Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 36

Chapter 36

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

” ta faɗa . Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“ “Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar wuƙa da kuma baƙin zare. Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida. Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya. Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na ce “wai Granny Mamar Daddyna?” Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki” “Yanzu mafarki ne nake yi kenan?” “Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ” “Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da sauri na ware idona tare da yaye abin rufa. “Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska. Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin Ayodele sai ya tuntuɓe ni)” “Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba. Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan. A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta. Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na fito na yi tsaye. Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani fuska ba sai wani cijewa take. A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji sunansa ba?” “Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi. “Mene sunanka?” na tambaye shi. “Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste ɗin. Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?” “Eh Madam ” ya bani amsa. Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa. Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa . Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta. “Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta . “Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin. Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo. Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita ba?” “Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi. Bayan sun

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});