Chapter 37
Chapter 37
shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi. Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse. Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?” “Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu. Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba. Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha hira da Inna A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman dama tun da na dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar ɗanɗanon magani amma ban yi magana ba na ci na ƙoshi. Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ” Na ce “kin san kasuwar ne?” “Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo” “To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata sai dai sam babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page ɗin farko na soma jin kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya taɓa faruwa da ni,da na tsananta tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe saitin goshina da ya soma tsira min,ba tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi niyya ba. Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman wani abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar halitta,har tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci ba kuma na samo amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban kuma ɗauki lokaci ba na tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i tana ta sauri yayin da wata matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan rabin kurwar Inna A'i na hannunta. Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi) Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna ina kiran sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu alamunta,daidai nan na tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa da ni. Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana kakarin mutuwa jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki Innarmu?” Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun kifi na ci shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu” Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai kifin.Tsam na miƙe tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin rai,ni kaina ban san wa nuna min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata hanya har na isa.Allon sanarwar na duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada hakan ya fi shuren masaki amma na kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye numfashina na shirin tsinkewa. Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni kaina banda shi. In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa. 30 Janairu 2025 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38