Chapter 15
Chapter 15
duk shaƙiyancina na tsani zina ban ƙaunarta ko kaɗan.Ko da ace saurayina ne wanda nake so ban ji zan iya basa kaina ba ballantana sindiƙin ƙato mashuriki matsafi. A lokacin da zuciyata ta yi rauni sosai,shine ganin yadda jini ya soma yi wa Abba zuba ta hanci da kuma ido daga ƙarshe yayi shaƙuwa shikenan ashe ta fitar rai ce.Wuaren ƙarfe bakwai ne na yamma likito suka tabbatar mana da hakan,tsabar tashin hankali yasa na suma aka bani gado.Ban san abubuwan da suka faru ba sai a washegari na farka tuni kuma an kawar da gawar Abba an kai shi mankwancinsa na gaskiya.Sai a lokacin na yi kukan mutuwarsa kamar raina zai fita,kafin a sallame ni daga asibiti Allah ya ƙulla alaƙa tsakanina da wani Dr David shine ma ya ɗauki nauyin biyan kuɗin maganina har na ji ɗan sauki. Bayan na koma gida ma haka yake zuwa yana kula da ni,kusan ma in ce shi ya ɗauki nauyin gidanmu tun da babu wanda ya tallafa mana daga dangi. Cikin abin da bai wuce wata ɗaya ba wata irin shaƙuwa ta shiga tsakanina da Dr David ,sonsa ya samu matsuguni a zuciyata duk da hankalina bai kwanta ba saboda shirun da Zuly ta yi sam ban yarda da shi ba,don na sha jin yadda ƴan ƙungiyar asiri ke da mugun naci.Ashe kuwa ban saɓa lamba ba,a wani yammacin Laraba mun ajiye magana Dr David zai zo ya ɗauke ni mu je gaishe da mahaifiyarsa .Mun yi waya da shi kenan ya shaida min ya ga shi nan zuwa,bayan kamar mitin goma aka kira ni aka shaida min yayi hatsari yana can asibiti . Cike da tashin hankali na fita ko Ummah ban shaida ma ba,ina fitowa nan cikin layinmu wani mai mashin ya kaɗe ni sai da na yi sama na faɗo duk kayan jikina suka ɓace da ruwan dauɗa,dole na koma gida na yi wanka ina ƙoƙarin sake fita kuma ita ma Ummah ta soma nata ciwon abu kamar wasa sai ga mu har da zuwa asibiti. Bayan mun dawo gida na yi ta gwada kiran Dr David amma layin bai shiga,amma ban haƙura ba a cikin haka na samu ya shiga sai dai ba shi ne ya ɗaga ba mahaifiyarsa ce wacce nan take ta hau ni da masifa akan na rabu da ɗanta kar abin da nake ciki ya shafi ɗanta na je can na ƙarata da matsalata.To a nan ne fa na gane zama bai same ni ba,sam kasa bacci na yi .Tsakar dare kuma ciwon Ummah ya ƙara tashi ta soma numfashi kamar za ta mutu,a lokacin tuni na soma yin kuka na ɗauki wayata tsabar ruɗewa wai da Dr David zan kira nan ne na ci karo da saƙon Zuly tana yi min hannunka mai sanda tare da barazanar cewa in ban yarda na dawo bakin aiki ba to zan rasa Ummah tamkar yadda Abba ya tafi. Ina matuƙar son Ummana wannan yasa na aika mata saƙon zan koma a gobe,hum in faɗa muku wani abin mamaki kamar cirar ƙaya haka Ummah ta warke ta samu bacci.Sai na ji na ɗan samu nutsuwa,ni kam ban yi bacci ba har sai da na yi sallar asuba wacce zuwa yanzu ina yin sallolina. Sai wuraren ƙarfe tara na farka,na yi wanka na shirya sai kuma na shaidawa Ummah zan koma a bakin aikina. “Ni kam Lubna tun da Abbanku ya rasu ban ga wani daga cikin ƴan wurin aikinku ya zo ba,har shi ogan naki” shine abin da Ummah ta ce. Na ce “kin san na rasa wayata,kuma oga ba ya ƙasar ita kuma Zulaihat faɗa muka yi lokacin da na ce ta ara min kuɗi ta ƙiya ƙila shi yasa ba ta zo ba ko kuma ba ta samu labari ba” “To Allah kyauta,ki je Allah ya tsare ki ya kuma kare ki da sharrin dukkan mai sharri” Cike da jin daɗin addu'arta na amsa da “amen” kafin na fita.Ina zuwa bakin titi motar Zuly ta parker a gabana,zuciyata cike da ƙunci na je na zagaya na buɗe na zauna ta saki murmushi mai sauti kafin ta ce “barka da safiya” ban amsa ma ta ba har muka isa gidanta na canza kaya muka wuce. Sosai na yi mamakin yadda aka shirya min tarba ta musamman,har da yi min wankan fure aka yi min kafin kuma na yanka cake aka shiga taɓi.Bayan wannan sai muka wuce ofis ɗin oga ni da Zuly,bayan mun zauna ne ya soma yin magana “Luby duk da dai ban so kika rasa damarki ta farko ba,amma mun rarrashi Boss kan ya janye wannan dokar duba da yadda kike da ƙoƙarin aiki dakyar ya yarda amma da sharaɗin za ki kawo sperm ɗin wani wanda kika sani mai ilimi” Na ɗan yi saƙo kafin na ce “a ina kuma zan samu sperm oga?” Zuly ta yi karaf ta ce “ saurayinki David mana ,ai kin ga yana da ilimi sosai kuma ma ai kin ga ba musulmi ne ba ballantana ki sha wuya wurin shawo kansa” Shiru kawai na yi,duk da na ga sharaɗin ba wani mai tsauri ne ba amma tabbas na san da haɗari a ƙasa. “Ko kuwa dai kin fi so a dinga yi wa ahalinki ɗauki ɗaiɗaya suna mutuwa ɗaya bayan ɗaya?” Zuly ta jefo min tambayar da na ji tamkar na shaƙe mata wuya,kuma sai yanzu ma ne raɗaɗin mutuwar Abba ya fi yi min ciwo fiye da can farko. A hassale na ce “ kar ki yi kuskuren taɓa Ummana don wallahi zan shayar da ke mamaki,kun faɗi sharaɗinku ai sai ku jira in ban yi ba sai ku bijiro min ta nan” Oga ya ce “ Zuly ke ma ya kike yi mata magana haka? Ki yi haƙuri Luby ki je ki fara shirye-shiryen taron da za ki gabatar yau da dare,Zuly ki bata sanadaran da kuka fitar na taurari”cewar oga kafin ya miƙe ya shiga toilet,ita kuwa jakarta ta zuge ta miƙo min wasu kwalabe biyu ɗaya mai baƙin murfi yayin da ɗayar kuma ke da farin murfi.Na karɓa ina juya su yadda kowacce kwalba ke fitar da bata kalar hasken. “Baƙin tauraro yana da matuƙar muhimmanci ga waɗanda suka san amfaninsa,shi kuma farin yana ƙara ƙarfin power ne kawai” Zuly ta faɗa kafin ita ma ta tashi ta take wa oga baya.Ba a ɗauki lokaci ba yanayin sautinsu ya fara farmakar kunnena babu shiri na fita na bar ofis ɗin amma sam sautin ya ƙi fita da kwayanta hakan ya haifar min da zuwan wani hatsabibin feeling wanda ya fi kama da na haddasawar sheɗanu.Ido kawai na lumshe tare da ƙanƙame jikina,a inda nake zaune nake a cikin ofis ɗin Zuly nake jin wasu idon sharri na ankare da ni amma da na duba ban ga kowa ba. Ina zaune cikin wannan hali Zuly ta shigo,jan bakin da ta saka duk babu shi a leɓenta sannan zaman rigarta ma haka.Ba tare da wata damuwa ba ta ce “kafin mu isa Japan ya kamata ki aiwatar da aikinki na kawo sperm ɗin David,ki tabbatar komai ya tafi kan tsari” “Ta ya za a yi na samu sperm ɗinsa ba tare da mun yi sex ba?” “Ki yi tunani Luby,yin sex da masoyi ai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38