Chapter 20
Chapter 20
kuma sun ce yayi tafiya.Yanzu ma daga can nake saboda na ji labarin yau zai dawo amma kuma bai zo ba,da zan wuce ne na tsaya don in ci abinci saboda yunwar da nake ji sai kuma na soma yin tari haɗi da aman jini” tana kawowa nan na tashi daga gabanta. Ina mai kallonsu,Aliya ce ta soma magana “ina ga yayi amfani da jininta ne don bunƙasa arzikinsa ” Lubna ta karɓe da cewa “a'a bana tunanin domin kuɗi yayi hakan,don in don su ne to zai nemi yayi sex da ita ne ko kuma ya nemi ta basa jinin period ɗinta tabbas sai dai don wata manufar” Bayan duk na saurari jawabansu sai na ce “in dai ba don kuɗi ne ba to tabbas da buƙatar mu je can gidan nasa” “A'a zuwa gidansa ba shi ne mafita ba,neman taimakon ƴar aike dai ya kamata mu yi” cewar Aliya tana dube-dube. Na ce “wace ce kuma haka ?” ba ita ta bani amsa ba,Lubna ce ta ce “duk wata power ko ƙungiya akwai shugabanta Haule ” “Ina za mu samu tukunyar laka?” Aliya ta tambaya. “Ko a kasuwa za a samu,me za a yi da ita?” na tambaya. “Ku fito mu je kafin wasu costumer su zo .Haule rufe ko ina,mu tafi” Aliya ta faɗa ,duk yadda na so yin tambaya kuma Lubna ta hana haka muka rufe restaurant muka nufi kasuwa tukunyar lakar muka saya kafin kuma Aliya ta ja mu can wani guri mai ƙazanta. “Ku rufe idonku ” ta bamu umarnin da na so yin gardama amma tuna halin matar da muka baro yasa na yi yadda ta ce. Wani irin hayaƙi na ji ya turnuƙe min hanci yayin da Aliya kuma ke karanto wasu abubuwa maras kan gado.Yanayin yadda iskan shaƙata ya canza yasa na buɗe ido,cikin wani ƙasurgumin daji ne muke duba da labarin da Lubna ta bamu sam ban yi mamakin hakan ba. “Wannan shi ne ƙasurgumin dajin AOKIGAHARA,ana yi masa laƙabi da dajin fatale da dodanni.Duk wani da ke son kafa ƙungiyar asiri to dole sai ya biyo ta nan domin samun albarka aljanai da kuma tabarakin manya-manyan mashahuran matsafa waɗanda suka taka rawar gani wurin zalunci.Kamar yadda kuke gani dajin ya rabu biyu, wannan shi ne tafarkin haske masu kula da fararen ruhika kuma masu kyautar ƙarfin iko na power,to mu can ne za mu je” Aliya ce ta yi jawabin tana mai nuna mana wata ƙofa wacce wani ƙaton icce mai kan mutum ya raba tsakanin hanyoyin biyu ta sharri da kuma ta khairan. “Kina nufin BAƘIN RUHI ya samo asali ne daga wannan hanyar kenan?” na tambaye ta ina mai nuna ƙofar wacce ke cike da tarnaƙin hayaƙi da duhu. “Wannan amsar ai ke za ki bamu ita Haule saboda maɗaukakiyar ceto da ke a jikinki” Aliyar ta faɗa tare da yin gaba,muka take mata baya ina mai juya kalmar ni ce ke ɗauke da maɗaukakiyar ceto a jikina. Can cikin muka lula kafin mu samu wani keɓaɓen wuri mu zauna,ni ce a tsakiyarsu kamar yadda Aliya ta ce na yi.Bayan duk mun zauna sai muka ajiye tukunyar lakar a tsakiyarmu,yawun bakina na tofa a ciki sai wani irin haske ya soma bayyana daga can ƙasan tukunyar .Gaba na ɗan yi da fuskata na leƙa ciki,da wani mugun sauri na dawo baya sakamakon fuskata da na ga ta rabu biyu.Ɓangaren hagu fuskar Maheer ce yayin da bangaren dama kuma yake tawa,ban san me hakan ke nufi ba sannan kuma ban tambayi Aliya ba wacce tuni ta soma kiran sunaye barkatai sam ban aje hankalina sosai ba tunanin Maheer ne ke yi min yawo a zuciya. “Ban san mene ne matsalar ba ƴar aike ta ƙi bayyana a gare mu,Haule ko da wani saƙo da aka isar miki zuwanmu?” tambayar nan da Aliya ta yi min ya katse min tunanina,na girgiza mata kai na ce “a'a babu wani saƙo da aka isar min” Yanayin fuskar Aliya ya nuna rashin jin daɗi,sai ta miƙe ta ce “ku tashi mu tafi ba za ta zo ba,ban san kuma me yasa ba” haka muka fito daga ɓangaren ba tare da na yi tunanin cewa hoton da aka nuna min na fuskata ta tsage gida biyu sannan ta haɗe da ta Maheer shi ne makullin nasarar da muke tunkara ba. Da muka fito Lubna ta ce “ amma Aliya ita wannan hanyar fa? An hana a shiga ne ko da haɗari?” “A'a ko ɗaya,sai dai ita tana da sharuɗa ne masu tsauri shi yasa ba kowa ke son shiga ba.Kin ga muddin mutum ya shiga to ko ya ga abin tsoro bai da ikon yin ihu ko ƙara,sannan duk abin da za ka gani iya kallo ɗaya ne kacal za ka yi masa ka ɗauke idonka a kai,sannan ko ƙasar cikin wurin ba a yarda ka ɗebo ba ballantana furanni ko wani abu da ke ciki” Aliya ta faɗa . “Haule zo mu je mu shiga mu gani ko ba komai za mu ƙara ilimi”Lubna ta faɗa tana wani kamo hannuna,haka kawai na ji gabana na dokawa amma na daure na yarda muka shiga . Tun a bakin ƙofa wani irin iska mai zafi ya dake min,kuma tamkar an zuƙo mu ne ba tafiya muka yi da ƙafafuwanmu ba haka na ga mun yi saurin shiga tsakiyar wurin.Wuri ne mai cike da furanni masu tsantsar kyawu wanda ya ɓoye sharrinsu da kuma gubar da ke ɗauke da shi.Muna tsaka da tafiya muka dinga jin kukan jarirai,Aliya ce ta yi mana bayanin dalilin kukan. “Dayawan matan da suka rasa rayukansu suna ɗauke da ciki su ne in sun shigo nan suke haife cikin,wani sa'in jariran na rasa madarar da za su sha ne to in sun ji ƙamshin bil'adama ne sai su fara kuka.In da mace mai shayarwa to haka za ki ga madara na ta ɗiga daga mamanta tana shigewa ƙarƙashin ƙasa” ina gama jin bayanin nan sai wani tsoro ya kama ni,duk gani nake ni ma hakan na iya faruwa da ni duk da kuwa ni budurwa ce. Wajen wani koren fure muka ratsa sai ya soma yin rangaji yana motsi tamkar wani mai rai,Lubna ta kai hannu za ta tsinko amma Aliya ta buge hannun tare da cewa “ ba ki ji na ce ba a taɓa komai ba?” “Na manta” ta faɗa tana dariya. Sai da muka yi yawo sosai kafin mu kamo hanyar fita,nan ne na ji tamkar na taka wani abu mai motsin rai.Ina ɗaga ƙafata sai na ga wata sarƙar diamond mai shegen kyawu sai ƙyalli take,kallo ɗaya na yi mata ina shirin kawar da idona amma wani abu ya ja hankalina a tsakiyar sarƙar harafin H ne aka zana sannan ga wasu duwatsu masu kaloli da aka ƙawata harafin. Na duƙa na kai hannu na ɗauki sarƙar,ko da na ɗago sai na ga tuni su Lubna sun kai bakin ƙofa.Kamar wacce aka yi wa dole haka na saka sarƙar a wuyana tare da gyara ɗan ƙaramin hijabina sannan na ɗan ruga na cimmar musu. Ko da muka fito waje sai Aliya ta ƙara mayar da mu can wurin nan mai datti. “Yanzu ya za a yi kenan?” Lubna ta tambaya. Aliya ta ce “mafita guda gare
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38