Chapter 27
Chapter 27
motocin suka tashi muka hau titi,ta windown mota muke kallon juna ni da Uncle muna sakarwa juna murmushi har aka zo mararrabar hanya motocin namu suka rabu.Sai a lokacin na maido dubana kan titi ina jin abu biyu,kewar Uncle da kuma murnar cikar muradina ba tare na san abin da ke can yana jirana a ƙauyen Ƙwargwam..... [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 05 Sosai Jabeeru ke sharara gudu kan titin da yake tsit babu kowa kamar an yi ruwa an ɗauke.Kamar daga sama haka na ga tsohuwar nan mai ƙusumbi daga can nesa ta yi tsaye tsakiyar kwalta amma duk nisan tazarar bai hana ni ganin ƙwayar idonta ba wacce ke yi min magana kuma raɗam nake jin sautin muryarta kamar waccan lokacin. “ Me kike jira da har yanzu ba ki sanar da Uncle ɗinki saƙona ba? In wani abu ya samu ɗana sai na ɗanɗana miki azabar da ba ki taɓa tunani ba ballantana gani a duniya” na shagala sosai da kallon ƙwayar idon nata sam ban san lokacin da Jabeeru direba ya kawo dab da ita ba,cikin ƙaraji na ce “ Jabeeru ka taka burkiiii!” sai dai ko kafin in rufe bakina tuni ya ratsa ta jikinta amma abin mamaki sam bai kaɗe ta tamkar dai iska wannan mai kaɗawa haka gangar jikinta take. Jabeeru ya tsayar da motar,ina haƙi ina ƙari na ɓalle murfin motar na fita na je na yi tsaye na duba can gaba a zatona ko zan ganta sheme a ƙasa sai dai wayam ba komai.Kamar wata mahaukaciya haka na ƙara yi a guje na duba bayan motar nan ma babu kowa ko ɗigon jini babu.Da na leƙa ƙarƙashi ma babu komai,tuni sun fito suna tambaya ta lafiya.Kai na dafe kafin na koma cikin mota na ɗauki wayata don na kira Uncle Salem sai dai sam babu network.Zuwa wannan lokacin hankalina ya soma tashi ji nake kamar dai gaske wani abu zai same shi. “ Wai Nafisa lafiya duk kike wannan kai komon kamar mai saffa da marwa?” Inna A'i ta tambaye ni. Ba tare da na dube ta ba na ce “ network nake nema ina son kiran Uncle ne” Jabeeru direba ya ce “ Hajiya fatan dai lafiya?” “ Jabeeru ina son samun network don Allah,mu je ko cikin dajin nan ne mu duba ko zan samu tsauni na hawa” na faɗa kamar zan yi kuka. Inna A'i ta ce “ a'a gaskiya ba zan bari ki shiga daji ba,daga ganin wannan ciyayi ba za su rasa maciji ba.Ki yi haƙuri mu ƙara gaba na san za a samu” Jabeeru direba ya yi caraf ya karɓe zancen“ eh Hajiya wallahi sosai ake samun macizai zo mu ƙara gaba ai mun kusa shiga inda ke da network tun da ga ƙarfen falwaya can ina tsinkaye” jin yadda suke ta tsorata ni yasa na yarda muka koma ciki sai dai juyin duniya motar ta ƙi tashi a dole kuma muka sake fitowa Jabeeru ya soma dubawa. Da wani irin gudu na ratsa cikin ciyayin saboda wasu manyan duwatsu da idona suka hango min.Ina jin Inna A'i na kirana amma ko waigowa ban yi ba ballantana na amsa mata,da isa ta na hau can ƙoli ai kuwa sai ga network ya shigo ko kafin na kira Uncle text ne birjit irin waɗanda ake turowa in an so a kira mutum amma ba a same shi ba.Hannu na rawa na rubuta lambar Uncle Salem wacce ke zaune raɗam a kwanyata,sai na ji yana cikin kira amma ba a ɗauki lokaci ba ya ɗaga yana mai jan ajiyar zuciya yayin da ni kuma na saka masa kuka tare da soma magana “ Uncle Please kar ka tafi tarko suka haɗa maka duk ƙarya ce babu wani kashe sojojinku da aka yi, Please ka koma gida” “ Naf lafiya kike kuwa? Wane irin zance ne wannan? ” ya faɗa .Na ce “ ni ma ban sani ba wata baƙar tsohuwa ce ke son haukata da farko ta ce mijina,yanzu kuma ta ce kai” “ Ya siffarta take?” ita ce tambayar da ya jefo min. Na ce “ tana da ƙusumbi...” ko kafin na ida koro masa sauran bayanan ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ Ok to” yana faɗar haka aka shaida min kuɗina sun ida,daidai nan kuma na ji muryar Inna A'i tana cewa “ Nafisa zo mu wuce motar ta tashi” tuni na sauko na kama hannunta muka fito daga cikin ciyayin don sai da ta biyo sawuna. Muna shiga motar muka ci gaba da tafiya cikin gudun da ya saba,sai da muka yi wajen awa uku kafin ya tsaya mu ci abinci da kuma fitsari sannan muka ɗora tafiya .Ba mu kai ƙauyen Ƙwargwam ba sai wuraren sallar azahar lokacin rana ta zo tsakiya,muna shiga garin gabana ya soma faɗuwa ina jin wani irin yanayi kamar wacce ta taɓa zuwa dama har da wasu tsofin moments nake gani wanda na rasa daga ina suke ziyartar kwanyata sam ban taɓa kawowa cewa suna ɗaya daga cikin ire-iren mafarkan da nake yi ba tun ranar da na soma ganin period. Kamar yadda tun kafin mun tawo Uncle ya bani duk wasu takardun sheda da ya karɓo daga can makarantarmu haka muka samu wani yaro ya kai mu can gidan shugaban makarantar wanda yake cikin ƙatuwar school ɗin wacce sosai na yi mamakin yadda aka yi ma aka gina ta. Da isar mu can sai muka taras da wasu malaman da alamu suma zuwansu kenan .Tarba muka samu daga wajensa kafin ya nuna mana ɓangaren jerin flat/appartement ɗin da aka tanada domin malaman ƙetare waɗanda ba ƴan ƙauyen ba.Kowane daga cikinmu ya bamu key ɗin ɗakinsa kafin mu wuce ,Jabeeru ya tuƙa mota har zuwa ƙofar ɗaki mai lamba uku wato nawa.Shi ne ya kai mana kayanmu ciki,ɗakin tsaf yake bai da datti kamar an sa da zuwanmu.Ciki guda ne sai toilet da kuma ƴar ƙaramar kitchen,haka duk muka jera komai wajensa Inna A'i ta cire zanen da muka tarar shimfiɗe kan ƴar madaidaiciyar kafitar ta shimfiɗa wata,na shiga toilet bakina ɗauke da addu'a na yi wanka tare da alwala sannan na fito sai na tarar tuni Jabeeru ya tafi ko sallama bai yi min ba .Dadduma na shimfiɗa na gabatar da sallah yayin da ita kuma Inna A'i ta shiga toilet ita ma don yin wanka.Ina zaune ina lazumi na ji ihunta haɗi da yin ƙara,kafin kuma na ji tana magana da alamu akwai abin da take kora can kuma ta fito kamar wacce aka jefo. Cike da kulawa na ce “ Innarmu lafiya?” Cikin masifa ta ce “tsakaka ce na gani kin san ban son ganinta“ ta bani amsa. Na ce “ ai kuwa inda kashe ta kika yi da kin samu lada ” Ba tare da ta ce komai ba ita ma ta zo ta yi sallar bayan ta gama ne muka soma taɓa hira kafin kuma mu ji bugun ƙofa,ita ce ta je ta buɗe sai kuma ta dawo hannunta riƙe da kwanon abinci tana mai cewa “ kin ga shugaban makaranta ya aiko mana da abinci” Na ce “ ban jin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38