Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Bakin Ruhi Book 1 Complete Hausa Novel 1,244 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta markaɗe ni na huta” haka kawai na ji hankalina ya ƙi kwanciya da wannan aikin,sai nake jin kamar na je na shaida musu ban so. Bayan wajen minti talatin ina zaune sai ga Zuly ta shigo ,kallo ɗaya na yi mata na ɗauke kai. Ta zauna tare da soma magana ba tare da na tambaye ta ba,“sai haƙuri Luby,ni ma na fara gajiya sai dai ba a komawa baya.Kin ga a ranar da ƙawata ta haɗa ni da oga da farko iya aikin yi masa lissafi kawai ne nawa,amma sannu-sannu sai ya fara bijiro min da ainahin zuwan nawa.Cike da tako yayi nasarar kai ni kan shimfiɗarsa har sai bayan komai ya kammala ne na fahimci kuskurena,don da soyayya ya ɓullo min .Amma yana bani kuɗaɗe masu mugun yawa sai ya girgiza tunanina,sai kawai na biye masa kusan kullum in na zo aiki muna keɓewa yayin da shi kuma yake cika min jakata da ƴaƴan banki” “Ita kuma alaƙar tsafi?” na jefo mata tambayar. “Shi ne ya bani power ya kuma nuna min yadda ake yin komai” “To amma me yasa ba ki rabuwa da Alhaji ki auri oga ? Ai hakan ya fi nake gani tunda da dukkan alamu shi oga kina sonsa” Wani kallo ta yi min kafin ta ce “ki shirya za mu fita zuwa yawon ƙauyukan da za a soma aiki” “Aikin me fa?” “Na gina banɗakunan kan titi mana” ta bani amsa. Ko da muka fito tuni motar da za ta yi yawo da mu ta zo,haka muka shiga mu da wasu sauran ma'aikata.Yawo sosai muka yi muna duba wuraren da za a gina banɗakuna,wasu cikin kasuwa wasu kuma kan titi.Sai bayan sallar azahar muka dawo,Zuly ce ta yi wa oga bayanin komai kafin ta sauke ni asibiti. Ina shiga daidai nan Abba ya rufe idonsa ya soma bacci,bayan na gaishe da Ummah sai na zauna na tambaye ta jikinsa ta amsa ana ta samun ci gaba. Nan na wuni,har dare amma Abba bai tashi ba har likitocin sai da suka yi mamakin irin baccin nan da yake alhalin ba a yi masa allura ko magani mai sa haka ba.Saƙon Zuly na samu kan ina iya tafiya gidanmu ba sai na je can gidanta ba,da wannan na yi wa su Ummah sallama na je can gidan.A daren ne kuma na yi wani mafarki mai matuƙar firgitarwa,ga Abba nan yana kuka yana kiran sunana yayin da kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya sun ɗora shi kan garwashin wuta suna gasa shi tamkar wani tsire. A firgice na farka wanda yayi daidai da kiran Zuly,“ki fito ina ƙofar gidanku” shine abin da ta faɗa min ta kashe wayar. Cike da mamaki na duba lokaci,ƙarfe biyun dare ne.Amma haka na fita na same ta cikin mota,ina shiga ta fizge ta kuwa ta soma yin gudu kamar za ta tashi sama tambayar duniya kuma ta ƙi bani amsar abin da ke faruwa . Gidanta muka wuce,tana yin parking duk muka fito hankali tashe take jan hannuna zuwa ciki.Wannan dai ɗakin muka shiga wanda na yi laƙabi da ɗakin sirrinta,ko da muka shiga sai ta buɗe madubinta ta tsaga yatsanta jini ya soma zuba ta kamo nawa da niyyar tsaga shi kenan mijinta Alhaji ya shigo ɗakin yana salati tare da jefo mata tambaya “Zulaihat tsafi cikin gidana? Dama ke MATSAFIYA (Mrs SADAUKI) ce ban sani ba? Ai kuwa yau...” bai ƙarasa kai ƙarshen maganarsa ba Zuly ta jefa wuƙar hannunta tare da furta furucin tsafi nan take wuƙar ta sauka daidai tsakiyar ƙirjin Alhaji a nan take ya faɗi jini na yi masa malala...... My book is only 500 via 2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank DM +22795045822 [02/04 12:10] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*🧌🐲 ```LoVe aNd HoRrOr story```👽 By Chamsiya Laouali Rabo {MRS SADAUKI💫✍️} *SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a kan dukkan wani da ke son cutar da mu. *FCWA*☀️ ________________________ 07 Ban taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba,kisan kai ne aka yi a gabana ga gawa kwance cikin jini.Tsabar ruɗewa da na yi yasa na soma zagayen ɗakin ina ihu,yayin da ita kuma Zuly ta soma tsafe gawar tana barbaɗa mata wata hodar tsafi kafin ƙyaftawar ido gawar ta ɓata ko kumfan jini babu,a wannan lokacin ne na ƙara ganin bala'in da na tsoma kaina a cikinsa.Zuly ta nufo ni da niyyar kama ni amma na yi tsalle na koma can gefe ,idonta ta juye tamkar wata zakanya kafin ta soma yi min magana cikin wata irin murya “Luby ki zo mu wuce ba mu da sauran lokaci,in kuma kika jinkirta duk abin da ya biyo baya babu ruwana” Ina kuka ina ƙari na ce “amma Zuly kisan kai fa kika yi,mutum ne fa kika kashe kuma mijinki” “Babu ruwanki da wannan matsalar ki zo mu wuce” ta yi furucin tare da yin tsalle ta zo ta cabko ni muka tashi cikin iska kafin mu ratsa ƙofar da ke cikin mirror. A wani ɗaki muka bayyana,da na duba da kyau sai na ga wancan dai ne na ƙasar waje.Duk yadda na so na bijiro da zancen kisan kan da ta yi ta hana,a gaggauce ta tirsasa ni na shirya cikin kayan arna kafin mu fito.Yanzu ma buɗe mana mota aka yi muka shiga ,muna tafe ina duban hanya sai na ga wata ce aka ɗauka ba waccan ba.Mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu isa, wannan karon a tare muka shiga ɗakin taron mai ɗauke da ɗumbin jama'a daga ƙasashe daban-daban.Ciki kuwa har da oga shi ma ya haɗe cikin wasu baƙaƙen suit kamar sauran mazan,wuri muka samu muka zauna oga ya dubo inda muke zaune fuskarsa ta nuna alamun damuwa. Can kamar minti biyu wani zabaya ya fito sanye cikin jajayen kaya kansa ya ɗora wata hulla kamar ta sheɗan,gashin kansa da idonsa duk wasu iri ne kamar wani makaho haka ya ƙanƙance su yana ƙarewa kowa kallo ,da ya zo kaina sai ya tsayar da dubansa gare ni.Gabana ne yayi wani irin mugun faɗuwa ,so nake na kauce idona amma tamkar wacce aka yi wa dabaibaye na kasa. “Mansoor fatan ka yi wa ɗalibarka bayani?” shi ne abin da ya faɗa . Muryar oga na ɗan rawa ya ce “a'a tukuna dai Boss ” Bai ce komai ba sai ya zauna kan kujerar ya soma yin wasu maganganu da ban gane su ba saboda kogin tunani da na abka,ban farga ba sai da na ji Zuly ta zungure ni sai na dawo hayyacina nan kuma na ƙara jin wani zancen banza wanda kuwa hankalina ya kasa ɗauka. Oga ne ke bayani kamar haka “Luby a family muna da wata ƙa'ida,babu virgine a tsarin tafiyarmu in ma ta shigo to dole a yi amfani da ita don kawar da budurcinta.In irin wannan damar ta samu to Boss ne yake yin wannan aiki ,kamar yadda tsarin yake zai yi amfani da ke a gaban dukkan family bayan nan kuma sai ki karɓi zoben ƙarfin iko da kuma madubinki wanda zai sauƙaƙa miki yin balaguro zuwa ƙasashen duniya da kuma in an tsara meeting” Wata irin bazawarar dariya na yi,don abin jin shi na yi kamar wasar kwaikwayo sai na miƙe tsaye kamar mahaukaciya ina mai ci gaba

Table of Contents

Chapters

38 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});