Chapter 18
Chapter 18
ƙanƙanme shi ina kuka ashe gudun gara na yi na faɗa gidan zanzaro shine mamallakin macijin. “Sahut!” shine furucin da yayi kafin macijin yayi tsalle ya ɗale kafaɗarsa hakan ya baiwa bindinsa bugun fuskata nan take na yi luuu zan faɗi da sauri ya juyo tare da taro ni sai dai muna haɗa ido da macijin igiyar saita numfashina ta katse ban ƙara sanin abin da ke faruwa ba sai da na ji muryar Hajiya a kaina tana cewa “ka ƙi faɗin abin da ya same ta,sannan ma wai me ya kawo ta ɗakinka? Maheer me ka yi wa ƴar mutane?” Wani irin sarawa kaina yayi jin wani batu wai ɗakin Maheer ,ban shirya ba na buɗe idona tarau ai kuwa a ɗakin nasa nake kwance kan bed ɗinsa abin da ya fi ɗaga min hankali bai fi yadda na ji duk ƙamshin jikinsa ya dabaibaye ni ba. Muna haɗa ido da Hajiya ta yi saurin matsowa “Haule me kike yi ɗakin Alhaji?” Shiru na yi don kuwa sam na kasa tuna komai da ya faru ciki kuwa har da zuwan Husseina,abin da na sani dai shi ne ina kwance a ɗakinmu Lubna ta gama bamu labari. Maheer ɗin na kalla wanda shi ma ni yake kallo da idonsa da suka kaɗa suka yi ja kamar tsohon maye. Hajiya ta mangare ni cike da masifa ta ce “don ubanki ba za ki faɗa min abin da kika zo yi ɗakinsa ba?” Shaaa hawaye suka fara yi min zuba,don sai yanzu ma ne nake ganin illar wanzuwata a nan uwa uba kuma ni kaina ban san ta ya aka yi na tsinci kaina a nan ɗin ba. A karo na biyu na juya na dubi Maheer,Hajiya ta buɗe baki da niyyar yin wata masifar iya sunana kawai ta furta Maheer yayi wata irin busa mai ratsa dodon kunne sai ta yi shiru tana mai cewa “In Haule ta gama gyara maka ɗakin ta je ta shirya don Allah kafin su Lubna su gama saka kaya a mota” sai kuma ta fice. Ya juyar da kai gefe ya ce “ki tashi ki koma ɓangarenku” “Amma Alhaji me ya kawo ni nan?” na yi tambayar wasu sabbin hawaye na ƙara zubo min. “Dalla Malama saukar min daga gado,ban sani ba ki je ki tambayi fatalwar da ta kawo miki ziyara” ya faɗa a hassale. “Fatalwa kuma?” na yi tambayar,ya zo da ƙarfi ya wani fizgo ni na faɗo daga gadon amma sai na yi saurin miƙewa ina jin tsanarsa na ƙara ninkuwa a raina.Idona har wani rufewa suke na nufi ƙofar fita,da na ratsa falonsa ne idona ya sauka da duwatsun awarwarona nan ma mamaki na yi,na duƙa zan kwashe su amma tamkar yadda iska ke ɗaga leda haka duk suka tashi sama suka yi bayana,sai na juya nan na ga ashe shi ne yayi amfani da siddabarunsa ya janye su. Hannuna na duba na ga yayi ja alamun an yi wa wurin mugun riƙo,ban tanka shi ba na fita.Ina fara taka step na ga Lubna a tsaye tana kallon benen wanda yake ɓangaren Maheer ne,a cikin idonta nake hango wasu abubuwa da suka haɗa da zargi da kuma mugun kishi amma ban kula ta ba na wuce part ɗinmu. Sai da zan shiga toilet ne na lura doguwar rigar baccinsa a jikina,na kwance ɗaurin na jefar da rigar amma abin mamaki sai ta ƙi taɓo ƙasa. Ban san lokacin da na furta “matsafi kawai” sai kuma na ɗauki rigar na ajiye ta cikin jakar kayana.Bayan na shiga toilet na cire kayan jikina,ina wanka amma ƙamshinsa ne ke tashi.Bayan na gama wanka na zo na gabatar da sallar asubah wacce ta wuce ni don tuni ƙarfe bakwai ta buga. A gaggauce na kimtsa cikin kaya masu kyau sannan na ɗauki rigar da nake ɗorawa a sama mai sunan Hajiya da kuma restaurant ɗinta. Ko da na fito tuni an jera komai a mota,cike da ladabi na gaishe da Hajiya .Yadda na ga Lubna na kauce min yasa ban takura ta ba akan sai mun yi magana,a yau tare da Aliya za mu je a nisa umarnin Hajiya hakan yasa muka shiga mota muka wuce can. Bayan an gama jera komai a wurinsa sai kuma na fito nan inda ke teburan cin abinci na ƙara gyarawa,babu jimawa kuwa mutane suka fara zuwa Aliya ta dinga taya ni aikin har muka samu ƙafa ta ɗan tsana sai na zuba abincin da za mu ci,sai kuma a lokacin na dube ta da kyau na ce “Aliya don Allah me ya faru a jiya a gidan Hajiya na kasa tuna komai,kawai dai na tashi na tsinci kaina a ɗakin Alhaji ” Dama tun tuni na lura ita ma da magana a bakinta,kawai dai ta yi shiru ne. Aliya ta ce “to mu dai mun tashi ba mu gan ki ba,shine Anty Lubna ta je ta sanar da Hajiya ita kuma tana shiga ɗakin Maheer don sanar da shi ta tarar da ke a gadonsa kina bacci sai ta yi kururuwa duk muka haura sama kafin kuma mu iya cewa wani abu shi Alhajin ya fito daga wanka dole muka fita waje saboda mugun kallon da watso mana.Amma ni ma ban san me ya faru ba,na dai ji Anty Lubna na cewa kin ci amanarta kin je ɗakin Alhaji alhalin kin san tana sonsa,kuma wai don kawai ta yarda da ke ne shi yasa jiya ta bamu labarin cewa sperm ɗinsa ne ta kai a madadin na Dr David ” Kaina ne na ji yayi wata irin sarawa,ɓacin rai ya ƙara dirar min.Tsakanin jin sperm ɗin Maheer ne Lubna ta yi amfani da shi,da kuma jin zargin da take min sai na rasa wane ne ya fi yi min ciwo. Abincin na ji ya fita raina,na miƙe na wanke hannuna.Kuka nake son yi don samu salamar zuci sai dai ina fitowa idona yayi tozali da wata mai ciki tana aman jini duk ya ɓata teburin da ke gaban kujerar da take zaune,hankali tashe na nufe ta sai dai tana ɗago idonta na tsaya cak sakamakon abin da ya gigita ji da ganina..... My book is only 500 amma na yi discount daga yanzu zuwa kafin na saki page 10 ta ƙarshen free.ki tura 300 ta wannan account 2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min da shaida biya +22795045822 Wacce ba ta shirya ba don Allah kar ta yi min magana [06/04 14:24] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ Last free page 10 Fuskarta ta yi wani irin ja kamar za ta tsage jini ya zubo,ga idonta da suke baƙi ƙirin sam babu hasken nan.Bakinta kuma jini ne shaɓe-shaɓe yana mai ci gaba da ɓulɓulo mata.A kallon tsanaken da na yi mata duk ta yi gudu ba za ta haura shekara ashirin da biyar ba,sam kasa cira ƙafata na yi daga inda nake sai ita ce ta yunƙura ta taso ta zo tare da zubewa gabana.Yatsun hannunta na taɓa ƙafata na ji wani irin yanayi ya ratsa ni,yanayi ne wanda na taɓa shiga irinsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38