Chapter 33
Chapter 33
Naf! Ina sonki,ina buƙatar ki a kusa da ni haƙurina ya ƙare” Tamkar wacce aka bugawa guduma a kai haka na ji ,kalamansa kuwa kusan tarwatsa min kwanya suka yi sam kasa fahimtar abin da yake nusar da ni na yi.“Wuce ki tafi ki kula min da kanki”ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɓalle murfin motar na fito..... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 09 Ƙafafuwana har harɗewa suke saboda kalaman da Uncle Salem ya fesar min,ruhina kuwa yayi wani irin sanyi saboda zazzafan romance ɗin da yayi min wanda ya toni duk wani sirrin zuciyarsa da muradinta na shekara da shekaru.Ta ya zan so Uncle soyayya ta aure? Ta ina ma zan fara wannan cakwakiyar da sam ƙanƙanuwar kwanyata ba za ta iya ɗaukar wannan rikicin ba.Ina shiga ɗaki na tarar da Inna A'i tana jera min takardun da ni ce na fidda su a jaka,ta ɗago ta dube ni kafin kuma ta kawar da kai.So nake na shaida mata kalamai da kuma abin da Uncle yayi min ko zan samu sukuni amma sam ba ta bani fuska ba.Wannan yasa kai tsaye na shige toilet,ga mamakina duk jikina ya ɓace saboda abubuwan da yayi min har sai da na canza pant na kuma wanke fuskata.Ina tsaka da maida kwalliyar fuskata na ji ƙarar tashin motarsa,na ja ajiyar zuciya tare da motsa laɓana kaɗan na ce “Allah ya sauke ka lafiya!” sai na ɗauki wani sabon hijabi saboda wancan duk Uncle ya cukuikuye shi sannan hawayena sun jiƙa shi ta gaba. “Na tafi sai na dawo”na faɗa dakyar,ta ce “a dawo lafiya” jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gidan na nufi can ɓangaren makarantar. Ina zuwa gaban ajin da zan koya na tarar tuni ɗaiɗaikun ɗalibai sun zo,haka suka gaishe ni irin yadda ake yi.Wani sanyi ya ratsa ni duk sai na ji ƙuncin ya sauka daga zuciyata har da murmushi,ina nan tsaye kamar sauran malamai bakin aji aka soma kawo yaran sai a lokacin na dinga cewa su shiga aji su zauna.Ina nan tsaye wani ya kawo ƴarsa sai kuka take,da sauri na kama hannunta ina mai rage tsayi na ce “yi shuru mana babyna ko ba ki so na baki alawa?” Cikin murya ƙurciya ta ce “ina so” Na ce “yawwa to yi shuru sai na baki ,me sunanki?” “Firdausi”ta bani amsa,na gyara mata zaman ɗan guntun hijabinta kafin in saɓe ta kamar wata ƴata na ce “to yi wa Daddy bye bye sai mu je aji na nuna miki inda za ki zauna” da murmushinta kuwa ta yi masa alama da hannu,ya ce “na gode Madam ” Na ce “bai komai ai aikinmu ne” sai kuma na shiga aji na zaunar da ita a kujerar gaba ta kusa da kujerar da aka ware domin zamana. Bayan nan na ƙara komawa can bakin ƙofa,ban shigo ba har sai da ajin ya cika zuwa lokacin tuni ƙarfe takwas ta buga.Ina shiga na yi zaune ina kallonsu ɗaya bayan ɗaya ina jin wani sanyi na ratsa min zuciya,kafin kuma na tashi na bi ɗaya bayan ɗaya ina tambayar kowa sunansa.Dukkansu yara ne da ba za su wuce shekara bakwai ba,wasu ma ba su kai ba,ina cikin zagayen ajin sai ga headmaster ya shigo shi da mataimakinsa. Takarda mai sunan ɗalibai ya miƙo min da kuma alli wanda zan yi rubutu da allo,liste ɗin na ɗauke da ɗalibi ɗari cicif.Bayan fitarsu ma sai da na sake kiran sunayen yaran kafin na je na soma yin rubuta a jikin baƙin allon wanda yake goge fesss,kwanan wata na rubutu da kuma ABCD sai na soma koya musu suna yi duk bayan na faɗa.Haka muka ta yi har lokacin shan iska yayi,sai dai kamar yadda meeting ɗin jiya ya sanar da mu dokokin makarantar hakan yasa ban fidda su waje ba. Grand Maa ce ta shigo ita da wata budurwa ɗauke da wani basket,cike da girmamawa na gaishe ta yayin da kuma budurwar nan ta soma raba wa yara abincin da za su ci.Bayan ta gama a gaban idona Grand Maa ta miƙawa wani yaro biscuit kafin su fice. Bayan an gama cin abinci duk suka je suka jefar da abin take away ɗin a shara nan na ci gaba da yin cours ina aika kowane ɗalibi ya zo ya rubuta harafi ɗaya daga cikin ABCD ɗin da na yi musu.Ƙarfe sha biyu na rana cif aka kaɗa ƙarar rawar tashi ,nan aka zo fara ɗaukar yara ba ni na baro ajin ba sai da kowa ya watse . A gajiye na shiga gidan,Inna A'i ta yi min Barka da zuwa na amsa ina mai rage kaya na shiga toilet.Bayan na yi wanka ta gabatar min da abinci,na saka plate ɗin gaba tare da ɗaukar waya na kira Ammy bayan mun gaisa cike da alfahari nake bata labarin yadda ranar farko ta kasance ,sai murmushi take kafin mu yi sallama ina gama cin abinci na ɓingire bacci wanda tamkar jirana ake aka ƙara yi min maimaicin duk abin da suka faru a yau ɗin tun daga lokacin da na je na yi tsaye gaban ajina har zuwa lokacin shan iska na yara.Yaron nan da Grand Maa ta baiwa biscuit na ga yana ta kuka yana kallona yana kiran “madam? Madam cikina ciwo! Madam mutuwa zan yi ,wayyo cikina” amma sam wai na kasa tashi daga kujerar da nake zaune,a gaban idona jini ya soma yi masa zuba ta ƙofofin hanci kafin kuma ya faɗi babu rai bayan yayi wata irin ƙara wacce daga nan na tashi daga baccin. Na yi miƙa tare da duba agogo sai na ga tuni lokacin sallah yayi,kawai na miƙe na je na ɗauro alwala na gabatar da sallar.Sam ban wani bai wa mafarkin da na yi muhimmanci ba sai ma takarda da na ɗauka na soma rubuta abubuwan da zan koyar da su gobe,bayan nan kuma sai muka hau yin hira da Inna A'i lokaci lokaci kuma ina chating abina. Ana kiran sallar magrib na tura wa Uncle saƙo kamar haka “barka da shan ruwa!” Sai ya maido min da amsa da “ azumin da kika yi sanadin karewarsa?” “Kamar ya?” “Eh mana Naf ɗanɗanon yawunki ma kaɗai ya isa ya karya min azumi,uwa uba kuma tattausan ƙirjinki” da ya turo min saƙon nan na karanta shi ya fi sau goma,ina ta juya kalaman cikin tunanina ina jin tabbas Uncle nada buƙatar ganin likita don kuwa na sha jin ana cewa in mutum ya daɗe bai yi aure ba to hankalinsa na yin rauni .Da wannan na yi masa uzuri na ce kawai bai da lafiya ne kuma na yi alƙawarin zan sanar da Daddy a sama masa magani. ★Uncle Salem Ikon Allah ne kawai ya kai shi gida lafiya,duk yadda azumin nasa ya zama gurgu hakan bai sa shi ya ajiye shi ba.Wanka kawai yayi ya ci gaba da yin abinsa har aka kira magrib ya ajiye shi,ya dawo daga sallah kenan ya tarar da saƙon Nafisa .Cikin son nuna mata fa eh haƙurin nasa ya ƙare yasa duk ya cire nauyi ya soma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38