Chapter 15
Chapter 15
laifin da suka yi masa ba. Mama duk suka saka ta a duhu, ta rasa gane komai, sai da Sumayya ta share hawayenta ta gaya mata komai cikin muryar kuka. Mama ta kasa tuno mutanen da ake matsalar a kan su, ta san dai ire-iren jama’ar sa ne da baya rabo da kyautatawa, da irin jajibe-jajibensa, amma hakika ta harzuka da abinda Surayyah ta yiwa Yayanta, bata san ko su waye wadanda yake turowa kudin ba duk wata tun daga Jeddah ba, ba kuma tareda ta damu da ta sani ba, amma tunda har ya dauki tsahon shekaru uku yana turo musu kudi duk wata bait aba mantawa ba to masu muhimmanci ne a wajensa, kasancewar ta san halin sa akan son tamakawa mutane da son kyautatawa na kasa da shi da marassa lafiyansa, sai hakan bai zame mata wani sabon abu cikin halayen dan nata Sarham ba, Mama tace. “Da gaske wannan cin amana ne, kuma zai fi bakanta masa rai ne kasancewar mutane mafiya kusanci da shi ne suka yi masa”, ta dube su cikin fushi ta sake cewa “a duniyar nan in dan uwanka ciki daya bai rike maka amana ya rufa maka asiri ba, in bazaku kashe ku rufe kai da shi ba, ba tareda ko iyayen ku sun ji ba, waye zai yi maka? Sannnan da wa zaka yarda a duniya, kuma da wa zaka aminta? Kin yi kuskure Surayyah, ba dan uwa irin naku ake badawa kasa a idanu ba, saboda shi din dan uwa ne har dan uwa guda har da rabi, ko in ce Yayan da babu irin sa, ko don son da yake muku da kulawar sa da kyautayinsa gare ku”. Surayyah ta gama dukkan nadamar da mutum zai iya, a lokacin da yasan bai kyauta ba aka kuma ankarar dashi. Cikin kuka ta ce. “Mama don Allah ki bashi hakuri, na tuba na bi Allah na bi shi, zan biya shi duka kudin sa da zarar na fara aiki, dama ban kashe da niyyar bazan biya ba, kawai ya zo ba ‘notice’ dina ne, nayi niyyar in bata ta kai musu kafin lokacin zuwan sa, wallahi zan biya shi”, Mama ta wani harareta ta ce “ta baya ta raggo. Duk abinda zaki biya shi yanzu bazai karba ba, kuma bazai masa amfanin komai ba. Surayyah an yi bokon banza tunda shi ya koya miki son abin duniya, kayan kwalliyarbanza kayan kwalliyar hofi, saboda Allah da me iyayen ki suka rage ki banda son kyale-kyalen ki na banza da wofi da kika dorawa kan ki tun shigar ki jami’a, da son lallai sai kin hada kafada kin goga da kawaye da suka dauki karyar rayuwa suka dorawa kan su? Kullum ina nuna miki ‘reality’ akan barin sayen abubuwan nan masu tsada da suka fi karfin aljihun ki ko na iyayen ki, kina ganin kamar ni kaina ban waye ba, tunda bana sayen turare su ‘designer’ sai Humrah sai Oud, har ni zaki nunawa sanin ya kamata akan rayuwar duniya Surayyah? Yaushe aka haifeki har kikayi wayewar??” Mama tayi ta fada ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, daman tana cike da halin Surayyah din kan irin tsarin rayuwar ta mai tsada, fadan da Sarham bai tsaya ya yi musu ba don bacin rai shi Mama tayi ta yi musu ta wanke Surayyah tas. Wankin babban bargo. Surayya dai sai hakuri take baiwa Mama ganin har tafi Sarham daukar zafi da al’amarin. Aka ce dan uwa rabin jiki, ganin yadda duk ta muzanta sai ta koma baiwa kanwar ta Sumayyah tausayi, Summy ta ji kamar a maida laifin ya koma kanta, ita a cigaba da yi mata fadan ita kadai, ta koma taya ta suka yi ta baiwa Mama hakuri da rokonta kan ta bashi hakuri in ya dawo, sunyi alkawarin bazasu sake yin kuskure makamancin wannan ba, Sumayyah dai ta ari laifin suka yafa shi tare da ‘yar uwar ta. **** **** **** SARHAM D a ya fita cikin zafin rai, wata motar Abbansa (Peogeot 504) ya dauka wadda tun saukarsa da ita yake amfani, kasancewar bai kai ga sayen motar kansa ba tun dawowar sa, ya fizgeta a guje ba tareda ya san wajen zuwa ba, yana dai so yayi nesa da gida don shi kansa ya san bai iya fushi ba, baya son ‘yan kannen sa su ga launin fushin sa mara kyau, ana he’s jovial amma in yayi fushi kamar zawayi yake komawa don rashin hakuri, musamman akan Surayyah da baya son wasu halayenta. Sai ya samu sitiyarin nasa na sarrafa shi, ya dauke shi yayi hanyar titin da zai sada shi da kofar Na’isa. Yana tafe yana gayawa kan sa ya yafewa Surayyah duniya da lahira, ya yafe mata, amma hakika ta ragewa kanta matsayi a idon sa. kuma ‘outing’ din da yayi niyyar fita dasu zuwa Dam, don tayata murnar kammala degree ya gayawa kansa ya fasa. Duk da Mama ta ce zata bashi hakuri inya dawo, amma hankalin su su duka bai kwanta da fitar sa cikin fushi ba da kuma ganin tsayin lokacin da ya dauka bai dawo gidan ba. Ya isa kofar Na’isa da yamma lis, ya karya kan motar sa zuwa titin da zai kai shi lokon su Hauwa, yana tafe yana tunane-tunane akan su, ko a wane hali zai same su? Ko Hauwa ta gama makaranatar sakandire yanzu? Ko yaya suke rayuwar haka babu tallafin kowanne namiji? Ko Baban su Malam Bilyaminu ya dawo? Ko yaya idanun Hauwa? Allah Masani! Bai san meyasa zuciyar sa ta damu da al’amarin su ba, take kuma daraja su, yana saka damuwar su a ran sa in ya tuna a hannun sa Hauwa ta karbi shaidar makanta da lasisinta, daga zuwa neman magani. Shi ya san da ace ba shi yayi mata aikin nan ba, da bazai damu ba don an samu mishkila. Har gobe kuma ya kuma kasa yafewa kan sa a kan makancewar Hauwa, ya ki cire abun a ran sa, duk da ya san kaddararta ce, shima kuma ba yin kansa bane amma har gobe Sarham yana ganin negligence dinsa ne wato (sakacinsa da rashin iya aikin sa), su suka janyo har Hauwa ta kai ga rasa idonta completely. Haka tunda ya tafi Jiddah yau shekara uku bai taba kasa tuno su ba kullum, har Allah-Allah yake a yi albashi don kawai ya tura musu, ranar Allah dai-dai ce da baya tuna su, tare da yi musu addu’a da fatan alkhairi. Ya san kuma kudin da yake aiko musu daga albashin sa zai ishe su kananan bukatocinsu na yau da kullum da makarantar Hauwa. Bayan motar Abban sa da ya tuko, shake yake dankam da tsarabar su Inna rankatakaf! Wadanda tun daren jiya ya saka su a mota yana jiran ya samu nutsuwa ya je kofar Na’isa, yayi ido hudu da Innar sa Safiyya, don ba Hauwa yake kewa ba Inna yake kewa. Eh mana, Hauwa da bata son sa kuma take kullace da shi. Hauwa danger Hauwa hukuma. Har sabuwar waya nokia karama ya sayowa Inna, da alkawarin yanzu in ya koma Jiddah kai tsaye zai ke kiran su. Idan har Hauwa ta kammala sakandire da kyakkyawan sakamako ya fara tunanin bincike akan yiwuwar cigaba da karatun ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36