Chapter 22
Chapter 22
sani akan ilmin zaman aure da zamantakewa da ake yi a kasa mai tsarki ko na likitanci komai nisan gari zaka samu Dr. Madinah na kokari ta halarta, wannan ya karawa Madina (exposure) akan ilmin data ke da shi. Domin bata tsaya ga bangaren karatunta na likitanci kadai ba, a’ah, tana kara fadada ilmin ta a kan zamantakewar aure da zamantakewar al’umma, tana da yawan rubuce-rubuce (wadanda bata wallafawa) akan sha’anin mata da aure musamman da bata fara aiki da kowanne asibiti ba a lokacin, kullum cikin bincike take a yanar gizo kan yadda zata kara inganta kimar ta a gidan auren ta. Ko wata uku ba’a rufa ba da auren su, Madinah ta fahimci yaron ciki na wata guda a tare da ita. Ciki irin silent dinnan (mara laulayin nan), cikin data kira da suna DAN SO. Yo dan ta da Sarham ai dole ta kira shi DAN SO wanda tarihin soyayyar shekara goma ne ya samar da shi ‘sharp-sharp’ kamar a dokin kofa tayi tuntube da cikin sa. Koda cikin ya soma girma ya shiga watanni biyar bai hana ta komai daga harkokin ta ba, amma yasa ta fasa karbar tayin aikin da ta samu da Dr. Siddiqah hospital, domin ta zauna a gida ‘fully’ ta raini dan So, ta kuma baiwa ubansa kulawar da zata gusar da hankalin sa daga kan sauran mata. Addu’ar ta kullum Allah yasa abinda ke cikin ta namiji ne, tana fatan yayo kamannin Sarham, da halayen sa da kwakwalwar sa. cikin ‘yan watannin da ta kasance kullum a gida Madinah ta kara kaimi wajen ganin ta samarwa kanta kyakkyawan matsugunni a zuciyar Sarham, ko dama matsayin ta mai girman ne, to ta kara girman matsayinta ta hanyar kula da shi da bukatocin sa, ta tsare masa cikin sa, ta kware wajen iya girke-giren zamani dana larabawa, ta mallakawa Sarham duk wata kauna, soyayya, kulawa da yardar da diya mace kan yi wa namiji. ‘Yan gidan su Madinah na yawan zuwa gidanta, haka Daddy din ta da kan sa sai ya dauko Hajjah Ramlah a gaban mota ya tuko da kansa su zo ganin ta, musamman da cikin ta ya soma girma, dokin su ga haihuwar Madinah kamar a kan ta zasu fara samun jika bayan kuwa jikokin su sun kai goma daga yayyen Madinah, don cikinsu Usman ne kawai bai yi aure ba. Amma a wajen Hajja Ramlah da Dr. Sorondiki na auta Madinah na musamman ne tunda ko cikin ‘ya’yan su ita din ta musamman ce. Don haka sayayya sosai ake ana tarawa don jiran haihuwar. Cikin Madinah na da watanni takwas Hajjah Ramlah tace a dawo da ita Sorondinki ta haihu a can, ita bazata iya zamar mata jego ba (zaman dabaro), da farko Sarham yace bai yarda ba amma Mama ma sai tace a kai ta, ai haihuwar fari ce, normally a wancan lokacin ana zuwa wankan gida. Don haka bada son ransa ba ya fara ma Madinah shirin tahowa haihuwa, don dama sun riga sun gama sayayyar haihuwar su tuntuni, shi yayi, su Daddy sun yi, Sumayyah ma ta tara kayan baby da yawa iya karfin ta ta bashi da zasu taho, koda bata yin Madina tana maraba da isowar dan ta ko ‘yar ta daga Bhaiya. Sarham yana cike da damuwar yadda zai rayu a gidan su shi kadai ba tareda Madinah ba. Shi ya kai Madinah gun kakanninta, weekend kawai ya samu yi tare da su Mama ya koma Jeddah. Tafiyarsa da sati uku Madinah ta haihu, ta haifi lafiyayyar diyar ta mace, mai kama da ita, amma kalar fatar jikin da bafulatanar sumar ‘yan Shanono yala-yala ta Sarham ce, Surayyah ce ta fara kiran sa tayi masa albishir, cike da doki. Sannan Mama ma ta kirashi don duk suna asibiti tareda ita aka yi haihuwar, Daddyn Madinah tuni ya fara shirin tahowa Kano tarbar amaryarsa da aka haifa ranar Laraba, “Laraba Tabawa Ranar Sa’a” inji Haj. Kulu. Tana mai jan hancin yarinyar dan sirit da shi. Ranar da Daddyn Madinah da Sarham suka sauka a Kano kwana shidda cif da haihuwar, da yammacin ranar ya je gidan su Madinah a Sorondinki ya dauki yarinyar yana kallon ta da wani irin paternal love, kafin Madinah ta fito daga daki, ta sha ado, kamar ba itace ta dawo daga kofar lahira kwana shidda a baya ba, Sarham ya daga kai yana duban ta da wani irin murmushi, amma sai me? Sai kwakwalwar sa ta gaya masa cewa kawai ya saka ma baby din Madinah suna HAUWA’U ya dinga kiranta da Maijiddah, in the memory of his lost blind sister (miskiniya KULU). Madinah ta fito ta same shi da yarinyar a hannu amma yayi nisa cikin tunani, yana murmushi shikadai, sai da ta sakala hannayen ta a wuyan sa ya dawo hayyacin sa, ya sumbaci goshin yarinyar itama Madinah ya sumbaci goshin ta, Madinah duk ta kumbure a hakan ma ta dan sace, “an sha gumurzun haihuwa an zama uwa”, da ya dube ta yaga yadda hancin ta da bakin ta suka bubbude leben ya zama tafkeke saiya fashe da dariya. Madinah ta san me yake yi wa dariyar don yanzu itama ta gama kallon kan ta a mudubi kamar ta fashe da kuka, amma wannan yasa ta kara kaunar Hajjah Ramlah, ko ba komai ta ga yadda ta kawo ta duniya ba wasa bane, ta kuma kara girmama lamarin ta fiye da na Daddyn ta. Yo Sarham yana can Jeddah cikin ofishin sa yana shan rabar AC tana labour room tana gumurzu kamar ta sheka barzahu. Kwafa tayi ta cuno bakin gaba tace “ai na gama daga wannan babu kari” Sarham ya sake darawa ya ce “ah haba Madam Dr. yaushe aka yi daren garin zai waye? Yanzu muka fara saka kwallo a raga, sai kin yi dozen Hajjaju wannan ta ladan noma ce, ki rubuta ki ajiye na gaya miki” ya hada su ita da jaririyar ya rungume su, yayi musu kyakkyawar sumba a bakunan su, sannan ya yi mata sannu da sauka, ya kuma saka mata albarka, daga bisani yace. “Allah ya raya mana Nana Hauwa’u, AKA Kuluwa, Kulun Majadun”. Madinah ta zaro ido ta ce “sunan tsofaffi zaka saka mata? Ka rufa min asiri don Allah ka sa mata ko sunan Sumayyah mana”, yace “Sumayyah ce ta taya ni haihuwar ta? ko sanda nake shan yakushi da cizo a Riyadh Sumayyah ta zo ta taimake ni?” Madinah ta rufe ido cikin jin kunya tace “kai don Allah SARHAM!” Yace, “of course, sunan da na ga yayi min daidai kenan, Hauwa’u, Hauwah uwar al’ummar duniya, Hauwa uwar matan duniya bakidaya, uwar bil adama”. Sai da ya kama hanya a mota zai koma gida yana cikin matsanancin nishadi, akwai contentment mai yawa on becoming a father, ya tambayi kan sa “why HAUWA? Me yasa sai Hauwa zai sakawa ‘yar sa? Bayan in don yake tuna su ne, sunan Inna ya kamata ya saka wato Safiyyah? Murmushi yayi, a lokacin yazo zai wuce ta kofar Na’isa, yana kallon kofar wadda aka sake ginewa aka sabuntata, bayan hawan sabuwar gwamnati, sai kawai ya tuna da Malam Isa, kawai sai ya karya kan motar sa ya nufi gidan Malam Isa mutumin sa. Tun daga nesa ya hango ginin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36