Chapter 14
Chapter 14
ku yawace babu asibitin da za ta iya warkar da cutar mahaifinki,ke ce maganinsa in kina so ya warke dole ki bai wa Boss haɗin kai” tana gama faɗa ta bar ni nan tsaye.Na jima cikin shock kafin na fice,wajen wani mai sayar da wayoyi na je na karɓi kuɗi tare da bar masa wayata jingina. Ko da na isa asibiti na tarar ana yi wa Ummah tijara,haka dai na biya kuɗin gado da kuma na sauran maganin da ba a siya ba. Na yi tunanin na kawo ƙarshen matsalar duk da kuwa furucin Zuly bai bar kwanyata ba,ashe nan duk shimfiɗa ce aka yi min mamakin na gaba. Ƙanwata auta ita ce ta kawo mana abincin dare mun ɗan taɓa hira kafin ta koma gida ni kuma na yanke shawara zan zauna tare da Ummah. Dare ya tsala bayan duk kowa ya kwanta,na ji motsin buɗe ƙofa wanda yayi daidai da farkawata daga bacci sai dai tamkar gawa haka na sandare na kasa motsi.A gabana oga da Zuly suka shigo ɗakin suka yi tsaye kai ga Abba,can kuma Boss ya bayyana su biyu suka danne Abba yayin da shi kuma yayi masa wata allura wacce ta sa shi soma yin ihu da kururuwa yana kiran zai mutu su tausaya masa su bar cutar da shi,cikin ɗacin rai Boss ya ce “ƴarka ce duk ta ja maka masifa ba za mu taɓa barinka ƙalau ba sai ranar da ta amince da ƙudirina” Ina jin lokacin da Abba ya soma magana cikin azaba,“Lubnata ba za ta taɓa aikata abin da kuke so ba,na gwammaci na dawwama cikin wannan masifar kan na ga ta gurɓata rayuwart...” Zuly ce ta ɗauke Abbana da wani mari wanda hakan yasa sauran maganar ta maƙale masa,suna gamawa suka fice sai kuma a lokacin kawai jijiyoyin jikina suka ci gaba da yin aiki. Dakyar na iya tashi na je na yi tsaye gaban Abba ,idonsa ya zuba min yana kuka.Bakinsa ya juye ba zai iya yin magana ba,amma a haka ina fahimtar abin da yake son sanar da ni.Na faɗa jikinsa na saki wani irin kuka mai cin rai wanda yayi sanadiyar tashin Ummah ita ma sai ta soma yin kukan don ta yi tunanin mutuwa yayi. Sai da likitoci ne suka shigo suka tabbatar mata da ransa,allura bacci suka yi masa saboda wani irin abu da ya soma yi kamar mai cutar hauka. Jikin Ummah na je na ƙanƙame ta ina mai ci gaba da yin kuka yayin da ita kuma ta soma rarrashina tare da kwantar min da hankali Abba zai samu lafiya. Da gari yayi haske suka sake shigowa suka duba Abba,suka ce jikinsa ya ƙara mutuwa da buƙatar a yi masa gashin ƙashi .Haka suka tura gadonsa aka shiga da shi wani ɗaki,ni da Ummah iya bakin ƙofa kawai muka tsaya.Daga nan muna jin yadda Abba ke ƙwallowa yana ihu da ransa. Sosai kururuwarsa ke taɓa min zuciya ,sai nake ganin duk laifina ne.A haka dai na fita don zuwa mu yi cinikin wayata da na baro jiya,nan ɗin ma wata masifar na tarar shagon wayoyi ya ƙone ƙurmus sai gawawarkin wayoyin ga su nan jere ringis duk sun ƙone.Yana ganina ya ƙara ƙaimin kuka,ni ce na basa haƙuri don da ace ya san ta dalilina ne yayi asarar nan ƙila kotu ce za ta raba mu. Idona sun rufe,babu komai cikinsu sai ɓacin rai.Gidan Zuly na nufa don so nake a yita ta ƙare,ko da na isa na tarar da ita a zaune tana karɓar ta'aziyar mijinta ga mutane duk sun cika falon.Ɗakin da aka ware domin ni na shiga bayan na yi mata alama da ido ina son ganinta,sai dai ina shiga na tarar da Boss a hakimce kan gado yana murmushi... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [04/04 11:00] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 08 A lokacin da na ga Boss kwance kan bed sam babu sutura a jikinsa,wani irin bugawa zuciyata ta yi sai dai na kasa ɗaga ƙafata ballantana na koma baya na fita daga ɗakin. Cike da shaƙiyanci yake cewa “ki gama gujegujenki ni ɗin nan ne zan raba ki da budurcinki,in kuma kin fi ƙaunarsa kan mahaifinki ai shi kenan” yana gama faɗar haka ya ɓata kamar walƙiya.Na ja ajiyar zuciya,abin da na fahimta a family su komai nasu ba su yinsa dole sai ta daɗin rai wannan dalilin yasa ko da wasa ba su saka ƙarfi ba wurin baiwa Boss ni ba. Ina nan tsaye ina saka wasiƙar jaki Zuly ta turo ƙofa ta shigo,kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai tare da yin gaba.Ni kuma na take mata baya ina mai kiran sunanta,sai da ta cire zumbulen hijabinta sannan ta juyo ta fuskance ni ta ce “Luby ban san wace irin zuciya ce da ke ba marar tausayi,duk halin da Abbanki yake ciki kin kasa haƙura ki bada kai bori ya hau.Me za ki yi da shi budurcin? Ina ce duk don da dai ki kai shi ne gidan mijinki,to ki sani a family ba a auren bare.Duk wanda ko wacce ta shigo babu aure to dole ne ya zaɓi abokin rayuwa cikin ƴan ƙungiya,kuma ina ce ai a gabansu za a yi komai ba za ki samu matsala da mijinki ba tun da ya san komai” Tamkar mai cutar dundumi haka na ji a lokacin,sai kuma na fahimci ba ƙaramar ƙungiyar asiri ce wannan ba wacce ta ɓoye sirrika masu yawa sai a sannu ne za ka dinga ganinsu suna fitowa. Ban kai ga cewa komai ba Zuly ta ƙara da “kawai ki amince ita ce shawara da zan baki” Idona wani irin raɗaɗi na ji suna yi min kamar an watsa barkono ciki,maƙoshina ya bushe ƙamas dakyar na iya tattaro yawu na haɗiye kafin na ce “ban gane ba zan iya auren wani ba? Zulaihat wai wannan ɗin duk mene ne? Wane irin dokoki ne wannan? To ki tsaya ki ji in faɗa miki daga yau a yanzu da nake faɗa miki na fita daga family har abada,ku je can ku yi tsafinku kuɗi ne dai to ban so ku riƙe abinku.Kuma wallahi kika yi ƙoƙarin ɓullo min da wani sharri to sai na je har ofishin ƴansanda na shaida musu ke ce kika kashe mijinki” ina gama faɗar haka ban tsaya ɓata wani lokacina ba na fita na bar ta cike da shock. Duk a tunanina shikenan na huta na jefar da ɗan mangoro na huta da ƙuda sai dai ina isa asibiti na tarar da tashin hankalin da ban taɓa zato ba. Jikin Abba ya rikice sai aman jini yake dunƙule-dunƙule,likitoci sun duƙufa wajen bincike amma result bai nuna alamun wata cuta ba ga jinin Abba sai ƙasa yake yi ga shi banda kuɗi,jinin kuma sai an saya. Duk da yana cikin firgici da gushewar hankali bai hana shi isar min saƙon kar na saki na bayar da mutumcina ba.Banda kuka babu abin da nake yi,ji nake kamar na je na cewa Zuly na amince sai dai fa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38