Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abincinsa” ta faɗa tare da ficewa .Ina kukan sangarta na fita zuwa falo,cikin gunguni nake cewa Ammy “ duk ga ƴan aiki nan amma shine ba za su kai masa ba sai ni ” Ta dube ni da mamaki kafin ta ce “ au! Dama can ƴan aiki ke kai masa abinci?” Ba tare da na ce komai ba na nufi dianing na ɗauki ƙaton tray ɗin da aka jera komai nasa,na ɗauka tare da fita ina tafe ina turo baki har na isa sashen nasa dakyar na lalubo sallama can ƙasan maƙoshi na yi. Bai amsa ba sai ɗagowa da yayi yana kallona kafin kuma ya mayar da dubansa kan system ɗinsa.Hakan yasa na ji haushi na ajiye tray kan table har na juya zan tafi na ji ya ce “ Naf!” na tsaya cak ba tare da na juyo ba ina jiran abin da zai ce sai kawai na ji tsayuwarsa a bayana.Da sauri na juyo muna fuskantar juna,idona tab tsoro nake kallon nasa da nake hango tsantsar ɓacin rai a cikinsu. “ Ka yi haƙuri!” na faɗa murya na ɗan rawa.Bai ce komai ba ya kamo hannuna ya zauna da ni kan kujera,“ ki zuba abinci ki ci” shi ne abin da ya faɗa sam babu wasa a maganar sai ya je ya zauna ya ci gaba da aikinsa. Ni kuwa kallo na soma ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da yalwatacen saje da ɗan madaidaicin gemu,kan jajayen laɓansa na tsayar da ƙwayar idona waɗanda ke yin furucin da babu sauti da alamu wani abu yake karantawa. Tamkar wacce aka yi wa dole haka na ƙanƙance ido ina karanta bakin nasa,na waro ido jin tamkar har da muryarsa ke yi min raɗa a kunne tana sanar da ni abin da yake cewa ɗin. “ Ba ki ji abin da na ce ba?” ya jefo min tambayar,da sauri na mayar da hankali kan abincin haka na zuba na soma ci lokaci-lokaci ina satar kallonsa har na gama. “ Kawo min wanda kika rage ɗin” ya faɗa ,sai na dubi plate ɗin yadda duk abincin ke cakule saboda miya da na zuba dayawa don ina son haka. “ Uncle bari na zuba ma wani” na faɗa tare da ɗaukar wani sabon plate ɗin. Ya ce “ wanda kika rage nake so” Na ɗan ɓata fuska cike da kunya na ɗauka na kai masa,ya amsa ya ajiye shi kan system ɗin kafin ya soma ci hankali kwance . “ Uncle wannan wane ne?” na tambaya ganin wani matashin soja baƙi an naɗe kansa da bandeji. “ Wani ne” ya bani amsa,da ido na ƙara kafe hoton don kuwa ni dai yayi min kyau sosai har ban san lokacin da na ce “ yana da kyau sos...” yadda Uncle ya ƙware ya shiga yin tari ya hana ni ƙarasa abin da nake son faɗa,da sauri na je na kawo masa ruwa ya karɓa tare da rufe system ɗin ya soma sha kafin kuma ya miƙa min kofin ya je ya kwanta kan kujera mai zaman mutum uku yana wani jan numfashi tuni na tsure wuri guda ina kallonsa.... [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 03 Jikina na ɗan rawa na isa gare shi ina mai zube wa ƙasa daidai kusan kansa na ce “ Uncle?” shuru yayi min bai ce komai ba haka ya ƙi buɗe idonsa,hakan sam ba ƙaramar barazana ba ce a gare ni don gani nake na yi masa laifi ne har ya sa shi ƙwarewa amma ban san taƙamaimai mene ne ba. “ Uncle?” na ƙara faɗa wannan karon ina mai kai hannu ina gwale fatar idonsa a dole so nake ya buɗe su ya kalle ni,na kuwa ci nasara ya buɗe su sai dai yadda suka yi ja sosai har sai da na ji tsoro na ɗan ja baya. Murya a disashe kamar wanda ransa zai fita yana kokowa da numfashinsa ya ce “ Nafisa me na faɗa miki? Ban ce kar na saki ko da wasa kin ce wani namiji yana da kyau ko kuma ki kalle shi ba?” Na ɗan ja ajiyar zuciya tare da matsowa na ce “ ka yi haƙuri Uncle ba zan sake ba,amma saboda me Uncle? Ka ga fa duk ƙawayena suna da samari ni amma ka hana ni kuma...kuma kamar mai baƙin jini maza sun tsane ni ” shaaa hawaye suka zubo min tuna yadda ko a makaranta ƴan ajinmu ba su shiga duk abin da ya shafe ni,kusan kuma malamanmu maza ma haka ba kasafai suke saka ni yin wani abu ba,in an zo nan ta wurin ƙannaina da kuma mazan da suka zo karatu a gidanmu su ma duk hakan ce ke faruwa. Ba tare da ya ce min komai ba ya tashi zaune haɗi da ɗan duƙewa ya dafe saitin zuciyarsa,ina ganin haka sai na miƙe da sauri har ina tuntuɓe na nufi bedroom ɗinsa na ɗauko masa maganinsa.Na cika kofi da ruwa tare da ɓallo ƙwaya biyu na miƙa masa ya karɓa tare da sha,cikin ƙanƙanin lokaci ya soma yin wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ ki je ki haɗa kayanki,zuwa jibi sai na kai ki can ƙauyen da za ki koya” Duk ƙuncin da ya cunkushe min zuciya ne ya tafi ban san lokacin da ƙawa zuci ya ja ni ba kawai na rungume shi ina cewa “ na gode sosai my Uncle,kenan har ka yi magana da Daddy ya amince wayyy!” na yi ihun murna ina jijiga bayan Uncle da na rungume tsam a ƙirjina kafin kuma na sake shi da gudu na bar falon. Ina shiga ɗaki na tarar da family na cin abinci,ɗakina na nufa na shiga sauko da akwatina ko taimakon masu aiki ban nema ba na soma shirya kayana ina yi ina murmushi ina jin daɗi na luluɓe min ruhi.Sai hoton kaina nake gani a cikin aji ina koyar da darasi wa ɗalibaina,ban zauna ba sai na haɗa duk kayana na jiki da kuma jaka da takalma. Takardu da littafaina ma trolly daban na ware musu kafin na miƙe ina yawo cikin ɗaki ina magana ni ɗaya kamar irin yadda malamai ke yi.A hankali na soma jin ciwon kan da ya zame min aboki tun na ƙurciya na ziyartata,tun ina daurewa har na kai na kasa jurewa na haye bed na kwanta.Mafarkin da na jima ban yi ba tun shekaru kusan uku shine na soma yi kamar ana jirana. Tsaye nake kan ƙafafuna na mage ina juya idona masu matuƙar haske da hange nesa tamkar na Alhuduhudu. Manyan-manyan dabbobin daji ne a tsaye a gabana suna buɗe min bakunansu masu manyan haƙora yayin da ni kuma ke ankare da kowanne daga cikinsu kafin mu soma yin dambe ina jibgarsu duk na yi musu jina-jina da jini kafin wata halitta mai siffar babban sauro ta caka min bakinta daidai cikina .Azabar da ta ratsa ni ce yasa na saki wani razananen ihu,daidai nan na farka sai dai abin mamaki daidai wurin da aka cake ni ɗin har a zahiri ciwo yake yi min. “ Lafiya Nafi?” Ammy ta faɗa wacce ta shigo yanzu hankali tashe,ido na soma juyawa amma na kasa faɗa

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});