Chapter 14
Chapter 14
gaba da baya kasancewar auren zumunci ne a tsakanin iyayen ta, sun kuwa nunawa Hajjah Ramlah zumuncin da karah, don kwansu da kwarkwatarsu zuri’ar Sorondinki sun yi dafifi a ‘main house’ din su, don halartar yinin bikin Madina a ranar da aka daura aure. Iyayen Madinah su ya kamata a kira masu Kano, ba kuma wai sarauta ce dasu ba domin iyayen ta da dangin ta na uwa dana uba wadanda duk abu guda suke, sun kame duk wasu madafun iko na Kano. Sai bayan daurin aure ne, da ya samu ya huta ya samu nutsuwa bayan mutane sun watse, a daren daurin auren ya samu ya zauna da Sumayyah yana tambayar ta yaya labarin su Hauwa da Inna? In ce ko tana zuwa tana gano masa su da baya nan kamar yadda ya bar mata sallahu? Kuma in ce ko duk wata tana kai musu sakon da yake aikowa ta hannun Surayyah?” Ya tsare ta da kaifafan idanun shi ganin yanda tun bai gama magana ba Sumayya ta shiga cikin rudani da damuwa, na farko dai itama ta mance da su Hauwa, bata kara tunanin zuwa kofar Na’isa ba tun bayan tafiyar sa, na biyu ga abunda Surayyah tayi, wanda ke nufin dukkan su sun zama masu laifi ga Bhaiya, sai dai a ce laifin Surry ya take nata wato, sawun giwa ne ya take na rakumi. To amma ta kwana da sanin halin Bhaiya baya son yayi maka tambaya wadda a wurinsa mai muhimmanci ce ka zuba masa na mujiya nan da nan zai harzuka, sai duk ta daburce, ta hau inda-inda da in-ina, tana son cewa ba ita bace Surayyah ce, tana kuma son kare Surayyar. Kawai sai jikin sa ya bashi babu gaskiya acikin al’amarin ta, ko wani abu mummuna ya faru dasu Inna a bayan tafiyar sa, gabansa yayi mummunan faduwa ya fiddo wayar sa ta tafi da gidan ka daga aljihun gaban farar shaddar shi Wagambari wadda ta sha maikon sabunta, Ango sosai, sai walainiya yake yi a cikin farar Excelcior din, yasa dan yatsan sa daya yana dannawa Surayyah kira, tana amsawa yace ta same shi a karamin falon Mama. Tun daga jin kiran sa itama Surayyah ta hau numfarfashi ta san ta gama barewa, a lokacin suna tare da wanda zata aura a harabar gidan su wato Engnr. Aliyu Barde, wanda dan abokin Baban su ne, iyayen su suka hada su, Aliyu ya fahimci hankalin ta ya rabu gida biyu tun bayan amsa wayar ta, yace “me ya faru ne a wayar?” Surayyah ta dauki excuse daga wajen Aliyu kan Yaya Doctor dinsu yana kiran ta a cikin gida, ko zai bata minti goma? Egnr. Yace ai tafiya ma zai yi don akwai inda zashi, don haka suyi sallama kawai, sai wajen jibi zai dawo. Don lokacin an saka musu lokacin aure. Bayan sun yi sallama ya tafi, Surayyah ta taka zuwa cikin gida tana tafe salalau-salalau kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Sarham har ya gaji da jiran shigowar ta ya mike zai biyo bayan ta yana huci sai gata tana shigowa. Tun kafin ta zauna ya jefo mata tata tambayar kamar yadda yayiwa Sumayyah game da sakon su Inna da yake turowa ta account din ta duk wata, yau shekara uku bai taba fashin turowa ba, wanda yace a dinga kaiwa mutanensa na kofar Na’isa. Surayyah tayi zuru-zuru ta yi wiki-wiki da ido tayi masa shiru, kiris ya rage ya mare ta, don baya son halin ko’in kula in yana maka maganar da a wurin sa mai muhimmanci ce, kayi shiru ka zuba masa ido kamar tsohon maye kana kallon sa. Da kyar Surayyah ta motsa baki ta ce cikin rawar murya “I’m sorry Yaya Doctor!” Ta kara cewa “I’m so sorry” “Sorry for what?!” Ya tambaya (in exclamation). Sumayyah kanwarta wadda ta soma hawayen ganin yadda ransa ke hauhawa wajen baci tun ma kafin yaji laifin da Surayyah tayi masa, taga basu da mafita banda ta gaya masa gaskiya, sai tace. “Bhaiya, maganar gaskiya ko sau daya bata taba bani komai tace in kai musu ba, sai ranar da ka zo take gayamin ai kayan kwalliya take saye da kudin, ni ma kuma ban taba zuwa duba su ba, wallahi na manta hanyar gidan sam, lokunan (are complicated), don haka dukkan mu mun yi laifi Bhaiya, muna rokon ka in ka tashi hukuntamu, to kayi mana sassauci a hukuncin ba don halin mu ba, ka yi mana uzuri da ajizanci irin na kowanne dan adam”. Sarham ya kasa magana don takaici sai raba ido yake a kan su su biyu, amma kalaman ta na karshe sun yi tasiri sosai a cikin ran sa dake tafasa, ya ciza fatar bakin sa kadan, yana kallon su da lumsassun idanu duk sun zama unease, kada Surayyah ta ji labari, wadda ta kasa zama tana daga tsaye har lokacin amma kafafun ta rawa suke. Da kyar Sarham ya hadiyi miyau, yace cikin sanyin murya. “My only two and beloved Sisters ne suka ci amana ta haka?!” Sumayyah ta cigaba da hawaye tace “wallahi Bhaiya babu ruwa na, bata ma taba gaya min ba ni sai ranar da ka dawo. Ni nawa laifin na rashin zuwan maka ne kawai, da kuma rashin taya ka kula da abinda kake so a bayan idanun ka, wanda ko kadan baka cancanci hakan daga gare ni ba. Kamata yayi ace ko kare ka ajiye don kana son shi ya kamata in kula maka dashi in your absence balle mutane ‘yan adam. Na yi kuskure Bhaiya, amma na tuba, ka karbi hanzari da uzuri na, ajizanci ne na dan adam da mantuwa, na tuba Bhaiya bazan sake ba”. Sumayah ta durkusa a gabansa ta daga hannu cikin roko, hawaye na bilbila, Surayyah ta kasa kare kanta amma hakika yau ta ji kunya, ta kuma yi nadama a lokacin da bata da amfani, wato lokacin da ko ta bada sakon ba zai yi masa amfanin komai ba tuda ya riga da ya dawo, gashi ta san ta sirewa dan uwan nata yanzu, saboda rashin amana, koda bai fada ba bai kuma bai doketa ba. Mama ta shigo da sauri jin kukan Sumayyah, tana tambayar su “me ke faruwa ne haka a falon nan ake kuka har da kururuwa?” Sarham ya ce cikin kololuwar feeling of disappointment “Mama kin gan su, su duka sun ci amana ta!” Mama ta ce “kada Allah ya nuna mini ranar da zan haifi Da maci amanar dan uwan sa, sun dai yi kuskure wanda ba wanda yake sama da aikata shi, ka yi hakuri Sarham ka yafe musu kaji! Duk da ban san girman laifin ba”. Sarham ya dubi Surayyah (feeling disappointed) ya ce “Surayyah idan abinda kika yi kyautatawa ne ga zumunci na da ke, na gode. Allah ya saka da alkhairi. Ke kuma Sumayyah baki yi min laifin komai ba, amma daga yau na san matsayina a wajen ki, na kuma ga ajin da kika ajiye ni, tunda bazaki zame min ‘yar uwar da a bayan raina zata kula da haula ta ko abinda na bari ba”. Sai ya sa kai ya fita, makwallaton sa har motsi yake don tsananin bacin rai, ba tare da ya tsaya yi wa Mama bayanin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36