Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yunwa amma in kina ji kawai ki ci ki rage min” Inna A'i ta ce “ ai kuwa ina ji tun da a mota abin turawa ne kawai kika bamu ” tana nufin cake.Na yi dariya tare da ɗaukar wayata na soma saita app don jiya ban samu na yi ba.Ita kuwa Inna A'i hankali kwance take cin shinkafa da miyar kajinta tana santin cewa ashe ƴan ƙauye ma sun iya girki,ashe ba ta san guba ce take ciwa kanta ba. ★ Uncle Salem Tun jiya da ya rabu da zoben hannunsa yake jinsa wani iri tamkar gangar jiki babu ruhi amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya bar wa Naf ɗinsa.Tun asali zoben Inna Delu ce ta basa shi a ranar da ta sanar da shi za ta koma can maƙabarta makwancinta,sam bai san amfanin zoben ba amma yau da Nafisa ta kira shi ta sanar da shi cewa ta ga tsohuwa mai ƙusumbi kawai ya fahimci wato sirrin ganin Inna Delu da yake a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro shi ya ta'allaka ne da zoben.Suna tsaka da gudu ya cewa direban da ke jansa yayi su koma gida,cike da mamaki direban ya juyo ya dube shi sai dai babu damar tambaya don bai ma ga fuskar tambayar ba . Suna tafe yana tunanin yadda Naf za ta ɗauki wannan lamari mai kama da wahayi don gudu yake abin ya bata tsoro don ya fahimci har zuwa yanzu kamar ganin abin take a mafarki. Tunani ya soma ta yadda zai bi ya karɓe zobensa ba tare da ya ɓata mata rai ba,a haka har suka isa Company.Ya fita cike da izzarsa wacce ba kullum yake bayyanar da ita sai in yana cikin fushi ko kuma yana son gwada ƙarfin ikonsa akan wasu.Ofis ɗinsa ya nufa tare da buɗe shi,yana shiga ya duƙufa yin bincike. ★Ƙwargwam Sallah kawai ke raba ni da wayata wacce bayan na kira gida mun gaisa na shaida musu mun sauka lafiya sai na soma chating da ƙawayena a whatsapp.Hira sosai muke a group ɗinmu na ƴan makaranta har dare yayi,sam ba mu yi girki ba saboda akwai abinci shi Inna A'i ta ƙara ci kafin ta kwanta ni kuma sam ban jin yunwa saboda dama haka nake muddin ina maƙale da wayata. Kiran Uncle Salem ya shigo a lokacin ne kuma na yi alwala na canza kaya ina shirin yin shafa'i da witiri na kwanta.Na ɗauka tare da yin sallama na gaishe shi cike da girmamawa sannan ya soma tambaya ta hanya ina basa amsa har muka yi hirar yadda muka samu tarba mai kyau. Ya ɗan jan numfashi kafin ya ce “ ina kewarki Naf” Na yi ƴar dariya kafin na ce “ Uncle tun da ka fasa tafiya me zai hana ka zo nan ɗin ka yi kwana biyu?” Ya ce “ kika ce ɗaki ɗaya ne tal inda aka sauke ku” Na ce “ eh amma ai ba za a rasa wurin da za ka kwanta ba ko da hotel ne” Yayi ƴar dariya kafin ya ce “ to zan duba na gani,amma Please ki kula min da kanki sosai banda magana da maza ko da kuwa shugaban makarantar ne ban so” Na ce “ to Uncle in sha Allah,amma yaushe za ka zo?” “ Sai zuwa wani satin Naf,yanzu akwai binciken da zan yi” Kafin na basa amsa sai da na juya na dubi Inna A'i wacce ta zagaya toilet a karo na uku tun lokacin da na soma waya,ina son tambayarta lafiya amma saukar numfashin Uncle a kunnena yasa na ƙara mayar da hankali wurinsa. “ To Uncle zan fara lissafin kwanaki tun yanzu” “Faɗa min me za ki shirya min na special?” tambayar da yayi min kenan wacce na ji wani banbarakwai don har wani salo na daban amon muryarsa ke fitarwa.Kamar zai yi kuka na ji yana cewa “ Please Naf faɗa min mana kar ki ji kunyata ” hakan kuwa ya ƙara ɗaure jijiyoyina na rasa amsar da zan basa,daga can toilet na soma jiyo saurin nishin Inna A'i cikin azaba babu wani tunani na kashe kiran Uncle ɗin tare da nufar toilet ɗin ina tambayar lafiya.Ba ta bani amsa ba sai ƙofar toilet ɗin da ta buɗe ƙiiii da kanta,daga inda nake tsaye na hangi Inna A'i zaune kan wc tuni ta fita hayyacinta don da alamu gudawa ce take ta yi. Tsakaka na gani kan katanga tana saukowa kamar za ta faɗo bisa kanta da mugun sauri na ɗauki takalme ina kiran sunan Allah na kashe tsakar,ta kuwa faɗo ƙasa bindinta ya rabu da gangar jikinta da mugun sauri kuma ta bi ta ƙafafuna shuuu ta fice ta bar guntun bindin wanda sai motsi yake. Daidai nan Inna A'i ta soma kelaya amai kamar hanjinta za su faɗo,ba tare da tsantsani ko ƙyanƙyaminta ba na taimaka mata ta yi wanka ,bayan nan na sa abin kwashe shara na saka bindin tsakakar sannan na wanke toilet ɗin na rufe ƙofa.Ina zuwa tuni Inna A'i ta yi bacci,ni ma sai na raɓa gefenta na kwanta. Washegari bugun ƙofar ɗakinmu ne ya tashe mu,yadda ake jijiga ƙofar kamar za a ɓallata yasa muka kalli juna kafin na miƙe na je na buɗe,da sauri na yi baya ina kallon shugaban makarantar da mamakin abin da ya zo nema a yanzu ko ƙarfe shidda ba ta yi ba.Yadda kuma yake yi min wani kallon tsaf yasa na sha jinin jikina...... Ga mai son shiga paid group 500 ne via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Sai ya turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 6-7 Na haɗiye wasu yawu muƙut, Allah na gani ba na cikin mutane masu mugun tsoron nan don za a iya kirana jaruma kai tsaye amma kallon idon headmaster kaɗai sai da suka hautsana hanjin cikina. “ Barka da warhaka shugaba!” na samu bakina dakyar ya furta. Ya saki wani murmushi wanda kana gani ka san ba na jin daɗi ba ne kafin ya ce “ lafiya! Ina son duba toilet ne don ganin ko gyaran da aka yi yayi” ya faɗa cikin wani irin amo. Kamar na ce masa wane gyara kuma amma sai na basa wuri ya shigo,cike da girmamawa ya gaishe da Inna A'i wacce ke zaune har yanzu a inda na bar ta kafin ya shiga cikin toilet ɗin na take masa baya kuwa.Dube-dube na ga yana yi kamar mai neman wani abu amma ban kawo komai ba don na yi tunanin ko gyaran ne a gaske yake dubawa . Fuskarsa duk ta nuna alamun ƙin jin daɗi har zai fito sai kuma ya tsaya cak yana cewa “jinin mene ne can?” Inda ya nuna na duba sai na ga daidai wurin da na kashe katsakakar jiya ne,amma ai na wanke toilet ɗin sosai ta ya aka yi jinin bai fita ba. Yadda ya watso min idonsa masu matuƙar dafi yasa na soma inda-inda,“ dama...dama jiya ne da Innarmu ta shiga ta ga tsakaka...” da sauri ya katse ni “ kenan ita ce ta buge mata bindi? ” Tsuru-tsuru na yi don ina tsoron kar

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});