Chapter 29
Chapter 29
ya kore ni ya ce ba zan koya ba,ya ƙanƙance ido ya ce “mu nan garin ba a kashe ƙwari ban san daga wane wajen kuka fito ba” sai kuma ya fita ni ma na take masa baya,ina kallon yadda ya bi Inna A'i da wani mugun kallo kafin ya fita. Ɗakin na rufe bayan na gama kallon yadda har a wajen sai da yayi ta dube-dube. Ko da na juyo sai na ga tuni ta shiga toilet,sai na jira ta fito sannan na shiga ni ma na yi alwala na fito na yi sallah sannan na zauna na yi Azkhar ɗin safe. “ Ina kwana Innarmu? Ya ƙarfin jikin naki?” na faɗa bayan na gama komai. “ Alhamdullah ai na ma warware,ina ga kajin jiya ne suka buga min ciki don na yi doguwar tafiya” ta bani amsa . Na ce “ ai kuwa dai ,yanzu ki kwanta ki huta dai zuwa an jima sai ki yi mana girki” Ta ce “ a'a na fa warke yanzu zan shiga kitchen“ tana gama faɗa ta miƙe kuwa,ni kuma na ɗauki wayata nan na ci karo da miss call ɗin Uncle Salem ya fi goma duk yayi su ne bayan na kashe kiransa na jiya.Ɓangaren saƙo na duba sai na ga text ɗinsa yana bani haƙuri tare da alƙawarin ba zai sake ba. Kiransa na yi sai dai sam lambar ba ta shiga,duk sai na ji babu daɗi haka na kunna data na soma yin shat ban ajiye wayar ba sai da na ga ta kusa mutuwa sannan na saka ta caji.Ina shirin shiga wanka na ji ana shelar ana son ganin dukkanin malaman da suka zo a ɗakin meeting da ke cikin makaranta da misalin ƙarfe takwas da rabi . ★Uncle Salem Cikin kaɗaicin son kasancewa da Nafisa ya soma bijiro mata da sabbin abubuwan da za ta fahimci shi mijinta ne amma da dukkan alamu ya ga sam ita a iya uban kawai ta yi masa matsuguni.Jin ta kashe masa waya yayi tunanin kunya da kuma fushi ne yasa ta datse kiran,hakan yasa yayi ta jera mata su da ya ga ta ƙi ɗauka sai ya tura mata text tare da kashe wayar ya rungume pilow.Zuwa yanzu haƙurinsa da juriyarsa sun yi ƙasa sosai,yana matuƙar son kasancewa da ita a duk cikin sati ranar juma'a da asabar kawai a bai yin azumi duk don kare mutumcinsa.Sau ɗaya tak ya taɓa neman auren wata wacce dama ita ce take haukan sonsa,amma an zo yin auren aka fasa saboda bai da wani asali. Idonsa sun kaɗa sun yi jajur saboda abu biyu da suka haɗe masa, feeling da kuma fushin Naf wanda a duniya in akwai abin da yake guje ma to bayansa yake shi yasa a kowane lokaci yake yi mata abin da take so.Ko da kuwa iyayenta sun so nuna masa illar gatan da yake yi mata sai ya ce musu har yanzu Naf yarinya ce.Sai dai a jiya da Daddy ya ce masa ya ci a ce ta tare da kuma yadda ya ga surarta cikin doguwar rigar da ta lafe jikinta duk ta fitar da shap ɗinta sai yake ji a ransa eh za ta iya ɗaukar nauyin buƙatarsa. Juyi yayi ta yi a daren,da ya ga dai sam baccin ba fa zai zo ba sai ya miƙe ya je watso ruwa tare da zama kan dadduma yayi ta lazumi bayan raka'o'i biyu da yayi.Sai daf da asubah ya samu bacci,amma duk da haka ana kiran sallah sai da ya je masjid da ke nan cikin Company ya dawo ya ƙara komawa bacci.Bai farka ba sai wuraren ƙarfe goma na safiya,wani wankan ya sake tare da shirya wa cikin wando tree quater na sojawa da kuma rigarsa t-shirt ita ma ta kakin soja.Bai ɗora hulla ba ya dai saka farin gilashi kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ta aiki da kuma wayarsa.Sai da ya fito a hanya ne ya kunna ta,bayan ya shiga mota ne ya ga saƙon cewa Nafisa ta so kiransa amma ba ta same shi ba.Ya ɗan saki murmushi yana jin zuciyarsa ta yi sanyi ko ba komai yana da tabbacin ta sauko daga fushin da take.Kiranta yayi har sau biyu,a na uku ne Inna A'i ta ɗauka ta shaida masa ta fita. ★ƘWARGWAM Ko da na fito daga wanka tuni Inna A'i ta soya min dankali da kuma ƙwai,na yi zaune na ci na ƙoshi kafin na jawo kayan kwalliyata na shafa mai da turare har da hoda.Bayan nan na zaɓo doguwar riga ta tambaya ƴar côte d'ivoire,sosai ta amshe ni sai na zaɓo hijabi da jaka da kalmi duk waɗanda za su hau da ita. Ina shirin fita ita ma Inna A'i ta fito daga kitchen hannunta riƙe da kwanon miya na jiya,ta ce “ ashe ba ki ci abincin nan ba dubi yadda duk yayi tsutsotsi ya lalace” Na dubi cikin kwanon na ga babu kyawun gani manyan tsutsotsi ne ke ta yawo suna shige da fice cikin ragowar naman kajin.Da mamaki na ce “ amma kuma abincin har ya isa lalacewa haka?” “ Ni ma haka na ce,ko ƙila zafi” Inna A'i ta faɗa . Na ce “ kawai ki zubar ki wanke kwanukan sai ki mayar musu ,ga key nan in za ki fita ki rufe ɗakin na tafi sai na dawo” “Allah ya tsare hanya” Na ce Amen ina mai yin addu'ar fita daga gida.Kamar yadda ƴan magana ke cewa in ka yi boko to ƙauyancinka ragage ne hakan yasa duk da ban san ko ina na makarantar ba haka na dinga karanta duk wani allon sanarwa da na gani har na dace da ɗakin meeting. Da isa ta sai na tarar duk kamar ma kowa ya zo ni ake jira,sallama na yi tare da samun wuri na zauna kusa da wata wacce na ga tana sanye da hijabi saɓanin sauran matan da ke wurin duk sun ci uban ado an ɗora mayafi. Babu jimawa kuwa manyan namu suka suka shigo,duk muka miƙe tsaye don nuna girmamawa kafin mu zauna. Ɗaya daga cikinsu ne ya soma yin magana ,su biyar ne huɗu maza sai mace ɗaya. “Yawwa da farko muna yi wa baƙin malaman School Ƙwargwam Barka da zuwa,kamar yadda kuka sani duk faɗin garin nan wannan ita ce kawai makarantar da ake koya karatun boko da sauransu...” sai yayi wani murmushi wanda yake ɓoye wata manufa kafin ya ci gaba da cewa “ Ƙauyen Ƙwargwam na zagaye da ƙauyukan maƙota guda huɗu,shine a tsakiya sannan dukkan sauran ƙauyukan nan a wannan makaranta tamu mai farin jini suke zuwa ɗaukar darasi.Kar dai na cika ku da surutu,ina son waɗanda za su koyawa ƴan sakandari su koma layin nan duk su zauna” ya nuna wani layi,nan duk wasu daga cikinmu suka ware kansu nan ne na fahimci wato ba iya primary ba ce kenan school ɗin. Kamar kuwa ya karanci tunanina sai ya ce “ makarantar ta kashi gida uku ne,da farko Sakandari sai ya nuna layin malaman kafin ya ce wannan shi ne Principal ɗinku ku da ɗalibanku,ƴan primary kuma ga naku shugaban headmaster sai ya nuna mutumen nan na jiya da ya kawo min abinci shi kuwa har da yin wani murmushi.Ina so duk ku basu girmansu,ni
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38