Chapter 21
Chapter 21
mu a yanzu shi ne mu je can gidansa” Kamar wacce aka tsikara na ce “na san gidan” duk suka kalle ni da mamaki,amma tun da abin da suke so ne kawai ba su tambaye ni ta yaya ba sai muka ɗau taxi ni ce na dinga nuna masa hanya har muka isa gidan. Bayan mun sallami mai taxi muka fito muka yi cirko-cirko,unguwar tsit take sosai ma na yi mamakin ta yadda aka yi Meelat har ta iya ganin maƙwabtan Alhajin. Aliya ce ta soma juya hannunta mai power ta ɓalle kwaɗon da aka rufe gidan da shi,su biyun duk suka shige ciki yayin da ni kuma na tsaya ina kallon wata matashiyar budurwa wacce ke zabaya tana leƙena ta wata can saman benen ɗaki. ‘Wace ce ita kuma waccan mai farar fata kamar fulawa?’ na tambayi kaina a zuci,ban kai ga samo amsa ba na ji kururuwar su Lubna daga can cikin gidan.A guje na nufi ciki sai na tarar suna gurmuzu su da wani gogon Biri duk yadda Aliya ke da power ta kasa tsayar da shi domin shi ma an tsafe shi.Abun mamaki ina shigowa sai ya tsaya cak tare da zubewa ƙasa yana wani irin abu kamar yana gaishe ni,ƴar kallon-kallon muka fara yi mu ukun . “Haule ke ma irin wannan protector ɗin gare ki? Na ga duk jikinsa yayi sanyi” Aliya ta yi min tambayar da sam ban ma gane mene take nufi ba hakan yasa na share ta na ce “ga ɗakin akwatin gawar nan” na nuna musu shi da yatsa sai suka nufi ƙofar yanzu ma Aliya ce ta buɗe ta. Sai bayan sun shiga na take musu baya ina mai waiwayen Birin da har zuwa yanzu yana a yadda yake. Kiciniyar buɗe akwatin suke amma sun kasa,don power Aliya ma ta ƙi yin aiki.Sai na zo na kama musu amma ta ƙi buɗuwa,Lubna ta ce “ina ga akwatin nan jini ne makullin buɗe shi” Duk sai muka kalle ta,kai ta jinjina ta ce “wannan tambarin Family ne” ta nuna wani logo da ke jikin akwatin. “To jinin wa za a tsaga?” na yi tambayar. Aliya ta ce “in dai haka ne da na Lubna za a yi amfani duba da ta taɓa zama cikin ƙungiyar,na san har zuwa yanzu zanen hannunta bai goge a rubutun da suka yi ba” sam ba mu yi tunanin wannan babban kuskure ne za mu tabka ba,haka Lubna ta tsaga yatsanta ɗigon jininta ya ɗiga sau uku a jikin tambarin nan take akwatin ya soma buɗe kansa a hankali wari da ɗoyi yasa suka ja baya,yayin da ni kuma na toshe hancina tare da matsawa ina leƙen akwatin.Yana gama buɗewa na ji an tunkuɗa ni ciki na faɗa yayin da kuma akwatin ya rufe ruf da ni a ciki.Cike da tashin hankali na soma kiciniyar buɗe shi amma ya ƙi yi,ina jin muryar Aliya kuma na cewa Lubna “don me kika yi haka? Yanz...” ban ji ƙarashin maganar ba sakamakon ƙanƙame ni da gawar ta yi tana yi min maganar da ta birkita lissafina.Daidai nan free page ya ida in kina son ci gaba sai ki tura 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 🔞Yanzu nake rubuta shi Ni ma banda complete in kin biya group ne zan saka ki 06.Apr.25 [06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️ ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta. *FCWA*☀️ ________________________ 01 Ra'ayi riga in ji ƴan magana, wannan haka yake a lokacin da matasa sa'anina ke sha'awar fita waje domin yin dogon karatu tare da burace-buracen ababen ƙyalƙyalin duniya ni kuma shiga ƙauyuka ne ra'ayina domin koyar da yaran da ke cikin duhun jahilci.Sunana Nafisa,matashiyar budurwa ƴar kimanin shekara ashirin da biyu a duniya.Na fito gidan sarauta,a jinin masu izza da taƙamar dukiya sai dai ni sam ba wannan ne a gabana ba.Duk da na sha wahalar shawo kan mahaifina kan ya bar ni na yi karatun zama malamar makaranta amma kuma fafur ya hana ni fita aiki wanda hakan ba ƙaramar barazana ba ce da cikar burin nawa. Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye na nufi ɗakinsa,shine kaɗai tilo da na san zai iya yin magana mahaifina yayi amanna da ita ba tare da gardama ba.Ko sallama ban yi ba ballantana neman izini kawai na tura ƙofar,kamar kullum yana zaune kan dadduma yana jan casbi.A gabansa na zube kamar raƙumar da ke jin ƙishi,ya ɗago fararen idonsa ya zube su a kaina kafin cikin tattausan furuci ya ce “Naf !” Baki na turo gaba idona na sake zubo da wasu sabbin hawayen. “ Yau kuma wa ya taɓa ki?” ya tambaye ni cikin nutsuwarsa wacce ke ƙara masa ƙwarjini. Cikin kuka na ce “Daddy ne wai ba zan yi aikin gwamnati ba” Yayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa waɗanda kullum suke shan gugar asuwaki kafin ya ce “ki je zan yi masa magana” da sauri na girgiza masa kai na ce “ a'a Please uncle ka tashi mu tafi yanzu kafin masu hura wuta su ƙara masa ƙaimi” na faɗi haka ne saboda ahalin gidanmu suna da ɗagawa sosai ta yadda suke ganin kamar ƙasƙanci ne a ce jinin gidan ya je yana aikin gwamnati,aikin ma koyarwa. Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin kamo tafin hannunsa wanda yake lutuf da tsoka sai taushi kamar na mace,hannun nasa ya duba da sauri na sake shi saboda ba tun yau ba ya yi min hani da hakan ba wai iya gare shi ba kawai a'a hatta ƙannaina maza ya hana ni raɓar su ko kuma taɓawa a tsakaninmu. Na sunne kai wasu hawayen na sake surnano min suna ɗiga kan farin hijabina. “Nafisatu?” ya kira ni cikin wani salo,ba tare da na ɗago ba na ce “ na'am uncle” “Me yasa ra'ayinki ya banbanta da sauran danginki? Me yasa kike son yin aiki alhalin mahaifanki sun tanadar miki komai na rayuwa?” Na ɗago na dube shi kafin na ce “ uncle kai ma ba ka son na yi wannan aikin jahadin na shiga ƙauyuka ina wayar da kan al'umma? Saboda me uncle? Kawai don iyayena suna masu arziki shi kenan sai na yi kwance na dogara da dukiyarsu? Me yasa ni ba zan yi aiki ba?” “ Saboda ke mace ce!” ya bani amsa yana kallon idona,ji na yi kamar ya watsa min ruwa zafi kawai sai na tashi na fita a guje ina gwanjin kuka.Ina shiga babban falonmu duk sai na tarar da ƴan uwana kuwa suna ta cece-kuce akan maganar,ɗakina na wuce direct na haye gado na kwanta rub da ciki amma abin mamaki sai na ji tamkar kan cinyar mutum ne kaina yake amma sam ban bai wa hakan muhimmancin ba na ci gaba da rera kukana,har na fi jin haushin rashin goyon bayan Uncle Salem kan na Daddyna.A hankali na soma jin ana shafar gashin kaina wanda ke luluɓe da hijabina,ido na soma lumshewa ba tare da na shirya ba yayin da kuma na soma sauke numfashi akai-akai.Ban sani ba ko na shiga duniyar mafarki ne ko kuwa zahiri ne amma sai na tsinci muryar wata dattijuwa na yi min gatana haɗi da bani tarihin ababen tsoro
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38