Chapter 7
Chapter 7
ke magana.Sai fa rayuwarsu ta soma burge ni ina sha'awar cewa ina ma ni ce,zan iya ce muku ma har hassadarsu ke tsarga min musamman in na ga mace wacce ba ta yi wani dogon karatu ba amma tana da kuɗi sosai nake jin haushi.Sai kuma ƙarfin imanina yayi ƙasa ina ganin Allah ya azurta kowa amma ni ya bar ni cikin ƙuncin talauci ni iyayena waɗanda kusan ma a lokacin ni ce ke kula da su saboda Abbana da ya samu karaya bai aikin komai. Kusan da wannan burin yin kuɗi nake kwana nake kuma tashi da shi har Allah ya jefo min wata ƙawata da muka yi makaranta da ita.Ba zan manta ba wata baƙar rana ce wacce ta shiga lissafin ƙaddarata,ina kwashe plate ɗin da aka ci abinci na ji muryar wata da na sani ta kira suna “oh Lubna ? Ke ce?” ni ma cike irin zumuɗin nan irin ka jima ba ka ga mutum ba na nufe ta zan rungume ta amma don wulaƙanci ta yi saurin ja baya tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi kafin ta ce “wai ƴar aiki kika zama bayan duk uban karatun da kika yi? Ki rasa abin da za ki yi sai tarben customer ?” Duk da na ji babu daɗi haka na danne zuciyata na ce “to ya zan yi tun da ban samu aikin gwamnati ba,faɗa min Zulaihat ina kike aiki?” Ba ta bani amsa ba sai wuri da ta samu ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin,“me ke da kwai marar nauyi ? Don yunwa nake ji shi yasa ma na tsaya da motata cikin rana na ci abinci na wuce” ni kuwa gwiwaina ne suka yi sanyi jin Zulaihat ce wai da mota duk da ban yi mamaki ba duba da suturar jikinta iya jakarta ma tana iya ciyar da ƴan gidanmu na tsawon wata biyu,uwa uba kuma wayarta iphone wacce kusan duk masu zuwa restaurant ɗin nan ina ganinsu da ita. Jiki na yi min ɓari na ce “jira na je na kawo miki” sai na koma can ciki na haɗo mata abincin da na san ƴan gayu irinta na so har da lemun kwalba,da na kawo mata sai ta bani damar zama kan kujerar da ke kallon tata.A kunyace na zauna, Allah yayi min sa'a ma babu kowa.Cike da yanga take juya cokali cikin plate ɗin kafin ta soma ci tana latsa waya,message ne na WhatsApp ta soma kunna wa ina saurare kusan duk akan manyan kuɗi ne da kuma kayan da mutane suka yi oder ko kuma suka saya suka yaba,can kuma ta soma mayar wa na ji tana zancen za ta tura miliyoyin kuɗaɗe.Ni kuwa ina zaune sake da baki ina kallonta,kuma kar ku ji zancen wasa wallahi burge ni ta yi yadda take abu na ƴan gayu.Hummm! Faɗar mintinan da na share a zaune kafin Zulaihat ta dube ni ƙaramin misali an fi goma sha,can ta ɗago ta dube ni da idanunta da suka sha gashin zamani ta ce “Lubna gaskiya ba zan ɓoye miki ba na ji takaicin ganinki a wulaƙance kina boyi-boyi,da kyawunki da iliminki.Amma dai komai ya wuce tun da Allah yasa mun haɗu zan duba na gani” Ba tare da na san wane aiki ne za ta samo min ba na shiga yi mata godiya,nan ta shiga nuna min hotunanta da ta yi ƙasashen duniya .Ni kuma sokuwa girman burina sai ƙara farashi yake ina jin cewa ni ma nan gaba kaɗan zan koma kamar Zulaihat,da za mu rabu sai ta bani lambata da ke jikin wani ɗan ƙaramin kati mai ɗauke da dukkan address ɗinta da kuma kantinta na business.Ba ta bar ni haka ba,sai da ta ware dubu goma ta bani shi ma wai don ba ta da canji ne kuɗinta duk daloli ne. Da na isa gida kasa bacci na yi,haka na yi ta juyi kan shimfiɗa .Saƙo kuwa na rubuta shi ya fi cikon casbi kuma sai na goge a ganina sam ba ta cancanci in yi mata text ba.Can na daure na kira ta, lokacin ƙarfe goma saura kwata na dare,har zan yanke kiran sai kuma na ji ta ɗauka tana cewa “Lub baby ƴar halak kin ƙi ambato yanzu na gama maganarki wurin oga ” Na washe baki na ce “na zata ma kin yi bacci,na gode sosai da wannan ƙoƙari me ogan ya ce ?” “Ki zo gobe nan babban kamfani yana son ganin ki,sannan ki haɗo da takardun karatunki sai takardar shaidar ɗan ƙasa da kuma hotonki kala biyu ” Tamkar na yi hauka haka na ji lokacin ba tare da na san ƙaddara ce da rabon a yi ke ja na ba.Tun a daren na jawo ambalof na shiga haɗa takarduna don dama kusan ina da komai da ake buƙata in aka fidda hoto.Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni a wannan daren,shi ma rabi da rabi ne.Tun bayan sallar asubah na shaidawa Umma zancen aikin sosai ita ma ta yi murna.Zuwa ƙarfe takwas na je gidan hoto aka yi min guda biyu,a nan take kuma aka bani su.Daga nan na kira Zulaihat sai ta ce na jira za ta zo ta ɗauke ni,ina nan tsaye ina jiran zuwanta sai wata tsohuwa ta tsaya kusa da ni tana mai neman sadaka .Murnar na samu aiki yasa na zuge jaka na bata sadaka,tana karɓar kuɗin sai ta soma juya su haɗi da kallona tsakiyar ido ta ce “ƴata ki koma gida inda za ki je ɗin nan babu alkhairi ” wani irin haushin ta bani kafin ma na kai ga yin magana Zulaihat ta parker motarta tana yi min horne,da sauri na zagaya na buɗe na shige ina jin tsohuwar nan na sake jaddada min maganarta amma na yi kunnen uwar shegu da ita . Fuska a sake muka gaisa kafin ta ce “ke ma dai kin kusa ki faso gari ki huta da yawon raba abinci a restorant” Na yi murmushi na ce “ai kuwa dai kin ga ban ma shaida wa Hajiyar na samu aiki ba” “In an gama miki interview ai sai ki je ki sanar da ita” Haka muka ta yin hira har muka isa wani katafaren kamfani,duk da ina cikin garin amma ni ban taɓa ganinsa ba da idona ina dai jin labarinsa.Tun da muka fito daga cikin mota ake gaishe da Zulaihat,sai na fahimci tana da babban matsayi a wurin . Jikina ne ya soma yin rawa lokacin da muka shiga ofis ɗin ogan,komai na wurin ja ne tun daga labulaye capet da kuma kujeru.Hatta kalandar da ke ɗauke da jerin sunayen watanni ita ma ja ce,haka ma book ɗin nan da mutane ke ɗauke abu mai muhimmanci shi ma ja ne. Wuri ta nuna min na zauna kafin ta ce “jira yanzu zai fito” sai na sakar mata murmushi kawai ina mai ci gaba da sauraren bugun zuciyata.Kamar minti biyar haka wani babban mutum ya fito,baƙi ne wulul kuma gajere yana da ƙiba sosai ga kuma ƙaton tumbi kamar mai cikin wata tara . Cike da girmamawa na sauka na gaishe shi har ƙasa,ya amsa cikin sakewar fuska kafin ya bani umarnin na koma inda nake.Zulaihat ce karɓi takarduna ta miƙa masa,a nutsu ya shiga duba su kafin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38