Chapter 8
Chapter 8
ya soma yi min tambayoyi ina basa amsa daidai da abin da na sani. Ya yi wani murmushi da ya ƙara bayyana muninsa kafin ya ce “Zuly ƙawarki nada kaifin basira kam,ina ga ita ya kamata mu baiwa kujerar mai kula da baƙinmu na waje ko ya kika ce?” Ta yi wani murmushi tana mai cewa “ai kuwa ko a makaranta ita ce ta ɗaya,sannan ta saba jagorantar duk wani abu da ya shafi jagoranci ina ga babu matsala in dai ta yarda za ta yi” Sai duk suka maido dubansu gare ni,wata irin rikicewar na yi da kuma mamakin ƙarshen furucin Zulaihat wai in na yarda.To me zai hana na yarda ? Abin da na jima ina nema ɗin shekara da shekaru. “Ba ki ce komai Luby” Zulaihat ta faɗa . Muryata har rawa take na ce “na yarda mana ina so,in dai maganar turanci ce ai kin san nan na fi ƙwarewa babu wata matsala” ina gama faɗar haka sai ogan ya miƙo min wata takarda haɗi da jar biro ya ce na saka hannu a ƙasa wanda ke bada tabbacin na yarda da dukkan sharuɗan zan yi aiki a kamfanin . Hum! Haule kin san dayawa mutanenmu ƴan Afirka muna yin babban kuskure shi ne saka hannu a takardar da ba ka karanta jawaban da ta ƙumsa ba,to ni ma a lokacin haka na rabbata hannu na miƙa masa.A tare suka saki wata ajiyar zuciya mai bayyanar da tsantsar farin ciki. Sai a lokacin kuma ogan ya buɗe ƴar takardar da ke ɗauke da hotunana biyu,ɗaya ya ɗauka sannan ya buɗe wani fayil mai ɗauke da hotunan mutane dayawa sannan ya maƙala nawa tare da yi masa wani rubutu can ƙasa. Bayan ya gama sai ya dubi Zulaihat ya ce “ki kai ta wurin shopping ki tabbatar kin zaɓa mata kayan da za su fi dacewa da aikinta,sannan inda buƙata har gyaran jiki a yi mata .Kin dai fi ni yadda ya kamata na bar miki komai a hannunki,sannan zuwa gobe za ta soma aikin kuna iya tafiya” Ba mu ƙara cewa komai ba muka fito,cikin yanayin tsarguwa na ce “Zulaihat mene ne kuma na yin gyaran jiki? Halan datti gare ni irin sosai?” Ta tuntsire da dariya ta ce “in ba abinki ba ke da za ki tarben turawa in ba ki kama kanki ba kina ganin za su yarda su zuba hannun jari a kamfaninmu?” Murmushi kawai na yi na basar,daga nan gidan gyaran jiki ta kai ni cikin wata ƙatuwar inji na shiga iya kaina kawai ke waje shi ma bayan an gama wannan ɗin sai da aka saka min relax aka sa ni a tukunyar busar da gashi.Bayan mun gama komai sai ta saya min wata doguwar abaya wajen matar mai gyaran jikin,na saka sai na dawo tamkar wata balarabiya na yi kyau sosai.Daga nan gidan cin abinci muka je bayan mun cika tumbinanmu sai muka wuce mall,yadda na ga Zulaihat na jido riga da wando yasa na yi mata magana don ba zan iya saka su ba amma sai na ta saurare ni.Bayan su kuma ta saya min har da after dress da kuma sari ,wasu kayan ma ban san da irinsu ba. Na yi tunanin gida za ta kai ni amma sai ta wuce da ni gidanta,a falo muka zube ta sa masu aikinta suka kwaso tulin kayan da ta sayo min kowanne da takalminsa. Sai da aka kawo mana kayan maƙulashe muka taɓa tare da jus sannan na soma duba kayan,sai dai ban ɗauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni a nan take kuma na soma yin wani mafarki marar kan gado..... [02/04 11:31] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 05 Mafarki ne wanda sam rabon da na yi sa ina jin tun lokacin isar min da saƙon balaga.Sai da wannan ya sha banban da wancan,don wannan sarai ina ganin wanda ke tarayya da ni.Ba kowa ba ne ba sai oganmu wanda yanzu ya gama yi min interview,abin mamaki kuma a cikin mafarkin bai fi yadda yake yabona ba yana cewa “ashe Zuly ta yi gaskiya kina da taurari masu kyau masu haske,ke ɗin maƙurar ilimi ce” ban farka ba har sai bayan komai ya kammala.A hankali na buɗe idona da suka yi min nauyi,sam ni na manta ma a inda nake sai bayan na watsake ne na tuna gidan Zuly ne nake. A hankali na tashi zaune ina jin duk jikina na yi min ciwo kamar wacce aka yi wa shegen duka.Ta zo da murmushinta ta ce “ashe kin tashi? Bari na sa a haɗa miki ruwan wanka in kin gama sai ki ci abinci” Ɗan murmushin yaƙe na yi na ce “to” sai ta ƙwala kiran ƴar aikinta bayan ta zo ta faɗa mata aikin da za ta yi sai kuma ta dube ni kamar mai son tantance wani abu kafin ta ce “kayanki suna ɗakinki an jera a drower” Abun mamaki kasa yi mata muso na yi ko kuma na tambaye ta yaya na samu ɗaki a nan gidan.Ita ce ta yi min jagora na isa can ɗakin wanda tuni an haɗa min ruwan wanka a baho,kar ku ji zancen wasa a ranar nan Zuly ce ta yi min wanka tamkar wata ƴarta ni kuma na kasa yin wani kataɓus.Duk da ina tune na yi mafarki amma sam tunanina bai bani na tsarkake jikina ba,saboda controling nasa ake yi.Bayan na fito ita ce ta bani kayan da na saka,sannan aka kawo min abinci kamar yadda ta shaida min tun farko.A cikin abincin nan Allah kaɗai ya san irin kalar maganin da aka saka min amma a haka na ci,kar ku tambaye ni maganar sallah don dama can farko ni ɗin na kasance mai wasa da ita ba kullum nake cika biyar ba sai in Umma ta yi min faɗa wannan yasa ko kaɗan ban samu ƙarfin zuciyar yunƙurin yinta ba. Ina cin abinci Zuly na yi min hirar yadda aikina zai kasance a gobe da kuma yadda tsarin yake,sai kuma ta soma nuna min yadda ake yin aiki da wata ƙatuwar waya bayan nan kuma ta kira ƴan aiki biyu suka yi min tausa da wani man da aka tanada don yin tausa sai dai shi sun garwaya shi da gubar tsafinsu. Har cikin ɓargon jikina nake jin yana ratsa min ,a sannu a hankali kuma bacci ya ɗauke ni nan ɗin ma mafarki na yi gani nan a wani ɗakin taro duk turawa ne ciki ni ɗaya ce baƙar fata.Masayar turanci kawai muke yi kowanne na yaba kamfanin da yake yin aiki,bayan mun gama meeting kuma sai muka je muka yi wanka cikin swimming pool maza da mata haka duk muka shiga ciki babu wata suturar kirki.Ina farkawa wannan karon babu kowa a ɗakin sai ni ɗaya,sannan babu wani haske sosai shuru na yi ina daidaita tafiyar numfashina.Daga nan kwance na ga lokacin da wata baƙar inuwa ta fita amma ban iya tantance ta mace ce ko ta namiji. Kamar minti biyu sai ga Zuly ta shigo tare da kunna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38