Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,228 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

“To ki karɓo min” Ina jin haka na yi saurin wucewa can ɗakinmu da aka ware na ƴan aiki.Ina tsaka da rage kayan jikina Lubna ta shigo hannunta riƙe da kofi ta ce “ki zuba na kai mata” Cikin ƙunar rai na ce “na ƙi na zuba ina ce dai yawuna ne” Lubna ta tuntsire da dariya tare ɗan matsowa kusa da ni ta ce “ke ba abin alfaharinki ba ne a ce kamar Hajiya tana shan yawun ƴar aiki ? Kin san da ace ta san mene ne ainahin maganin da ba za ta sha ba Alkur'an yadda ta tsani talaka” Wani ɗan murmushi na yi kafin na tofa yawuna cikin kofin ruwan,nan take suka soma tafasa suna motsi tare da canza kala. Lubna ta ɗaga gira ta ce “ai ke ce Hajiyar,sannan don Allah ki yi haƙuri ki bar saka mana hajiyarmu cikin wancan halin kar ta je ta mutu mu shiga tara” “Tafi dai ki kai mata kika tsaya surutu” na faɗa tare da shiga toilet na yi wanka,ko da na fito sai na tarar da Lubna ta kawo mana abinci.Nan ɗin ma wani murmushi na yi kafin na ce “cewa ta yi fa ba za ta ban abincinta ba” “Tun da dai ta zuba miki sai ki yi haƙuri ki zo mu ci” cewar Lubna. Sai da na canza kaya sannan na zauna muka ci shinkafa da miya muka hauda ruwa masu sanyi.Sai kuma muka hau yin hira kafin kuma ta miƙe ta ce “bari na je na gyara kayan miya na gobe,ki shirya don da na dawo za ki ɗora min labarinki” na yi murmushi kawai ba tare da na ce komai ba. Ina shirin kwanciya Lubna ta shigo kamar an jefo ta,na ce “ke lafiya?” Ta ce “uban ƴan tsamin rai ne ga shi can a falo tare da Hajiya yana juya kofin da na bata ruwa wai yana son ganin wane irin magani ne wannan da ta sha ta samu lafiya lokaci guda” Na ce “to mene ne na ga duk kin tayar da hankali?” Ta waro ido ta ce “hajiya ce ta basa amsa wai ke ce kike da maganin,kuma walla...”sauran maganar ce ta maƙale mata ganin an banko ƙofa da mugun ƙarfi har ni ma sai da na zabura yayin da haɗuwar idonmu ya saukar min da matsanancin faɗuwar gaba amma na aro mayafin jarumta na gaishe shi cike da ladabi kamar yadda uwarsa ta ce mu dinga yi. “Ina wuni Alhaji ?” na furta cikin sanyin murya ina mai sauke idona ƙasa. “Bani maganin da kika jiƙawa Mama ” shi ne abin da ya ce. Na ce “ya ida ai dama guda ne ya rage” “Bani kwalinsa ” “Bai da kwali ” “Ina aka taɓa sayar da magani babu kwali?” “Wannan ɗin ba sayar da shi ake yi ba ai,na gargajiya ne” “Ina son ganin ledar da aka ƙulla shi to” ya faɗa cikin son sai ya ƙure ni,na ɗago kai na kalle shi kafin na juyar da idona gefe na ce “na share ledar” Bai ƙara cewa komai ba ya fice ƙuuu tare da banko ƙofa. “Ina ga gida zan je zuwa an jima sai na dawo, wannan masifar ba ta ida ba wallahi sai ya sake dawowa kin san shi da zafin kai.Kuma ni ban son ganinsa cikin wannan halin duk sai na ji babu daɗi kuma gwiwaina su yi sanyi” Lubna ta faɗa tana yin wani kalar tausayi. Na taɓe baki na ce “ni ban ga abin da kika gani a jikinsa ba da har kike wani sonsa haka,mutum a bushe kamar mai cutar HIV sai shegun manyan ido kamar ƙuliƙuli dama-dama dai lips ɗin nasa su ne kawai masu kyau” Lubna ta yi min dundun wasa ta ce “ke ban fa son rainin hankali,alhajin ne kike shammata haka? Haba dai! Kuma ni ba sonsa nake yi ba kawai dai yana burge ni” ta ƙarashe zancen tana wani murmushi mai tona asirin zuciyarta. Canza zancen na yi na kamo wani,“ sai yaushe za ki dawowa nan da kwana? Allah na gaji da zama ni ɗaya cikin ɗaki kamar mayya” Lubna ta ce “ke na manta ban faɗa miki ba,ɗazu bayan kin tafi restaurant an kawo wata ƴar aiki da alamu nan za ta zauna ita ma tun da ba ta da kowa kamar ke take” “Ni babu ruwana da wata,ke nake magana yaushe za ki dawo nan? Na ga dai san ba za a hana ki ba duba da Umma ƙawar Hajiya ce ” “In na je yau zan tambaye ta in ji in za ta bar ni,amma da wuya kam zan dai gwada.Na tafi sai zuwa yamma zan zo kamar kullum” cewar Lubna .Sai na saka hijabi domin yi mata rakiya duk da ba wani nisa ne ke da kwai da gidan Hajiya zuwa nasu . Muna ratso falon muryarsa ta tarbe mu sai masifa yake duk a kan maganin da na bai wa uwarsa ta sha ta warke. Muna haɗa ido da shi ya ce “nan gaba duk ƴar iskar da ta sake bai wa Mamana maganin ƴan bori sai na kulle ta ,kar a sake shigo mana da kayan tsibo cikin gidan.Ke ma Mama ki rasa maganin da za ki sha sai na gargajiya? To mene ne amfanin karatun likitacin nawa?” Ban kula shi ba don na fahimci tun ranar da na zo nan gidan ya tsane ni,wannan dalilin yasa ni ma yake ban haushi.Muna fitowa daga gidan Lubna ta ja wata ajiyar zuciya a bayyane kafin ta ce,“matar Maheee nada jan aiki,a yi mutum sai masifa kuma sam bai ma gajiya ” Na ce “shi yasa yake ramewa ita ce duk ta cinye shi masifafe Allah ma ya raba ki da aurensa,don wannan ina ga har dukan mace sai yayi” Lubna ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “mutumniyata inda fa kike burge ni ke ɗin kamar yayen aljanu kike,to in faɗa miki jiya-jiyan nan ya ɗirka wa buduwarsa shegen duka saboda ya tarar da ita tana hira da wani ɗan ajinsu.Ina jin Hajiya na bai wa uwar budurwa haƙuri wai shegiyar zuciya ce da shi wannan yasa bai controling kansa” Ban san me yasa na ji zuciyata ta yi min wani iri ba duk sai na ji babu daɗi,na ce “budurwa? Dama yana da budurwa ne?” “Kin ji ki da wani zancen kuma,kamar Maheee ɗin ne zai rasa budurwa? Hum! To in faɗa miki shegen son mata ne da shi a yadda na ji Ummah na faɗa ƴan matan da yayi ba su da iyaka,in kin gansa da wannan yau to da an kwana biyu ya canza wata” Cike da ɗacin rai na ce “amma kuma bai yi kama da mai son mata ba,duba da ko kallon su bai yi.In fa kin ga ya kalle ki to fitinarsa ce ta motsa kawai don ya tsorata ka da shegun idonsa kamar na jinjirin jinnu” Lubna ta ce “ki shirya wata rana mu je asibitin da yake aiki ki ga yadda mata ke ɗaukar wanka saboda shi,kuma wallahi har da matan aure” Ban ƙara ce mata komai ba na yi gaba don dama can tsaye muka yi muna ta zuba,sam ban ji wuyar tafiyar ba saboda yadda zuciyata ke azalzala tana wani irin zafi .Ban

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});