Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Hauwa Kulu Book 2 Complete Hausa Novel 1,205 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

hudu-biyar basu zo ba. A wani dan tsakani da ya kasance sun kusa zana jarrabawar karshe a MBBS Madina ta baiwa Sarham iznin fara zuwa zance gidan su, ba don komai ba sai don iyayenta su san da zaman sa, kasancewar soyayyar tasu iya makaranta suke yin ta ba wanda ya san shi a gidan su har zuwa lokacin banda Yayan ta Osman dake zuwa kawota da daukan ta. Zuwa na farko, na biyu dana uku Alhaji Attahiru ya fahimci akwai mai zuwa wajen Madinahr sa, Hajjah Ramlah ma ta gaya masa wani ya fito neman auren Madinah amma bata san ko waye ba, saidai ga dukkan alamu Madinah tana yi da shi, ko daga girke-girken da take faman yi masa in zai zo. Daddy ya umarci Madinah data turo masa yaron dake zuwa wajen ta yana so zai yi magana ta gemu da shi, ba tare da tunanin komai ba a washegari Madinah ta gabatar da Sarham a tankareren falon mahaifin ta, daga nan ta basu wuri don su gana. Sarham yayi wani kuskure zai ce ko katobara, koda yake a wurin sa is normal, wato yawo da farar jallabiyya ta larabawa a garin Jeddah, maimakon da zai je gun siriki yayi shiga ta cika ido da kima sai yasa jallabiyyar sa abinsa wadda taji wanki da guga da turaren sa na Oud Abyad. Kallo na farko da Alhaji Attahiru yayi masa yaga yarintar sa da rashin cika ido, sannan kuma babu tantama dan talakawa ne ko daga sittirar jikinsa amma duk da haka bai yanke hukunci daga abinda ya ganar da kansa ba, sai da ya tambayi Sarham. “Yaro kai dan ina ne?” “Kano” “wane gari a Kano?” “Shanono” “Waye mahaifin ka?” “Prof. Abbas Shanono” “daga jin Farfesa malamin Jami’a ne kenan?” “Eh!” “to kai kuma meye taka sana’ar?” “dalibi ne ni” “Dalibi dan Farfesa, ilmi na dukan ilmi, amma dame ka shirya rike min ‘ya ta yaro da kai haka? Ko bata fada maka daga gidan data fito ba?” Sarham ya kasa hadiyar miyau, don bai zaci wadannan kalaman marasa kan gado daga babban mutum mai ilmi kamar sa ba, Daddyn Madinah ya cigaba da cewa “yaran zamani in zaku yi abu sam sam ba kwa tunani, yo me na sama ya ci bare ya baiwa na kasa? Yaushe zan ajiye ‘ya ta zaman jiran girman ka da yin arzikin ka kafin inyi mata aure? Ai kawai yaro kaje ka nemi daidai kai diyar malaman makaranta”. Sarham hatta jijiyoyin kansa saida suka mimmike, suka fito rada-rada, tun kafin ya tashi a wajen ya gayawa ran sa ya hakura da Madinah ko itace autar mata, don mai taba Abban sa ya zauna lafiya a hannun sa sai dukan ruwan sama. Shima don ba zai iya rike shi daga taba jikinsa bane. Duk da haka wannan tsohon baturen zai ce ko tsohon nasara ya ci arzikin Madinah-Munauwarah. Amma da ba haka ba?! Da yayi masa raddi daidai da nasa. Ya girgiza kai ya mike. A kullum Madinah na cin alfarmomin sunan ta a wurin sa, wato, yana son garin Madinah sosai, duk sati biyu yake ziyara Masjid Nabawy daga Jeddah, don haka ko cikin hira yana gaya mata cewa tana cin albarkacin sunan ta na Madinah garin Manzo, garin da ya zamewa Ma’aiki (SAW) mafaka (refege) kuma wajen yin hijira daga inda yayi masa kunci, don haka sau tari ya kan ce da ita, ko sunyi aure ta bata masa rai komai girman laifin zai iya yafe mata shi saboda sunanta, zata cigaba da cin albarkar city of Madinah, za kuma ta cigaba da samun wannan alfarmar har gobe a wurin sa. Don haka bai ce komai ba baya ga godiya ga mahaifin Madinah da barin gidan su ba tareda ya tsaya Madinah ta ga yanayin sa na lokacin ba. Shi uban da kansa ya gaya mata ya sallami wannan yaron, in bata da hankali shi da hankalin sa, ba daga turu aka fito da shi ba, kuma ta sani daga yau ta bar King Abdul Azeez University kenan, don ya fahimci irin ‘ya’yan talakawan nan ne masu hurewa ‘ya’yan manya kunne da ‘I love you’, su dau advantage na iyayen su don su samu abin yi mai maiko, in sun kama kasa su auro daidai su, ‘ya’yansu su koma na ladan noma. Madinah couldn’t control her tears, ta bi bayan Sarham da gudu amma bata cimmasa ba. A washegari kuma Babanta bai barta ta koma [KAU] ba, yasa Abubakar ya karba mata ‘transfer’ zuwa Yamboa ya kuma je ya kaita da kan sa, yace in ta kara neman wannan yaron ko a waya kota wata kafar sadarwa kowacce iri ce zai saba mata ko ya bar kasar bakidaya da ita. Madinah na matukar son birnin Jeddah don anan aka haife ta, amma haka Baban ta ya raba ta da shi saboda Sarham zuwa Yamboa. Madinah na matukar son Sarham, so irin wanda bazai misaltu ba, amma haka ta hakura da shi saboda ta yiwa mahaifin ta biyayyah. Madinah na matukar son mahaifin ta shiyasa ta zabi farin cikin sa a kan nata, wato ta zabe shi akan soyayyar dake zuciyar ta, ta kuma bi umarnin sa. Wannan kadai ya nuna Madinah mai biyayyar iyaye ce ta kuma ci ribar biyayyar tun a lokacin, domin duk da zuciyar ta tafi dare duhu, amma haka mahaifin ta yayi ta saka mata albarka, yana ankarar da ita illar auren ‘ya’yan talakawa gasu yara masu gata kuma ‘ya’yan manya kamar ta, yace basu da alkawari ‘yan taking advantage ne kuma basa juyuwa ta sauki ga matan su, taurin kansu kadai dafadin rai ga matayensu sai ta gwammace kida da karatu, sannan basa taba zama da mata daya. Duk Madinah tayi biyayyah ko a fuska bata taba nunawa mahaifin ta har lokacin Sarham yana ranta ba. ta kuma san duk abinda ya fada akan Sarham ba haka bane, Sarham akasin duka wadannan expectations dinne. Sai ta tattara komai ta fauwalawa Allah ta maida hankali ga fuskantar karatunta a jami’ar Yamboa, ta manta da komai, a shekara daya da Sarham ya gama nasa karatun itama a shekarar ta fita daga Yamboa University, ta fita da flying colours a specialization nata, ta zama cikakkiyar likitar fidar ido (ophthalmic surgeon) mai lasisin yin aiki a kasar Saudi-Arabia. Shima Sarham ya fiddo nasa kwalin daga (KAU), ba tare da sanin me kowannen su yake ciki ba. Daga nan ya tattara ya koma gida. Inda ya kama aiki a karkashin gwamnatin jiharsu. A lokacin ne AVM Adamu Alkali ya fito neman auren ta. Ba kuma ta kanta ya bi ba, ya tafi ne kai tsaye ta kan mahaifinta, shikuma a sanin irin biyayyar da Madinah keda ita bai bata lokaci wajen neman yardarta ba, saboda wannan shine daidai da ra’ayin sa, irin mijin da yake mata fata yake mata addu’a, gashi Allah ya bata a lokacin da ya dace tayi aure, miji wanda bazai yi kaico da aura masa ita ba, wato na saman da ya ci ya hantse yake watsowa na kasan sa, dama duk wadanda ke jikin sa koda sun kasance suma masu wadatar ne. Don haka Daddy bai ja lokaci mai yawa ba wajen sanya auren Madina da AVM (Air Vice Marshall A. Alkali), wanda

Table of Contents

Chapters

36 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});