Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,236 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da yin dariya kafin na ce “wato na basa budurcina? Akan wane dalili kenan? To ba zan yi ba,sai dai ku cire ni daga cikin family ɗin amma ba zan taɓa aikata zina ba” Da wani mugun sauri oga ya zagayo ya zo inda nake ya kama kafaɗuna ya ce “ Luby wannan dolenki ne! Kin ga ki ajiye hankalinki babu fa wata matsala sau ɗaya tak ne zai yi shi kenan ” Hawaye suka zubo min masu ɗumi,ji nake kamar na shaƙe wuyan oga har sai ya mutu na sake shi . “Na bata nan da sati ɗaya,ta je ta yi shawara don ina da ayyuka masu muhimmanci a gabana kowa zai iya tafiya” Boss ya faɗa tare da miƙewa ya koma hanyar da ya fito. Nan kowa duk ya watse,Zuly ta kama hannuna muka fito muka bar oga can.Har muka isa gida tana yi min nasiha haɗi da shawarwarin banza wanda in sun shiga kunnena sai su fita ta ɗayan kunnen,sam ban ji zan iya yin abin da suka ce ba. Na yi tunanin da zarar mun je za mu koma can Kamaru ne,amma sai na ji wata sabuwa wai zan sake yin wani zama da mutanen da na tallata musu hajarmu. Cikin bahon wanka na shiga na lumshe ido,tunanin iyayena da kuma abubuwan da suka faru suke ta min yawo a kwanya.Har sai da ruwan suka huce na zuba wasu sannan na yi wanka na fito,cikin kayan bacci na shirya sannan na kwanta sai dai fa na kasa yin baccin haka na yi ta yin juyi bisa gado.Can sai ga Zuly ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin tray ,tashi na yi zaune ita ma ta zauna bakin gado tare da miƙo min kofi ɗaya na madara ita ma ta fara shan guda. “Wacce shawara kika yanke ?” ta jefo min tambayar. “Game da me fa?” ni ma na tambaye ta. Da ɗan mamaki ta dube ni kafin ta ce,“maganar Boss ɗin ce kika manta?” “Shi wane ne?” ban ida rufe bakina ba kofin da ke riƙe da hannuna ya tarwatse har sai da kwalba ta shige min hannu nan take jini ya soma zuba. Jikin Zuly ya ɗauki rawa,sai ta dubi madubin da ke a ɗakin kafin kuma ta taimaka min ta tsayar da jinin ta naɗe min shi da bandeji. Sosai na tsorata ban taɓa tunanin Boss nada power har haka ba,don babu tantama shi ne ya tarwatsa kofin.A tsorace nake kallon Zuly kafin na ce “don Allah ki mayar da ni gida” Muryar Boss ta fito ɓaro-ɓaro ta cika ɗakin “duk inda za ki je ba za ki taɓa boyewa ganina ba,na soma bibiyarki kenan” Da sauri na rungume Zuly ,sai aka ƙwanƙwasa ƙofa ita ce ta bada damar shigowa.Ƴar aiki ce,cikin Yaren turanci ta ce “oga na falo yana jiran ku ” tana gama faɗa ta fice. After dress na ɗauko na ɗora a sama kafin mu fita falon,Oga na zaune ya hakimce fuskar nan kicin-cikin kamar za ta tsage. Na sunne kai tare da samun wuri na ja na tsaya ganin irin mugun kallon da yake jefo min. “Zuly kin ga saboda ke ina shirin samun matsala da Boss ? Ta ya za ki kawo wacce kika san za ta kawo mana cikas? Faɗa min wace shawara kuka yanke yanzu?” “So take mu koma Kamaru,kuma ni ma na ga kamar hakan zai fi.In mun je can za ta fi samun damar yin tunani in tana ganin Abbanta ” Zuly ta faɗa ,ban san dalilin da yasa ta kawo Abbana a cikin wannan lamari ba. Oga ya ce “babu matsala za ku iya komawa,amma ki bari har zuwa gobe don yanzu haka an tsinci gawar mijinki ƴan sanda sun soma yin bincike.Kin ga in suka biyo ta kanki za su samu ba ki ma ƙasar,kuma in kin je ki nuna cewa labarin mutuwar ne ya maido da ke” “Kenan in haka ne sai dai mu bi jirgi ba ta madubi ba?” Zulyn ta faɗa sam babu wata damuwa a tattare da ita. Oga ya miƙe tsaye ya ce “eh hakan za a yi,na riga da na tsara komai” yana gama faɗa ya murza zobensa nan take ya ɓace ɓat. A ɗakin Zuly na kwana, washegari kuma tun da safe muka shirya tsaf zuwa aeroport,jirgi ne na musamman wanda bai da buƙatar sai mun nuna wasu takardu.Tamkar zan fita daga wuta haka nake ji,don na lashi takobin da zarar mun sauka Kamaru ko ƙasa da sama za su haɗe ba zan ƙara shiga sabgar Zuly ba na fita daga family kenan. Jirginmu na sauka ƴan sanda suka tarbe mu,nan na ga ikon Allah yadda Zuly ke kuka idonta duk sun yi ja sai wani rangaji take kamar za ta faɗi sai na taro ta .Daga nan police station muka wuce aka yi mata tambayoyi kafin ta nemi tana son ganin gawar mijinta. Duk yadda ta so mu je tare zillewa na yi na tafi can asibiti,a zaune na tarar da Ummah tana kuka.Tana ganina ta taso ta ce “ina kika shiga tun jiya muna nemanki a waya ba mu samu ba? Auta kuma ta ce min kuna kwance tsakar dare kika fita kika bar gidan,ina ne kika je?” “Wurin aiki mana Ummah,amma ai gani na zo.Ya jikin Abba?” Hawaye ta goge da mayafinta kafin ta ce “ɗazun nan aka kawo masa kwara-kwara wacce zai dinga yin tafiya kawai sai kwacaaa na ji ya faɗi.Likitoci sun ce aikin da aka yi masa a ƙafa ya lalace sannan ya samu shanyewar ɓarin jikiii ” ta fashe da wani kuka mai tsuma rai ,nan take jikina ya ɗau rawa.Ban ida rikicewa ba sai da na je na ga yadda Abba ya koma ,kukan ni ma na dinga taya Ummah ga likitoci sai rubuta sabbin magani suke. Cikin wuni guda suka rikita mana lissafi don kuwa an kai gaɓar da kuɗin hannun Ummah sun ida dama oga ne ya bata su. Wuraren sallar magarib kuma babban likitan ya fito da wani zance,“kuɗin gadonku sun ida ku je ku zuba wasu kafin nan da ƙarfe goma na dare ” Ummah ta dube ni ta ce “ Lubna ki je ki biya,ko har yanzu ba a baki ko dala ba sai aikin?” a cikin kalamanta sai nake jin kamar har da ɓacin rai,wato gani take na ɓoye kuɗin ne musamman suturar da ke jikina da ke tsadadiya babu wanda zai yarda kan cewa banda kuɗi. “Bari na je na dawo” shi ne kawai abin da na faɗa kafin na fito,tafiyar ƙasa na soma yi ina tafe ina tunani har na isa gidan Zuly .A falo na tarar da ita,muka gaisa sama-sama kafin na shiga ɗaki na ɗauko wayata iphone wacce zuciyata da ruhina suka yarda da na sayar da ita na yi wa Abbana magani. Har na kai bakin ƙofar fita na ji muryar Zuly na cewa“kina tunanin kuɗin sayen magani su ne za su warkar da mahaifinki? To in dai haka ne kin makaro ” Da sauri na juya ina kallonta,ta sakar min wani murmushi tana mai kankare akaifarta. “Me kike nufi a nan?” na samu dakyar na tambaye ta zuciyata na ɗan dokawa. Ta miƙe tare da zuwa dab da ni sannan ta ce “ina nufin ko duniya za

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});