Chapter 25
Chapter 25
Daddy ya ce wani abu tuni tv ɗin da ke manne jikin bango ta soma yin wata tsaga “ƙiiiii!” kafin kuma ta faɗo ga ƙasa ,sai iska kuma mai ƙarfi wacce ta haifar da fashewa ƙwan lantarki ji kake ɗuuu haskensa ya ɗauke sai labulaye suka soma tashi sama suna wulwulwul.... [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 04 A cikin duhun ɗakin ne Daddy da Uncle Salem suka hango wata mace sanye da fararen kaya wanda ko tantama babu likafani ne.A tsaye take jikin window sam ƙafafunta ba su taɓa ƙasa ba sai wani lilo suke kamar wacce aka rataye,farin gashin kanta kuwa sai yin sama yake iska na naɗa shi. Cikin muryarta wacce kana ji ka san ba ta ɗan adam ba ce ta soma yin magana,“ ko kai ko abokinka babu wanda ya isa ya dakatar da ni daga yunƙurin da nake,Yarima Abdul Hameed ban sani ba ko ka san cewa sunan Deborat ya haramta ga duk wanda yayi hijira ya bar gidansu domin guje abubuwan da allolinmu za su zartar,ka sani cewa Nafisa jaruma ce ba mu zaɓe ta ba sai da sanin za ta iya.Sannan ka godewa Allah da ya kasance aikin alkhairi ne za ta gudanar ba wai na cutar da al'umma ba,sannan kai kuma da kake ta ƙoƙarin dakatar da mu ziyartar ta ka sani akwai lokacin da maganinka ba zai yi aiki a jikinta ba don haka gara ka baiwa kanka lafiya ka bar matarka ta yi aikinta yadda ya kamata.A tunaninka hatta auren naku ba mu sani ba? Mun sani sarai saboda kai ne za ka yi jinyarta a lokacin da ta kammala aikinta na farautar azzalumai ” tana gama faɗa kawai ta bi ta window ta fita yayin da kuma komai ya dawo normal hatta hasken ƙwan lantarki rasss ya koma yana yi . Daddy da Uncle Salem sai suka fara ƴar kallon-kallon ba tare da sun cewa juna komai ba. Can Daddy ya kasa yin shuru ya ce “ aboki ka yarda da fatalwa?” “ Na yarda mana saboda ni ma ita ce ta raine ni” Uncle Salem ya basa amsa . “ Ban gane ba” “ Eh kamar yadda na faɗa ma ni kaina ban san iyayena ba domin a titi aka tsince ni to Inna Delu ta raine ni ta bani dukkan tarbiyya da kuma kulawa ta uwa,sai bayan na mallaki hankalin kaina ne ta sanar da ni ita wace ce saboda za ta koma makwancinta“ Daddy ya ce “ wai kana nufin dama Inna fatalwa ce?” “ Eh sosai ! Bari na je na duba na ga ko Naf ta tashi” ya faɗa tare da miƙewa ya fita ,hankalinsa da tunaninsa na kan fatalwar Deborat wacce kusan duk dare Inna Delu na yi masa gatanarta. Ko da ya shiga ɗaki ya tarar Nafisa na ta yin baccin gajiya ,ya dubi agogo ya ga lokaci sai tafiya yake ga shi kuma ba ta yi sallah ba.Sam bai son ya tashe ta amma sanin sallar asar ma nada ƙurarren lokaci yasa ya soma shafar fuskarta da tafin hannunsa mai taushi da sanyi. Cikin bacci na soma jin sanyi na ratsa min kumatu,ga taushi kamar auduga.A hankali na ware idona na sauke su kan kyakkyawar fuskarsa,ban ida warkatsewa ba ya ce “ lokacin sallah Naf” Jin ya ambaci sallah na yi saurin tashi hankali tashe don na tsani na makara,ya ɗan ja da baya yana mai ci gaba da kallona kafin kuma ya fita.Ni ma fitowa na yi na wuce can sashenmu sai da na fara gabatar da sallar sannan na yi wanka na saka riga doguwa marar hannu na ɗaura kallabinta sannan na fita. Yunwa nake ji hakan yasa direct kitchen na shiga,Ammy ce da A'i mai aiki ke ta faman yin girki da dukkan alamu yau sarautar ta Daddy ta motsa shi yasa Ammy ke aikin da kanta. “Yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,A'i ta yi dariya ta ce “ oh shagwaɓarki Nafisa ko auta albarka ” Ammy ta ce “ bar ni da ita dai ta ci gaba da sakalcin in ta je can ƙauyen ai na ga wacce za ta yi wa” Kamar wacce suka yi wa allurar zaburar wa kuwa haka na wani kwanto jikin A'i mai aiki wacce nake kira da Inna na ce “ ai tare da Innarmu zan tafi ita za ta dinga kula da ni,kafin na dawo ta yi min girki mai daɗi” A'i ta washe baki don sosai take jin daɗin yadda Nafisa ta ɗauke ta tamkar Kakarta sam ba ta nuna cewa ita ke ƙasa gare ta,haka kuma ita ce ta raine ta tun tana cikin tsumman goyo ko aiki za ta yi haka take goye ta in kuma ka ga sun rabu to Uncle Salem ne ke gidan. “ Ki ma cire wannan a ranki don Inna A'i ba za ta bi ki ba” cewar Ammy tana mai zuba min kunun gyaɗa a kofi. Na ce “ wai Innarmu ba za ki je ba?” A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin daɗi na ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne. Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina kallonsa .Sanye yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda da shi . Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen tafiyata ne. Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki” sai ya zaunar da ni tare da ɗaukar kofin ya ci gaba da bani kunun har na shanye kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu wuce” Da murna na koma ɗakina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon hijabi har ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza kaya Naf ” da mamaki na dube shi,ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba. Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya ɓata rai yana kallon ƙirjina,sai na turo baki na koma ɗaki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38