Chapter 30
Chapter 30
kuma mai yin magana ni vice headmaster,wannan kuma vice principal ya nuna ɗayan namiji ,daga ƙarshe sai wannan kuma ita ce Grand Maa mai makarantar ce ofishinta shine dogon nan mai jan penti in kuna da wata matsala ko wani abu da ya shige muku duhu ita ce za ku je ku yi wa magana” bayan duk ya gama nasa jawaban su ma ɗaya bayan ɗaya suka yi nasu kafin su faɗa mana fatansu da kuma tsarin makarantar wanda tun da nake ban taɓa jin irinsu ba amma haka na ja bakina na yi shuru. Bayan an gama meeting sai wasu matasa suka shigo suka soma rabon coffe mai shegen ƙamshi.Ana bani na karɓa ina kallon ruwan coffe ɗin waɗanda a tsakiya aka shatin zuciya,na dubi na maƙwabciyata na ga ita ma nata haka yake. Na yi shuru ina tunanin ko sai yaushe zan fara soyayya oho. “Madam Nafisa ” Muryar headmaster ta katse min tunanin na ɗago muka haɗa ido,ya sakar min murmushi kafin ya ɗaga kofin hannunsa kamar yadda Turawa ke yi mai nufin Bismillah. Na ɗan murmusa kafin na soma kurɓa ina ganin lokacin da ya saki murmushi ,a baki coffe ɗin har ya fi daɗi kan kyawunsa a ido. Bayan mun gama sha ne aka rabawa kowa ajin da zai koya ,sai kuma duk muka miƙe Grand Maa sai ƙara jadadda mana take gobe tun ƙarfe bakwai na safe kowane malami ya tsaya bakin ƙofar ajinsa. Muna fitowa na cewa wacce muka zauna kusa da juna,“mene ne sunanki?” “Adama,ke kuma fa?” “Ni kuma Nafisa”na bata amsa nan muka so yin masayen lambobi sai dai ni na bar wayata can gida tana caji a dole ni na bata tawa na ce sai ta ɗago min hannu. Ina zuwa bakin ƙofar ɗakina sai na tarar da shi a rufe.Sai na zauna kan ƴar matakalar da aka yi bakin ƙofa na tsaya jiran Inna A'i don babu tantama gidan headmaster ta je.Ni kaɗai ce a wurin amma haka nake jin ana magana kusa da ni irin sosai ɗin nan,da na waiga ko ina kuma babu wanda na gani.Shuru na yi ina tunanin ko dai kunnuwana ne amma abin mamaki sai na ji ana dariya,da sauri na dubi inda sautin ke fitowa wani ɗan rame na gani irin na gidan tururuwa tabbas a ciki nake jiyo sautin amma sai aka yi tsit na wani lokaci. Ni kuwa da son jin ƙwaƙwaf na duƙa tare da kai kunnena ƙasa ina saurara,ƙafafun mutum na gani tsaye kusa da ni.Da sauri na tashi sai na ga headmaster ne,yayi min kallon nan nasa kafin ya ce “me kike yi haka a waje?” Na ƙaƙalo murmushin yaƙe na ce “na zo na tarar Innarmu ba ta nan ne shine na tsaya jira har ta dawo” “Kuma kin yarda za ta dawo ɗin?” ya jefo min tambayar wata iri,ni kuma da yake ba wani damuwa na yi ba na ce masa “ eh za ta dawo ai ita ce za ta zauna da ni har mu koma” “Hum!” ya ja wani ƙyaci kafin yasa key ya buɗe min ɗaki,na yi masa godiya tare da shigewa ciki. Har zan shiga wanka na soma jin ƙaurin ƙonewar abinci,da sauri na shiga kitchen na kashe gas ɗin .Bayan na yi wanka na fito na yi mamakin da ban ga Inna A'i ta dawo ba,wayata na cire a caji na duba sai na ga Uncle ya kira ni sai na mayar masa ya ɗauka.Muka fara gaisawa kafin na ce “ Uncle ina ne za ka je na ji kamar kana driving?” “Wurinki mana ko ba ki so?” Cike da murna na ce “ wai Uncle da gaske?“ “ Na taɓa yi miki ƙarya? Ke dai kawai ki shirya tarbena don na kusa zuwa sai an na iso” yana gama faɗa ya kashe,ni kuma cike da zumuɗi na miƙe na soma gyara ɗakin na shiga kitchen na fara duba abubuwan da duk muka zo da su na haɗa masa lemun zoɓo na jona ƴar ƙaramar frigine ɗin da ke nan a kitchen na saka. Haka na zauna na yi ta yin abubuwan da na san yana so kafin isowarsa.Aikin da na duƙufa shi ya mantar da ni wani cewa Inna A'i ta fita,haka na wuni ni ɗaya sai dab magrib ne Uncle Salem ya kira ni ga shi ya iso ni na je na tarbo shi can fara isa makaranta.Gidan gaba na shiga ya tuƙo motar yayi parking nata daidai ɗakina,nasa sabon key ɗin da headmaster ya bani na buɗe sannan muka shiga .A gajiye yake wannan yasa ya soma shiga wanka,ko da ya fito tuni an soma kiran sallah da sauri na ɗauke idona ganin ya fito babu riga daga shi sai farin towel ya ɗaura a ƙugu. A ɗan daburce na ce “ Uncle ga kayan buɗa bakinka” Bai ce komai ba sai gefen katifa da ya zauna haka nan ya ƙi saka kayan,da kansa ya zuba zoɓon don dai ni ba zan juri kallonsa a haka ba na shige toilet na ɗauro alwala . Da zan fito sai da na ɗan ziro kai don ganin ko ya saka riga sai dai karaf muka haɗa ido da shi,yana nan kuma a inda na barsa.Ya sakar min murmushi yayin da ni kuma na fito cike da kunya,kaina sunkuye na ɗauki dadduma na soma yin sallah ko kafin na gama ya canza kaya ,a nan ɗaki shi ma yayi sallah gefena kan nasa daddumar. Hannuna ya kamo da nake ta yin Azkhar ɗin yamma da ban samu na yi bayan sallar asar ba.Wani irin sanyi ne nake ji yana ratsa ni ga tuwon tafin hannunsa sai wani matse min nawa yake . “ An gama yi wa Uncle ɗin fushi?” ya tambaye ni yana murmushi mai sauti. Na ce “ ni ban yi fushi ba” “ Kalle ni” ya faɗa ,a hankali na dube shi ɗin idonmu ya sarƙe cikin na juna ina son kawar da kai amma tamkar wacce ya yi wa dabaibayi na kasa.A hankali na soma sauke ajiyar zuciya ,tsawon lokaci muna a haka kafin ya buƙaci in zuba abin da na dafa mu ci.Jiki duk a sanyaye na zuba muna ci muna aukin kallon juna har muka gama,ana kiran sallar isha'i na miƙe don gabatarwa amma ya katse ni “je ki yi ɗahara ki sake alwala” Ban musa masa ba don ba ya daga cikin halayena yin gardama a gare shi.Da mamakina kuwa da na shiga toilet alwalata ta karye iya ɗan kusanci da muka samu kawai,amma sam ban kawo shi wai don wannan niyyar yasa ya ce na je na sake alwala shi yasa ko da na fito ban wani ji kunyarsa ba na haye dadduma,shi ma sai da ya sake yin wata alwala kafin ya yi sallah. Hira muka soma yana tambaya ta meeting ina basa amsa cike da sakewar fuska kafin na soma jin cikina na yin ciwo,tun ina daurewa har na kasa. “ Je ki kwanta” cewar Uncle ,ina cije leɓe na haye katifa tare da yin rairan ina duban sama dafe da cikina. Jakar da ya zo da ita ya buɗe sannan ya ɗauko wasu kwalabe yayi wani haɗi cikin kofi ,kafin ya cika bakinsa da ruwan ya zo ya ɗora shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38