tambayar,ba ta bani amsa ba sai tashi da ta yi a guje za ta gudu amma tamkar wata ɓarauniya haka na yi saurin cabko ta na riƙe ta gam ina mai ce mata “wallahi babu inda za ki sai kin faɗa min wace ce ke”........ [16/03 11:36] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 04 Jikin Aliya ne ya soma yin rawa kamar mazari kafin ta ce,“don Allah anty Haule ki bar ni na tafi wallahi in ya gano ni ce nan na yi masa kutse zai iya hallaka ni ” Cikin ɗaga murya na ce “ba fa zan bar ki ba ,gwara ma ki bani labarinki kuma muddin ina tare da ke to babu abin da zai iya yi miki.Hatta ita gubar da ya bani na sha ba wai don ya cutar da ni ba ne a'a don ya dinga controling tunanina ne” Lubna da ke can tsaye a raɓe ta ce “wato kenan kin san da gubar ma a jikinki? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Allah ka tausaya wa rayuwata kar ka ƙara jefa ni cikin wani cakwalkwalin uƙubar da na tsira a baya” Na dube ta kafin na ce “don Allah Malama ki zo ki zauna kika wani tayar da hankalinki sai ka ce baƙuwar ganin abubuwan nan na siddabaru” Wata muguwar harara ta jefo min kafin ta kalli Aliya wacce har zuwa yanzu hannunta na fitar da wannan hasken. “Wace ce ke Aliya?” na sake jefo mata tambayar a karo na biyu. Kai tsaye ta bani amsa da cewa “ni ɗin almajira ce,na taso cikin Bara na kuma girma cikinta.Ni ɗin ba muguwa ba ce kamar yadda kika yi tunani,duk da kuwa ina ɗauke da BAƘIN RUHI a gangar jikina amma ban taɓa cutar da wani ba sai dai na bai wa kaina kariya ga masu son cutar da ni” Na ja wata ajiyar zuciya kafin na ce “amma me yasa kike jin tsoron Alhaji?” “Saboda shi ne babba a gare ni,powersa ta fi tawa ƙarfi sannan a tsarin zubin halitta protector ɗinsa ya fi nawa tasiri” Ina jin abin da ta ce sai na dubi Lubna wacce goshinta ke tsatsafo da zufa.Na saki ɗan murmushi kafin na ce,“na ga powerki irin wacce ake iya sharing nata ne ,ko za ki taimaka ki gutsurawa Lubna ko da ɗigo biyu ne?” Aliya ta jinjina kai kafin ta dubi Lubna wacce ke shirin artawa a guje amma na harɗe ƙafafunta ta hanyar kallo kawai,don ina juya idona ta kasa motsi na riƙe su gam. Na miƙe tsaye ina riƙe da Aliya har zuwa yanzu,ita ma tashin ta yi da taimakona ta samu ta dafa goshin Lubana koren hasken ya fita shuuu kamar yadda ake zuba man fetur a babur,yana fara shiga kuma ta yi saurin janye hannunta. Na saki murmushi na ce “yanzu dukkan tsoronki zai fice,shi kenan ke ma kin dawo tsagenmu” Da idonta da suka kaɗa suka yi jawur lokaci guda take kallona amma ta kasa magana,ban damu ba don na san ƙarfin ikon sarrafa wani yankin power Aliya ne ke ratsa jininta. An ɗauki kamar minti goma kafin Lubna ta dawo normal,ta ja wata ajiyar zuciya kafin ta ce “Haule kin kyauta kin mayar da ni mai ido uku,sai dai ki sani yau ba zan bari ki rumtsa ba sai kin bani labarinki duka” Na yi ƴar dariya kafin na ce “labarina nada tsayi sosai Lubana amma ke ki fara bamu naki,in kin gama sai Aliya ta ɗora daga ƙarshe ni kuma sai na dinga baku nawa lokaci zuwa lokaci” Da sauri Aliya ta ce “eh hakan yayi gaskiya” sai duk muka samu wuri muka zauna. Yanayin fuskar Lubna ya canza kafin ta ce “ban ma san daga ina zan fara ba,farko dai zan iya cewa na yarda da karin maganar nan da Hausawa ke yi ' ba duka ƙyalƙyali ne gwal ba' tabbas na yarda da hakan bayan shekaru biyu da suka gabata na rayuwata.Kamar dai kowacce ƴar talakawa haka na tashi da burin samun aiki mai tsoka , wannan yasa na kashe kaina wurin yin karatu tuƙuru.Na bi duk wani matakin ilimi da kika sani,na yi digiri har da digirgir sai dai fa samun aiki ne ya zama jan aiki.Tun ina ajiye takarduna har na gaji na bari,cikin haka ne Umma ta sama min gurbin aiki nan wurin Hajiya can farko iya zuwa can restaurant ne aikina ina kai wa costumer abinci .Kamar yadda kika sani iya wannan aikin kawai ba wani kuɗi ne masu yawa ba,amma haka nake yi don gujewa zaman banza.Sama da wata biyar ina wannan aikin ,daidai ɗaya rana ban taɓa cire burina na samu babbar kujera akan karatun da na yi ba.Sau tari ina jin haushi in na ga masu kuɗi suna shigowa nan su ci abinci na kuɗaɗe dayawa har su bar ragowa nan.Masu zuwa da ƴan mata kuwa haka zan zauna ina ta kallon yadda maza ke tattalinsu,duk abin da kika duba a jikin ƴan matan kuɗi kawai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38