Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,248 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [06/03 16:23] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ Happy sallah my dear fans, Allah karɓi ibadunmu Amen !!! *Wannan labari da da kaso saba'in ya faru da gaske,don haka don Allah kar wacce ta ji haushina yayin ganin abin da ya saɓawa ra'ayi* 01 “Kowanne ahali da nasa sirrin,haka kowanne ahali da nasu tabo ko ƙaddara ko kuma dai wani al'amari wanda suke ɓoye wa.Motar tsautsayi ce ta ja ni na bankaɗe mayafin da ya luluɓe baƙin sirrin gidanmu wanda silar haka yasa na baro ahalina domin tseratar da da gajiyayen ruhina,wanda aka raunata shi ta sigogi da dama” na yi shuru saboda hawayen da suka cika min ido.Ita kuwa Lubna banda aukin kallona babu abin da take yi,da dukkan alamu ta ƙagu ta ji ainahin labarin nawa. Na ɗan yi murmushi mai ciwo wanda ya bai wa ƙwallar da ta taru a idona sa'ar zubowa kan kumatuna,na ci gaba da cewa “ Gidanmu irin family house ne wanda za ki kaf yayyu da ƙannai a ciki,mu biyar ne mahaifiyarmu ta haifa,mu biyu ne mata ukun maza.Anty Aliya ce babba,sai Aliyu,sannan Fahad,sai ni sannan autanmu Haidar.Sannan akwai ƴaƴan kawunana su ma duk da matansu da ƴaƴansu,duk yawanmu a tukunya guda ake yi mana girki haka muka taso muka ga iyayenmu na yi.Sannan in za a ci abinci ma su iyayenmu maza a tare suke ci haka ma matan,mu kuma ana banbanta wa ƴan sa'inni ɗaya ake zuba mana a cikin faranti guda da wannan ne na yi sabo da cousin/cousine ɗita Hassana wacce ƴan biyu ne su ɗaya ta rasu a wani dare bayan mun gama cin abinci.Ni da Hassana akwai wani abu da ke faruwa cikin ahalinmu da yake mugun ɗaure mana kai yake kuma ci mamu tuwo a ƙwarya.Ba zan manta wata rana mun je ɗebo ruwa a ƙatuwar rijiyar da ke can bayan ɗakunanmu Hassana ta dube ni da kyau ta ce “Haule har yanzu mutuwar Husseina ta ƙi fita raina , kowane dare sai na yi mafarkinta tana kuka tana ce min na cece ta,amma jiya sai take ban shawara wai na gudu na bar gida ban san dalili ba” “Kawai don kin san abin a rai ne shi yasa, sannan duba da cewa ku ƴan biyu ne ƙila shi yasa kika kasa fidda abin a kanki amma kusan shekara fa yanzu da ta rasu” shi ne abin da na faɗa mata a wancan lokacin amma sai ta girgiza kai ta ce “a'a na fi tunanin dai wani abun ne yasa take zuwar min a mafarki, sannan kar ki manta ko sau ɗaya ba ta take rana sai ta kawo min ziyara tana maimaita abu guda na cece ta,amma na jiya ya banbanta kawai ta ce na gudu” ban kai ga ce mata komai ba goggo Lami wacce ta kasance mahaifiyar Hassana ta iso bakin rijiyar,sam ba mu yi tunanin ta ji abin da muke cewa ba don ba ta nuna alamu ba kawai dai ta ɗauki bokitin da muka cika da ruwa ta tafi.To mu ma sai muka watsar da zancen muka ci gaba da aikinmu,bayan mun gama sai muka koma can cikin gida. Wani irin kallo na ga Innarmu na bi na da shi,tun ban damu ba har na soma tsarguwa sai kawai na bar inda take don kaucewa kallon.Da dare bayan duk mun yi sallar isha'i muka fito cin abinci,tamkar wasu ƴan biki haka duk muka yi kashi-kashi muka kewaya kowa da faratinsu muna ci muna santin girkin iyayen namu har muka gama sai aka soma yin gatana har sai da dare ya tsala sannan duk muka rabu. Ina shiga ɗakinmu har na kwanta na ji muryar Innarmu ta kira sunana cikin wani sauti “Haule?” sai da gabana ya faɗi amma na daure na ce “na'am Innarmu” “Zo nan” ta faɗa ,sai na tashi na je kusa da gadon ƙarfenta mai rumfa na yi tsaye tare da sunne kai saboda har zuwa yanzu irin kallon nan ne na ga tana yi min. “Kar na sake jin kin yi zancen nan ke da Hassana ,kin ji ko ba ki ji ba?” “Wane zance Innarmu?” na tambaye ta don ni har ga Allah na manta. “Na mutuwar Husseina,ki je ki kwanta” shi ne abin da ta ce,na je na kwanta ɗin sai dai fa sam ba baccin na yi ba kamar yadda na so yi tun farko. Ido kawai na lumshe,ina jin lokacin da anty Aliya ta zo ta

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});