Chapter 19
Chapter 19
lokacin baya shi ma ba zan taɓa mata wannan mummunar ranar ba. Yawun bakina ne na ji sun fara taruwa da kansu kafin su soma ɗiga suna sauka kanta tamkar ana zubar da ruwan pampo ko kuma ana yayyafi.Zafin hucinta da fitar numfashinta shi ya cika wurin tamkar wacce ake zarar ranta,ƙila shi ya jawo hankalin Aliya ta fito daga can ɓangaren ta zo nan. “Ƙwayar cutar BAƘIN RUHI,Haule ki ja baya mana contact da ke yana iya haifar da tsayawar numfashinta” Aliya ta faɗa tana mai jawo ni baya,sai a lokacin na ji wani irin raɗaɗi a ƙafata daidai wurin da ta ɗora yatsun hannunta da na kai duba wurin sai na ga tamkar an zuba min acid ne tuni ya wani kumburo ga wata uwar azaba da nake ji. Na yi baya na samu kujera na zauna,yayin da Aliya kuma ta soma juya hannunta mai ɗauke da ƙarfin iko na power nan take ya kawo haske tare da bayyanar da wani dunƙulalen haske sai ta cillawa wannan mai cikin shi sai ya zagaye ta sai a lokacin ta nufo ni ta tsuguna ta kamo ƙafata. Hankalinta na ga duk ya tashi,ni kuma na ce “kar ki damu zan warke hakan ya taɓa faruwa da ni ai.Amma me yasa kika jefa mata wannan hasken?” “Ɗaure ta ne na yi ta yadda ba za ta iya motsawa ba,haka shi ma dafin jikinta zai tsaya da aiki don yana dab da raba ta da rayuwarta.Yanzu dai bari na naɗe miki ƙafarki,sai mu tattauna yadda za a warkar da wannan baiwar Allah ” Wani tissu ta samu ta ɗaure min ƙafa,na tashi tsaye kan ƙafafuna ina kallon mai cikin wacce ta zama kamar gumki ta kasa motsi. “Mene ne ke damunta Aliya?” “Ya za a yi mu samo maganin cutarta ita ce tambayar da ya dace ki yi Haule,kar ki bari kuskuren da kika yi baya ya sake maimatuwa ” ina jin furucin da Aliya ta yi sai na yi saurin dubanta,ta jinjina kai kafin ta ce “na san antynki ai,kar kuma ki tambaye ni ta yaya yanzu mafita za mu nemo kuma ke ce za ki jagoranci tafiyar” Na ja wani gwabron numfashi kafin na ce,“dole sai na samu labarin mafarin abin da ya haifar mata da wannan cutar” Shiru Aliya ta yi kafin ta ce “in haka ne muna da buƙatar madubi ko da ɗan guntu ne” Ban kai ga yin magana ba aka shigo,Lubna ce da sauri na nufe ta sanin kullum tana yawo da madubi a jaka. “Yawwa don Allah ki bamu aron madubinki” na faɗa . Inda mai cikin take a durƙushe ta duba kafin ta zuge zip ɗin jakarta ta miƙo min,sai na je kusan Aliya na tambaye ta “ya za a yi yanzu?” “Ki je saitin idonta ki haska madubin za ta yi magana sai mu ji” cewar Aliya . Dukka mu ukun muka yi tsaye,suka saka ni a tsakiya yayin da na daidaita madubin ita kuma Aliya ta yi amfani do powerta ta ɗago kanta sai a lokacin na yi mata magana “Wace ce ke? Mene ne dalilin shigarki wannan halin?” “Sunana Meelat,ƴa ga masu matsakaicin hali,ba mu da kuɗi amma muna da rufin asiri.Na yi karatuna a makarantun gwamnati har Allah yasa na kai matakin University,ina shekara ta biyu yanzu haka.Tun zuwana can na ga yadda rayuwar jami'a take yadda ake challenge ɗin sutura da kuma wayoyi.To dama tun can farko ina sha'awar rayuwar luxery,ina da babban burin shiga mota ,zuwa gidajen cin abinci na manyan mutane da sauransu.Kwatsam wata rana na fito daga jami'a zan je wurin gyaran gashi wata rantsatsar mota ta parker a gabana,a hankali ya sauke madubin motarsa wanda yake baƙi ƙirin ɗin nan.Wani babban mutum ne na gani cikin shiga ta alfarma,fari ne shi tasss mai kyau mai gayu wannan yasa ban wani ja aji ba da ya nemi ya rage min hanya.Sam ban yi duba da ya haife ni ba ko kuma kusan yin jika da ni ba,abin da ke gabana kawai kuɗi.Shi ya biya kuɗin da aka gyara min gashi da aka gama min kuma na kira shi ya zo ya ɗauke ni kamar yadda ya buƙata ya bani lambar wayarsa.Kafin ya mayar da ni can jami'a sai da yayi min shopping kuma ya faɗa min ƙudirinsa na sona yake,nan fa muka fara soyayya ko sau ɗaya bai taɓa kai hannunsa jikina ba tsawon watanni uku muna tare kuma komai nake so yana yi min.Ni da ƙawayena mun mayar da shi atm ɗinmu,a takaice dai sai da muka kwashe wata biyar kafin ya gayyace ni gidansa ya ce yana yin birthday na zo mu yanka cake sai na koma sannan kuma sai na duba gidan in yayi min nan zai ajiye ni in mun yi aure .Haka na je can gidan nasa mai kamar aljannar duniya inda ake parker motoci ma kawai abin kallo sannan akwai motoci iri-,kamar baƙauya haka na yi ta kallon har muka wuce can falonsa ashe ban ga komai ba don cikin ya fi haɗuwa.Ya nuna min kujera ya ce na zauna zai yi sallah ya dawo.Duk da a lokacin bai wuce ƙarfe biyar na yamma ba amma ban tambaye shi sallar mece ce zai yi ba kawai abin da na ɗauka mutum ne mai addini. Daga inda nake a zaune ina ɗan jin sautin muryarsa yana karatu,amma dai ba na Alkur'ani ba ne cikin wani yare ne yake yinsa.Kamar minti goma haka sai ya fito jikinsa sharkaf da gumi har goshinsa na ɗigar da zufa,hankali a ɗan tashe yake cewa “babyna zo! Taso zuwa gare ni, please ina son ki yi min wani taimako ni kuma na yi miki alƙawari zan mallaka miki key ɗin mota da gida da duk abin da kike so.Lokacin da yayi wannan furucin na yi tunanin sex ne zai nema wurina sai duk ban damu ba don na taɓa yin aure ballantana na ji tsoron rasa budurci kuma a shirye nake na biya masa buƙatarsa duba da hidimar da yake yi min,nan take na ce masa na amince in dai gaske zai ban motar.Sai ya kama hannuna muka shiga ɗakin nan da ya fito,babu komai a ciki sai wani ƙaton akwati a tsakiya yana buɗe shi na yi tsalle na ja da baya . Ba komai ne cikin akwatin nan ba sai gawar wata mata har ta bushe da alamu ta jima da mutuwa.Jikina ya ɗau kyarma,sai ya soma kwantar min da hankali yana cewa “kar ki wani damu baby kawai ciki za ki shiga kwanta na tsawon minti ɗaya kacal sai ki fito. Soyayyata da abun duniya yasa na yarda na kwanta a tsorace,kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa babu jimawa na fito sai ya bani maƙudan kuɗi waɗanda ni kaina ban san yawansu ba kuma ya mallaka min ɗaya daga cikin motocinsa da kuma gida.Tun bayan da na koma can in na kira shi wayarsa ba ta shiga,da farko ban damu ba sai satin da ya wuce da na soma ganin cikina na kumbura yana zama ƙato in kuma na yi tari sai jini yayi ta ɓulɓulowa na yi yawan asibiti har na gaji amma likitoci ba su gano abin da ke damuna ba.Har gidansa na je amma yana rufe da ɗan kwaɗo ,maƙwabtansa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38