Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,232 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ BONUS na book ɗin *BAƘIN RUHI* mai so ya tura 300 kafin na saki last free page 10 gobe in sha Allah ki tura kai tsaye ta wannan account ɗin 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Da zarar na saki last free page discount ɗin ya ƙare. Masu sha'awar karanta tsofin Books ɗina ku zo na yi muku discount,ga wacce ta shirya ta tuntuɓe Ni kai tsaye ta WhatsApp +22795045822 09 Dare yayi sosai wannan yasa muka jingine bayar da labarin,duk da na san akwai abubuwan da Lubna ta ɓoye wanda ba ta faɗa ba amma haka na yi shiru na samu wuri na kwanta.Ido na lumshe nan take Maheer ya bayyana cikin tunanina,zaune yake a ɗakinsa ya sha wata doguwar rigar bacci ta maza fara sol da ita.Gabanta a buɗe yake,hakan ya bani damar ganin fafaɗen ƙirjinsa mai ɗauke da suma baƙa silik ta kwanta sai sheƙi take.Duk da ban taɓa saurayi ba,amma gargasar ƙirji na ɗaya da abin da nake fatan samu a wurin mijin aurena hakan yasa na kafe gurin da ido ko ƙyaftawa ban yi. Har sai da na ji muryarsa yana cewa ,“kin ga dama kin zo” da wani mugun sauri na buɗe idona sai kuma na tashi zaune na dafe saitin zuciyata da take bugawa,sam na kasa gane shin tunaninsa ne na yi? Ko kuwa dai ban sani ba bacci ne ya ɗauke ni sai na soma mafarkinsa? Amma dai tabbas na gansa da idona sai dai irin wannan tunanin bai taɓa zuwar min ba. Cike da tsoro na ƙara kwanciya na lumshe idona zuciyata na ci gaba da matsanancin bugawa.Wannan karon jinsa na yi dab da ni har muna jin hucin juna kai kace hatta gangar jikinmu na tare da juna ne,nan kuwa iya esprit ne.A hankali na ɗaga idona na kalle shi,yadda yayi wani tsaye ƙiƙam a gabana duk ya kere ni kamar Giwa da ɗan tsako. “Yanzu kuma wannan mene ne da ka jawo ni cikin tunaninka?” na tambaye shi. Cike da shaƙiyanci yasa hannunsa mai sanyi ya wani matse haɓata tare da ɗago ta ya ce,“ni kike yi wa magana haka? Sa'anki ne ni? Wato ni ne ma na shiga tunaninki? Kin zata ban gane ba? Ke ce kika shigo tunanina,na lura tun da kika zo gidan nan idonki na kaina duk kin bi kin takura ni kin hana ni saƙat,faɗa min wa ya aiko ki?” Cike da jin haushi na sa dukkan hannuwana na tura ƙirjinsa sai dai ko gezau bai yi ba,shi ma tuni ya hassala sai ya kama hannuna ya murɗe har sai da na saki ƴar ƙara na soma fizge-fizge amma ya ƙi saki na. “Duk shegen kinibibinki ne ya jawo miki halin da kike ciki amma ko kaɗan ba ki cancanci samu wannan power ba,sam ban ga ma dalilin da yasa ƴar aike ta mallaka miki mahaɗin ƙarfin ikona b...” ban bari ya kai ƙarshen aya ba na gantsara masa cizo a ƙirji da wani mugun sauri ya sake ni tare da ja baya ,daidai nan ni kuma na tashi zaune tare da buɗe idona fayau. Saitin hannuna na duba inda ya murɗe sai na ga yayi ja sosai tamkar a zahiri ne ya riƙe ni ɗin,ƙin komawa na yi na kwanta sai na ci gaba da zama tsakiyar su Lubna da tuni sun yi bacci. Ina nan zaune na ji handle na motsi ,kafin kuma ƙofar ta buɗe kanta ƙiiiii sai dai ban ga kowa wanda ya shigo ba.Wani irin tsoro ne ya kama ni ,sai nake ganin kamar Maheer ɗin ne zai shigo a zahiri. “Haule!” na ji muryar da har na koma ga Allah ba zan taɓa mantawa da ita ba ta kira sunana cikin wani irin yanayi. Na soma waige-waige kafin na ce “Husseina? Husseina ke ce? ” ba ta bani amsa ba,sai jin wani abu na yi cikin iska ya kama hannuna yana jana sai kawai na sauko daga shimfiɗar na soma take mata baya duk da kuwa idona bai ganinta. Da muka ratso falo haka ƙofarsa ita ma ta buɗe kanta,haka ma ta ƙofar gida. Muna fitowa sai Husseina ta bayyana a gare ni,tana sanye cikin farin likafaninta har izuwa yanzu kuma kukan jinin take. Kan dakali ta ja ni muka zauna kafin ta ce “Haule sai yaushe za ki kuɓutar da mu daga cikin ƙangin da muke ? Har yanzu ba ki samo mahaɗin sirrin tarwatsa BAƘIN RUHI ba?” Jikina banda rawa babu abin da yake yi,na ce “ta ya aka yi kika zo nan? Kuma me yasa kika fito da ni waje? Ai sai ki yi min magana a can ɗakinmu” Ta ce “in muna cikin gidan nan idonki ba za su taɓa gani ba Haule,amma na tambaye ki wane ne kike so har haka wanda ya mantar da ke dalilin zuwanki ƙasar nan?” “So kuma? A'a ni ban son kowa” ban ida rufe bakina ba Husseina ta ɓace ɓat,cike da mamakin ta ya za ta tafi ba ta yi min sallama ba na miƙe da niyyar shiga gida sai dai kuma na tsaya cak sakamakon ganin mutum tsaye a gabana fuskar nan tamau fiye da kullum.Wani irin mugun tsoronsa da shakkarsa ne suka yi min dirar mikiya musamman da na gansa da kayan jikin nan irin na tunanina. “Da wa kike magana?” ya jefo min tambayar cikin tsawa kamar wani ubana. Mayafin jarumta na aro na yafawa kaina na ce “da kai mana” Ya waro ido kafin ya ce “ke kar ki raina min hankali da ni kuma?” “Eh to wa ka gani a nan bayan mu biyu?” “Me kika fito yi to?” “Abin da ka fito yi” na basa amsa kai tsaye tare da yin gaba sai dai ƙofar a rufe take ruf.Na juyo na dube shi,sai na ga yana wani miskilin murmushi kafin ya ce “ina ce dai fatalwa ce ta fito da ke waje? To ki ce ta mayar da ke in tana da izzar zama a inda nake” yana gama faɗar haka sai ya zo yana tsayuwa ƙofar ta buɗe kanta na yi wuf zan shige amma tuni ta rufe shi kuma ya shiga ciki. Tsoro ne ya kama ni,cikin magiya na ce “don Allah Alhaji ka buɗe min ” Banza yayi da ni duk da kuwa da ina jin alamun tsayuwarsa bai tafi ba.Hadari ne ya soma haɗa kansa haɗi da tsawa da walƙiya,nan tsorona ya ninku don kuwa duk jarumtata ban son ruwan sama su dake ni. “Ki faɗa min da wa kike magana sai na buɗe miki ” na tsinkayo muryarsa. Cikin kukan da ya fara zuwar min na ce “ka buɗe min na yi ma alƙawari zan sanar da kai” ai kuwa ya buɗe ƙofar ina shiga na baza a guje na nufi can ƙofar da za ta sada ni da babban falo. Cak na tsaya ina waro ido saboda wani jaririn maciji da ya sarkaye handle ɗin ƙofa,ina juyawa kuma sai na hangi Maheer yana takowa izuwa inda nake.Timmm na ji ƙarar faɗowar macijin kafin ya fara yin silululu yana tawowa,a mugun firgice na yi baya tare da rugawa na tarbo Maheer ɗin na koma bayansa tare da

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});